06/10/2021
UMURNIN IYAYE GAME DA ƊANSU YA SAKI MATAR SA !
Shin idan mahaifi ya umurci ɗanshi da ya saki matar shi, shin ya wajaba a gare shi da yayi masa Biyayya?
Wani mutum ya tambayi Imam Ahmad Bin hanbali (RH), Lallai mahaifina ya umurce ni da in saki matata,
sai yace da shi kada ka sake ta.
Sai mutumin yace; Shin umar (RA) bai yi umurni ga ɗanshi da ya saki matar sa ba?
Sai yace da shi'; Na'am, Kada ka sake ta, har sai mahaifin ka ya zamo kamar misalin Umar (RA).
*📓[(الأداب الشرعية)]*
An ce ga Hasanul Basari
(RH): Mutum ne Mahaifiyar sa ta masa umurni da ya saki matar shi?
Sai yace'; Saki ba ya daga cikin wani abu na biyayyar sa gare ta.
[البر و الصلة لابن المبارك 59]
Ishaq ya ce: in ɗa ya aikata abin da iyaye s**a ce (na ya saki matarsa) to ya kyautata, amma fa ba dole ba ne ya aikata maganar su, domin sakin mace ta gari ba ya daga cikin wani abu na biyayya ga Iyaye.
الكوسج١١٠٤
Wattsap Group; 08032216394
Telegram
https://t.me/rasheedahbintuabeebakar
Rasheedah Bintul Islam