Salwise's kitchen

Salwise's kitchen I'm Salaha by name born and bred in Zaria.A caterer,skin care consultant,also a writer.

*Clouded Awara ,by Salwise's kitchen*                   *Yadda Za'ayi Awarar**ABUBUWAN BUKATA**Waken soya(yadda ake buka...
05/04/2024

*Clouded Awara ,by Salwise's kitchen*


*Yadda Za'ayi Awarar*
*ABUBUWAN BUKATA*

*Waken soya(yadda ake bukata)
*ruwan tsami/alum
*Kayan miya
*Maggi(ajino moto)
*Mangyada

Za'a gyara waken soyar a wanke tas,sai akai a nik'a.Idan an dawo nik'a,sai ad'iga manja saboda yayi saurin fita a kyallen tatar.

Sai a dora tukunyar k'arfe(Saboda baya yin k'auri idan tukunyar karfe ce)

Sai a dora akan wuta adafa.Za'a tanaji ruwan tsami/alum yana fara tausa sai arik'a zuba ruwan tsamin/alum ahankali gefe da gefe,da tsakiya,za'a ga yana curewa,ruwa mai shar-shar na taruwa barayi guda,Sai a samu buhu wanda aka yaga,a sanya cikin roba ko kwano mai fad'i.Sai arika kwaso wannan dunk'ulalliyar awarar àna zubawa cikin buhun.Ruwan zai ta fita.Dama an jajjaga kayan miya,sai azuba maggi (fari kamar vedan ko ajino moto)da dan gishiri,sai a cakud'a ,sannan a zuba cikin awarar ajujjuya su had'e.Sai adaure buhun a ajiye a gefe guda,kan wani abu yadda ruwan zai fita tas,idan ya tsane tsaf,sai a kwance a yayyanka a soya.Bayan an soya.Sai adiba wanda za'ayi clouded awarar.

Sai a kad'a kwai(kada akada sosai ya tsinke)

Idan ƙwai Guda hudu ne maggi guda ɗaya za'a saka.

Da farko za'a yanka awarar ƙanana

Sai ayanka
Jar tattasai
Koren tattasai
Albasa

Sai azuba cikin Ruwan kwain adan juya.

Za'a d'ora tanda a wuta a zuba mangyaɗa kaɗan a kowanne kwaifar tandar,idan yayi zafi,sai ɗubi ruwan ƙwain a zuba,sannan a zuba awarar daidai yadda zai isa,sai a kuma zuba ruwan ƙwai ɗin a sama awarar,idan ƙasar ya soyu sai a kifa kamar yadda akeyi wa waina. Za'a ga yayi fuu! ya rufe awarar,idan ya soyu sai a kifa ɗayan 6arayin shima ya soyu,haka za'a yi tayi har agama,kamar yadda ake gani acikin hoton,sannan a kwashe a zuba a matsani,man ya tsane.Shikenan.

Note.

Ba'a cika wuta saboda tsakiyar ya samu soyuwa da kyau

Game da awarar

Idan babu ruwan tsami za'a iya amfani da dan tsami/alumun

Idan mai tsome za'ayi(sai adafa farin magin da dan gishiri,idan ya huce,bayan an yayyanka awarar sai

May the Almighty ALLAH accept it from Us🤲🏻
22/03/2024

May the Almighty ALLAH accept it from Us🤲🏻

ALOO CHOPS/POTATO CHOPSBY SALWISE'S KITCHEN✍🏻Abubuwan buƙata..1.Dankalin turawa(Irish)2.Ƙwai3.Marmasasshen burodi(bread ...
20/03/2024

ALOO CHOPS/POTATO CHOPS
BY SALWISE'S KITCHEN✍🏻

Abubuwan buƙata..

1.Dankalin turawa(Irish)

2.Ƙwai

3.Marmasasshen burodi(bread crumbs)

4.Mai ɗanɗano

5.koren tattasai,jar tattasai,albasa.

6.pasley da ruwan lemon tsami kaɗan(optional,idan ba'a so ba sai an saka su ba).

7.Mangyaɗa

Da farko na fere dankalin na dafa,haka ma ƙwai ɗin na dafa,sannan na yanka kayan miyar,na marmasa dankalin(Marshing).

Na zuba kayan miyar da mai ɗanɗano akai,na jujjuya s**a haɗe,sai nazo na raba ƙwai ɗin ko wanne guda ɗaya gida huɗu,sannan na shafa mai a hannu,na riƙa ɗiba ina ɗanyin faɗi dashi,sai na ɗauko 6arin ƙwai ɗaya na saka a tsakiya na mulmula har sai na rufe ƙwai ɗin,haka nayi tayi har na gama.

Sannan na kaɗa ƙwai yadda zai isheni,na ɗan barbaɗa magi na jujjuya,sai na tsoma wannan dankalin dana rufe da ƙwai,sannan na ciro na jujjuya cikin bread crumbs ɗin,na kuma maidawa cikin ƙwai na dawo dashi kan bread crumbs ɗin(sau biyu kenan,yadda zaifi kamawa).

Na ɗora mai a wuta,na watsa albasa,da yayi zafi,sai riƙa ɗaukowa daga cikin bread crumbs sai na saka a mai ɗin(kada acika wuta,kada kuma wutar yayi ƙasa dayawa).Haka na riƙa yi har na gama soyawa(idan yayi golden brown na kwashe.).

Shikenan

Salwise's kitchen✍🏻

*RAMADAN  RECIPE *potato omelette & Chai* BY SALWISE'S KITCHEN✍🏻*Abubuwan buƙata!1.Dankalin turawa(Irish) daidai yadda a...
19/03/2024

*RAMADAN RECIPE *potato omelette & Chai* BY SALWISE'S KITCHEN✍🏻*

Abubuwan buƙata!

