06/07/2025
*Albarka poultry services*
*Ko kun san tsarin abincin kaza mai kwai?*
✔️ Chick Ration:
Kaza tana fara cin chick ration daga rana ta farko (Day 1) har zuwa sati na 8. Wannan abinci yana taimakawa wajen girma da gina jiki a farkon rayuwarta.
✔️ Grower Ration:
Daga sati na 9 zuwa lokacin da kaza ta fara kwai, ana ba da grower ration. Wannan nau’in abinci yana karfafa jiki da bunkasa tsarin haihuwa.
✔️ Layer Ration:
Ana fara ba kaza layer ration daga lokacin da ta fara kwai (5-10% production), wanda yawanci ke faruwa daga sati na 18, idan an ba ta kulawa mai kyau da abinci mai gina jiki.
🔍 Lura:
Kaza zata fara kwai ne idan:
Nauyinta ya kai matsayin da ake bukata.
Kwayoyin haihuwarta sun girma yadda ya kamata.
Ta ci abinci mai inganci kamar Albarka Feed.
Ingantaccen kiwo da ciyar da kaji da Abincin Albarka Feed yana taimakawa wajen samun kazar da zata fara kwai da wuri kuma tana dabbaka kwai mai yawa.
Dr. Abdulaziz Musa Kwalli
07031856257
Veterinary Consultant
Albarka POULTRY Services