06/08/2024
ABIN MAMAKI: Ancire Tallafin Man Fetur Kuma Ana Bada Tallafi Saboda Matsalar Da Cire Tallafin Ta Jawowa 'Yan Najeriya
Daga Abubakar Shehu Dokoki
Wato wasu abubuwan idan suna faruwa a ƙasar nan Saika ɗauka a fim ne, kokuma Tatsuniya.
Ancire Tallafin man fetur wanda wannan kowa Yasan matsalar daya haifar ƙirƙirarta akayi, domin tsadarsa ce tajefa talakawa cikin halin wannan ƙunci, tsadar abinci, dakuma wahalar rayuwa ta kowanne ɓangare.
Tunda ansan cire tallafi shine yajefa Talakawa a wannan matsala, to komai dogon hasashen mutum, da iya turanci da fashin baƙi babu abinda zaisa talakawa suji daɗi idan ba'a rage kuɗin man fetur abinci ya sakko ba, babu Yaren da za'ayi wa Talakawa sugane matuƙar Kwanon masara Naira dubu biyu ko sama da Haka.
Misali idan gwamnati tabada Tallafin dubu Hamsin (50) domin talakawa suyi jari, to tayaya zasuyi jari idan sun sayi buhun masara dubu 52 ko sama da Haka?...wannan jarin dai bazai daɗe ba, domin tabbas jari bazai zauna ba, matuƙar mutum bashida abinda zaici.
Idan har cire tallafi zaijefa talaka har Gwamnati tayi tunanin tabashi Tallafi, to Mezai hana gwamnatin tadawo masa da Tallafin man fetur din, Saita haƙura da bashi tallafin.
Kuma ance saboda wasu tsirari aka cire, to yanzu dai kowa yagani ba iya tsirarin mutane bane, harda talakawa kowa yana Amfana.
Allah Yakawo Mana ɗauki, Ameen Summa Ameen.