Hyzango69

Hyzango69 Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Hyzango69, Shopping & retail, Mariri beside colanut market opp Maidugori Road, Kano.

07/08/2024

Ya Ubangiji! Ka Gafarta Min Tun Kafin Ranar Da Zan Gurfana A Gabanka Ka Auna Ayyukana.🤲
😭😭😭

Ameen Ya Hayyu Ya Qayyum 🤲

Alhamdulillah I'm + 1 Happy to Me 🥰💖💝Wanne Fata Kake min na Alkhairi
01/08/2024

Alhamdulillah I'm + 1 Happy to Me 🥰💖💝

Wanne Fata Kake min na Alkhairi

🙏🕋
18/06/2024

🙏🕋

Talaka Bawan Allah Masoyin Manza Allah Yana muku barka da Sallah 😍💕 Singular+ Single=
18/06/2024

Talaka Bawan Allah
Masoyin Manza Allah Yana muku barka da Sallah 😍💕

Singular+ Single=

05/09/2022

Malam ILU ABDU MARIRI.

Daga HAMZA YAKUBU ZANGO.

Malam ILU Wata baiwa ce da Allah Ya bawa mutanen Mariri Saboda Kaunar sa da ilimi hade da Kaunar Mutanen Mariri. Sanin duk Wani dalilin da Yayi Karatu a MARIRI SPECIAL PRIMARY SCHOOL. Yasan irin gudunwar sa dangane da harkar ilimi da son bunkasar ilimi a Wannan Yankin.

Malam ILU Ya Kawo wasu tsari Ko nace ya Kiyaye Tsarin PROMOTION, DEMOTION tare da REPEATING. Wannan Abu Yasa dalibai da Yawa sun dage Matuqa Wajen yin Karatu da Kuma ganin cewa mutum bai samu matsala Ko Wasa cikin Koyon sa ba, bayan nan Ya Koyawa Daliban sa sanin mahimmancin lokaci ma'ana lokacin Zuwa Makaranta Kaso 78% Kafin Karfe 7:40 sun dira a Makaranta, Wanda Ko Mutum bashi da lafiya Iyayen sa Zasu Yi Kokarin ganin cewa sun sanar da Makaranta. Malam ILU Ya Kulla alaqa da Iyayen Daliban domin samun Tarbiyya da Kuma Tabbatar da cewa ba shakka Yaro Yazo Makaranta, idan Kayi Kallon bangaren Tsafta a lokacin da Yake Koyarwa Zaka ga Kowa ya gudun Kar ya Zama Kazami, ga Sharar Area-Area da ake yi Wanda a assembly ground Za'a bayyana Wacce area ce ta Zama ta Farko hakan Yasa gasa Wajen Tsafta Baga Daliban ba harda Malamai. Wani Abu da Zai baka sha'awa da burgewa shi din ba fa bashi ne Headmaster ba😁 Tsagwaron Kishi ne da Kwadayin bada gudunwar sa ga Al'ummar sa. Cikin himmar sa da Fuwacewar da Allah Yayi Masa Malaman Zamanin sa na shakkar sa domin Kuwa Kowa baya iya Zama a Office lokacin da Yake da Period. Yakan bawa iyaye Gwarin gwuiwa akan dan su domin Yayi Karatun gaba da Firamare, Sakandire hade da Makarantun da suke gaba da ita Sakandiren {Tertiary}.
Bayan son ganin saurayi musamman Wanda Yake da Kokari Ko gatan Karatun Yaqiiyi Malam ilu Yana Zuwa har gida Yayi iya yin sa domin yaga mutum Yayi. Bana manta Ni Kai na Malam ilu shine Wanda da sanadiyyar sa ne nayi KANO STATE POLYTECHNIC. a hakan ma Kullum sai Yayi min Fadan Cigaba da Karatu.