1.Dankalin turawa(Irish) daidai yadda ake buƙata.

2.kore da jar tattasai da albasa

3.ƙwai da mai ɗanɗano(magi)

4.Mangyaɗa

Da farko na fere dankalin na yanka ƙanana,na ɗauraye na ɗan barbaɗa gishi kadan sannan na soya(Golden brown).

Daga nan,na kaɗa ƙwai na yanka ja da koren tattasai gami da albarsar ƙanana.Sannan na zuba cikin ruwan ƙwai ɗin,na saka mai ɗanɗano guda ɗaya(saboda nayi amfani da ƙwai guda4) na kaɗa kaɗan kada ya tsinke.

Na ɗora frying pan a low heat(kada a cika wuta) na saka mai kaɗan na zuba rabin ruwan ƙwai ɗin sannan na zuba dankalin dana rigada na soya,sannan na juye sauran ruwan ƙwain a saman dankalin,bayan ɗayan 6arayin ya soyu,sai na kifa a plate(gudun kada ya ruguje) sannan na kifo a frying pan ɗin,domin ɗayan 6arayin shima ya soyu.Yana soyuwa na kifa a mazubi.Shikenan.

Za'a iya ci da drink ko tea ko hakanan ma.

*CHAI*

Yadda na haɗa wannan tea ɗin

Kayan haɗi.

1 Cinnamon
2.Cardamom
3.Star annaise
4.black pepper
5.Cloves
6.Dried ginger
7.Nawa na ƙara da Mint leaf da lemon grasa
8.Sugar
9.Madarar ruwa,hollandia eva,ko peak milk ko dai wata kalar madarar da k**e da buƙata

Da farko na soya cinnamom,cardamom,star annaise sama-sama domin sunfi yin ƙamshi,sannan na daƙa hade da sauran kayan ƙamshin.

Na ɗora tukunya a wuta na zuba ruwa daidai yadda nake buƙata,sannan na zuba kayan haɗin harda sikari na bari s**a kusa dafuwa,na rage wuta,na zuba madarata na kuma rufewa na bari s**a dafu tare kamar na mintuna uku,sannan na sauke na tace.Shikenan.

SALWISE'S KITCHEN✍🏻

RAMADAN DAY1Potato surprise by Salwise's kitchen✍🏻Kayan haɗi 1.Dankalin turawa daidai yadda k**e buƙata2.fulawa kamar ba...
12/03/2024

RAMADAN DAY1
Potato surprise by Salwise's kitchen✍🏻

Kayan haɗi

1.Dankalin turawa daidai yadda k**e buƙata

2.fulawa kamar babbar cokali 10

3.Namar kaza ko namar saniya.

4.Tomato paste

6.Mix spices of your choice,sai mai ɗanɗano.

7.Toothpick

Da farko nayi amfani da potato peeler(Saboda yai fale-fale)bayan na bare,sai na sake amfani da peeler din na yanka fale-fale, sannan na ajiye a gefe.

Nazo nayi marinating ɗin namar(da tomato paste,mai ɗanɗano da mix spices) na ajiye a barayi guda,yayi kamar 30mnts.

Sannan na kwaba fulawa ruwa-ruwa kada yai kauri,na barbaɗa mix spices kaɗan mai ɗanɗano kaɗan,na juya sosoai.

Sai na riƙa ɗukar wannan potato ɗin idan na tsoma sai na ciro na ɗauki yankar namar na saka a tsakiya,sannan na saka toothpick na soka sai ya bullo ta ɗaya gefen,haka na riƙayi har na gama.

Sannan na ɗora mai a wuta(kada a cika pan,ɗan daidai)

Na soya,idan yayi Golden brown sai na kwashe har na kammala soyawa.

Asha ruwa lafiya.

21/10/2023
30/07/2023
Yau ne D/line na milk candy class,gobe zamu fara In sha Allah.Babu maimaita class ga masu register daga baya,sai dai ida...
24/07/2023

Yau ne D/line na milk candy class,gobe zamu fara In sha Allah.
Babu maimaita class ga masu register daga baya,sai dai idan suna telegram!.
Saboda akwai *ƘAMSHI CLASS* da zamu yi agaba.In sha Allah.

#400

Whatspp 08066914136

*FEW DAYS TO GO**TUWON MADARA PROMO CLASS  #400 NAIRA ONLY**DOMIN  KOYON SANA'AR TUWON MADARA KALA-KALA DA HANYOYIN AJIY...
18/07/2023

*FEW DAYS TO GO*

*TUWON MADARA PROMO CLASS #400 NAIRA ONLY*

*DOMIN KOYON SANA'AR TUWON MADARA KALA-KALA DA HANYOYIN AJIYEWA BATARE DA LALACEWA BA

DA KUMA YADDA ZAKU SANYA PRICE.

ZANA KUMA KOYAR DAKU DALILIN DAKE SANYA TUWON MADARA SAURIN LALACEWA

DA KUMA YADDA IDAN YAYI GARDAMA ZAKU GYARA A SAUƘAƘE BATARE DA ANYI ASARA BA.

*ZANA KOYAR DAKU ALBISHIR KYAUTA*

3199774668
Tanimu Salaha Muhammad
First bank.

08066914136

13/07/2023

Ga waɗanda suke son fara sana'ar ga bayanin yadda muke badawa a sari.

Whatspp 08066914136

For more details

I'm Salaha by name born and bred in Zaria.A caterer,skin care consultant,also a writer.

Address

Zaria

Telephone

+2348066914136

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Salwise's kitchen posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Salwise's kitchen:

Share