08/02/2026
Irin Sanin da Nake da shi ga Dr. Idris Abdul’aziz (R) | Fitowa ta (01)
Tun ina ƙarami na san Malam Dr. Idris Abdul’aziz (R). A gaskiya, zan iya cewa shi ne babban Malami na farko da na fara sani a rayuwata, kuma daga cikin mutanen da s**a fara zana min hoton yadda ilimi, tarbiyya, da tsoron Allah ya kamata su kasance a zahiri, ba a baki kawai ba.
Abin da mutane da dama ba su sani ba shi ne: a Jihar Bauchi aka haife ni, kuma a can na tashi na yi wayo, duk da cewa ba mu da wata alaƙar jini ko ‘yan uwa a Bauchi. Amma mun yi dogon zama a Bauchi, kuma rayuwar can ta ba ni damar sanin Malam fiye da yadda mutane da yawa za su ke zato.
Mun kasance maƙota da Malam, layin su ba nisa da namu. Ya san iyayenmu ƙwarai, kuma suna daga cikin mutanen da yake girmama wa sosai.
Wannan kusanci ne ya ba ni damar ganin wasu siffofinsa na kusa, ba wai a matsayin fitaccen Malami kawai ba, amma a matsayin mutum mai tsari, natsuwa, da tsoron Allah.
Mahifiyata ta yi makarantar malam anan Dutsen Tanshi, kuma daga cikin abubuwan da zan iya tunawa shi ne: ban taɓa ganin makarantar Matan Aure irin ta Malam ba. Makaranta ce da aka gina bisa tsantsar tsari ga tarbiyya.
A can, Malam bai yarda Malami ya ko haɗa ido da ɗalibai mata ba. Saboda haka ake sanya labule tsakanin Malami mai koyarwa da ɗalibai mata, har sai an kammala karatu Malamin ya fita ba tare da ya ga ɗaliban ba, su ma kuma ba za su gan shi ba. Wannan ba tsaurin ra’ayi ba ne kawai, a ganina, tsantsar fahimta ce ta yadda za a kare mutunci da tarbiyyar al’umma.
Malam ba ya yarda da sakaci ko banbadanci wajen tarbiyya. Shi ya sa ko a hanya, idan ɗaliba ta haɗu da Malami, za ta kawar da kai; ko gaisuwa ba za ta yi ba. Wannan duk yana daga cikin tarbiyyar da aka gina su a kai, tarbiyyar mutunci, kunya, da tsoron Allah.
Duk da tsauraran ka’idoji a bangaren tarbiyya, Malam mutum ne mai matuƙar tausayi. Ina tuna yadda Mahifiyata take fada mana cewa idan Malaman makarantar s**a kawo tambayoyin jarrabawa, sai ya ce:
“Haba, wannan sai ka ce na ɗaliban jami’a ne? A je a canza, a sassauta waɗannan tambayoyin.”Allahu Akbar.
Wannan kalma kaɗai ta isa ta nuna cewa Malam ba wai kawai yana son tsauri ba ne, yana kuma son sauƙaƙa wa dalibai, domin su fahimta, su koyi ilimi da zuciya mai kyau.
Daga cikin manyan siffofinsa kuma, shine baya son fitina da tashin hankali. Akwai wata addu’a da yake yawan yi yana cewa:
“Ya Allah, duk wanda zai kawo min fitina ko cikas a wannan makaranta ko a harkar karantarwa, ka raba ni da shi, ka nesanta shi da mu.”
Wannan addu’a tana nuna irin natsuwa da hangen nesa da Malam yake da shi a shugabanci da tarbiyya.
Bangaren taimako kuwa, ba a ma magana tun daga abinci, sutura, har da jari. Idan dai mutum ba shi da hali, Malam na tsayawa a kansa gwargwadon iko. Kuma Ba ya yin hakan don neman suna, sai don neman yardar Allah.
Haka kuma, Malam bai buɗe ƙofar alaƙa da mata ko kaɗan. Saboda haka, idan akwai wata buƙata ko uzuri, mata da dama s**an bi ta wajen iyalansa ne. Wannan ma wani ɓangare ne na tsauraran ƙa’idojin da ya kafa don kare mutunci da tsarkin mu’amala.
Bayan barin mu Jihar Bauchi, Muna da labarin Malam bai tsaya ba wajen ayyukan alheri. Ya buɗe shago, inda ya raba na mata daban, na maza daban, ba yadda za a yi a cakuda su da juna.
Ya buɗe asibiti. Ya kafa makaranta har ana NCE. Alhamdulillah, tarihin Malam cike yake da ayyukan alheri masu yawa, kuma duk wanda ya yi nazari a kansa zai ga cewa rayuwarsa ta kasance sadaukarwa ce ga ilimi, tarbiyya, da hidimar al’umma.
A nan zan takaita wannan rubutu na farko. Zan ci gaba a fitowa ta biyu, In sha Allah.
Na rubuta wannan ne saboda irin ƙaunar da nake wa Malam. Ranar rasuwarsa na daga cikin ranakun da ba zan taɓa mantawa da su ba a rayuwata. A ‘yan kwanakin nan, sai tuna Malam nake. Ina roƙon Allah ya sa yana cikin rahama da walwala.
Allah ya jikansa da rahama, ya ci gaba da ɗaukaka da’awarsa da karantarwarsa. Ameen.
🖊 Ibrahim Yahya Harande
05/02/2026