Delemi Dan maliki

Delemi Dan maliki Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Delemi Dan maliki, Shopping & retail, Omuo Obadore.

23/01/2022

Alhamdullah

19/11/2021

Masha Allah

14/06/2021

Alhamdullah...

Masha Allah
14/06/2021

Masha Allah

CIWON AFENDIX ABUBUWA 10 DA YA KAMATA MU SANI 1. Afendis wato "appendix" a turance, wani ɗan zunɓutu ne mai k**ar jela a...
02/06/2021

CIWON AFENDIX

ABUBUWA 10 DA YA KAMATA MU SANI

1. Afendis wato "appendix" a turance, wani ɗan zunɓutu ne mai k**ar jela a mahaɗar ƙaramin hanji da babban hanji. Girmansa ya kai girman yatsan hannu.

2. A ina afendis yake? Afendis yana nan a ciki a kwiɓin dama daga ƙasan cibiya kaɗan.

3. A likitance, afendis ba shi da wani tak**aiman aiki a jiki ɗan Adam. Sai dai, wasu masanan na cewa afendis na ɗauke da wasu ƙwayoyin garkuwar jiki waɗanda ke taimaka wa jiki yaƙi da ƙwayoyin cutuka.

4. Ciwon afendis, wato "appedicitis" a turance, ciwo ne da ke k**a afendis yayin da afendis ya kumbura ko kuma ya ɓule bayan ruɓewa saboda wasu dalilai.

5. Abubuwan da kan haddasa kumburin afendis sun haɗa da: harbin ƙwayoyin cuta k**ar bakteriya, toshewar bakin afendis daga dunƙulallen turɓayan abinci ko bayan gida, ciwon daji/sankara da dai sauransu.

6. Alamun ciwon afendis sun haɗa da:

- ciwo a kwiɓin dama, ƙasa da cibiya ƙaɗan.

- ciwo a kewayen cibiya wanda daga bisani kan zarce zuwa kwiɓin dama.

- ciwon da ke ta'azzara yayin tari ko wani yunƙuri.

- ciwo yayin da aka danna kwiɓin dama da cibiya.

- tashin zuciya da amai.

- Rashin sha'awar cin abinci.

- matsakaicin zazzaɓi, da sauransu.

7. Ciwon afendis na buƙatar tiyatar gaggawa domin cire shi, musamman idan ya riga ya ɓule ko kuma ana tsoron fashewarsa a kowane lokaci.

8. Barin ciwon afendis ba tare da an cire shi ta hanyar tiyata ba na da haɗarin gaske, domin ɓulewa ko fashewarsa na nufin fantsamar ƙwayoyin cuta da ke ƙunshe ciki zuwa dukkan sauran kayan ciki.

9. Hanyar kariya daga ciwon afendis: babu wata sahihiyar hanyar kariya daga ciwon afendis; sai dai masana kimiyyar abinci na ganin cewa ciwon afendis bai cika k**a masu cin datsar hatsi, ganyayyaki da 'yayan itatuwa ba, wato masu ƙaurace wa sarrafaffen abinci kenan.

Saboda haka, batun cewa afendis gidan tsakuwa ne ko kuma ciwon afendis na faruwa ne yayin da tsakuwa ta cika shi tatsuniya ce kawai!

10. Yaushe ya k**ata ka ga likita? Da zarar ka fara jin wasu daga cikin alamun da aka ambata a sama, garzaya asibiti domin duba ka.

Allah yabamu lafiya da zama Lafiya Ameeen.

OPPOSITE EMIR PALACE GATE SULEJA ABUJA
08161923214
08073346633

By Mai Ratata

28/05/2021

Shopping & retail

28/05/2021

Address

Omuo Obadore

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Delemi Dan maliki posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share