20/01/2017
TRUE LIFE STORY
LABARI NA
Part 1
Dani da masoyiya ta munso junan mu uwa bazamu rabuba,
hakika inasonta har cikin zuchiya ta, haka zalika itama tana sona sosai da sosai, mun fara soyayyar mu babu wanda ya sani, kasancewar kusan layinmu daya, babu dare babu rana kullum muna tare, amma a waya domin soyayyar tamu ta basaja ce, dalili kuwa shine ra'ayinmu yazo daya,
ra'ayinmu shine matasan layinmu sunada wata dabi'a, idan har akasan dawadda kake soyayya ko akasan sunan ta, to sunan ta zai koma naka, nata k*ma zai koma nata, babu wanda bazai san wance budurwar wane bane, mu k*ma anamu tunanin sai muke ganin hakan ba daidai bane, shi yasa muka yanke shawarar boye sirrin mu, domin afili idan muka hadu babu wanda zai ce akwai wata alaka a tsakanina da ita, domin bama yiwa juna magana saboda tsaro, amma idan muka hadu daga ni sai ita uwa ma chinye junan mu, haka rayuwar soyayyar mu taita tafiya gwanin ban sha'awa, bamuda aiki sai na waya, domin bazai taba yuwuwa minti talatin tazo tawuce batareda daya yayiwa daya waya ba, a kullum zaka ganni ina waya amma baka isa kasan da wanda nake wayar ba, haka itama a cikin kawayen ta yake faruwa babu wanda ya san da wanda take waya, mutane suna min kallon wanda ya ke burga da waya, domin kowa yanamin kallon cewa aduk lokachin da nake waya tofa karya nakeyi, kawai dai na kara wayar ne akunnena don na burge mutane sudauka cewa waya nakeyi, domin aduk sanda zaka ganni hannuna yana kan kunnena alamar cewa waya nakeyi, haka mutane s**ai ta karyata ni, domin yin wayan nawa yawuce misali, wani lokachin ko abinci nakeci tofa waya nakan kunnena, saboda akoda yaushe tare muke cin abinci, nasan mai karatu zaiyi mamakin cewa tayaya za'ayi abinci yaciwu ta wayar selula? Hmmm to bari kaji yadda mukeyi, idan na dakko abinci na saka a gabana sai na cemata itama ta dakko idan nayi cokali daya sai nace mata itama tayi, to kaji ta yadda muke cin abinci a waya tare, a kullum idan zamu kwanta bacci sai mun kirawo juna a waya munyi sallama sannan muyi addu'ar kwanciya bacci, da safe kuwa idan na rigata tashi zan kirata na gayamata cewa gari ya waye, haka zalika itama idan ta rigani tashi zata kirawo ni, idan azumi ya zo wani lokachin ita take tashina natafi tuhajjid, ni k*ma idan nadawo sai na tasheta muyi sahur