Bayan nan Tsakanin sa da Malamai Wanda S**a Yi Zamani dashi duk Wani Abu na Farin Ciki Ko Akasin Haka Malam ilu na Kokarin sanar da Tsofaffin Daliban Wannan Makaranta irin halin da ake ciki domin Yi Masa Fatan Alkhairi Ko Jajantawa, na Kusan nan akwai Wani babban Malami Wanda ya bada gudunwar a Makaranta Yayi RITAYA Ga Kuma Tsufa Malam ilu sai da ya hada dalibai S**a bada gudunwar su domin ganin Farin Cikin Malam .... Da watan Ramadan Wlh da aka Kai ma Malamin gudunmawar Abinchi da Kudi sai Hawaye lokacin Yana Tunanin Mai Zasu ci, bayan nan Malam Indabawa ya rasu Yana bin dalibai Yana Gaya musu cewa suyi Masa Addu'a Allah Ya gafartawa Malaman mu. Ya bada gudunmawar sa Wajen Samun dalibai Masu matuqar gaske, Wajen Addini da Zamani. Daliban sa sun hada daga yanki da Yawa musamman cikin Mariri, Farawa, Hotoro, Tarauni, Tulku, Zara, Tsamiya, Dorawa, Kureqe Juma da dai Sauran su.

Ubangiji Ya saka Masa da Alkhairi Kadan daga Cikin abunda Alkalami na na rubutu Zai fada daga gare shi Ina Yi Masa Fatan Alkhairi.

Affordable Price.08069230369
02/09/2022

Affordable Price.

08069230369

Sheikh Dahiru Bauchi: Malamin Da Ya Fi Kowa Yawan Zuri’ar Mahaddata Alkur’ani A DuniyaDaga Aminiya 2/9/2022 ✍️.Fitaccen ...
02/09/2022

Sheikh Dahiru Bauchi: Malamin Da Ya Fi Kowa Yawan Zuri’ar Mahaddata Alkur’ani A Duniya

Daga Aminiya 2/9/2022 ✍️.

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya kafa tarihin zama mutumin da ya fi kowa yawan zuri’ar da ta haddace Alkur’ani a tarihin duniya.

Alkaluma sun nuna cewa shehin malamin, wanda a kwanan nan ya cika shekara 98 a duniya — ranar 2 ga watan Almuharram 1444 Hijiriyya — yana da ’ya’ya da jikoki da ma tattaba-kunne kusan 300 da s**a haddace Alkur’ani.

A cewar kundin tattara bayanai na Cholan Book Of World Records, wadanda s**a karrama malamin da lambar yabo, Sheikh Dahiru Bauchi shi ne mutum na farko da ya taba samun irin wannan baiwar.

Bayanai sun nuna mashahurin malamain yana da ’ya’ya 95 da jikoki 406 da tattaba-kunne 100. Daga cikin wannan adadin, ’ya’yansa 77 da jikoki 199 da kuma tattaba-kunne 12 ne s**a haddace Alkur’anin

Yana daga cikin Halifofin Sheikh Inyass

Sheikh Darihu Bauchi ne daga cikin halifofin Shehu Ibrahim Inyass, Halifan Darikar Tijjaniyya, bayan wanda ya assasa ta, wato Sheikh Ahmadu Tijjani.

Yana daga cikin manyan malaman Musulunci a Najeriya, shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Koli da ke bayar da Fatawar Musulunci a Najeriya sannan babban jigo ne a Darikar Tijjaniya a Najeriya da ma Afirka.

A zantawarsa da ’yan jarida shekarun baya a Bauchi, Sheikh Dahiru ya ba da takaitaccen tarihinsa, inda ya ce, “Tarihina dai ni Bafulatani ne, dukanin kakannina hudu Fulani ne, domin kowane mutum yana da kakanni hudu — ta wajen mahaifinsa biyu, ta wajen mahaifiyarsa biyu.

To ni dukanin kakannina Fulani ne babu inda muka hadu da wata kabila ta kowace fuska. Mu Fulanin Bauchi ne a lokacin da Jihar Bauchi take hade da Jihar Gombe.

“Bayan da aka raba Jihar Bauchi da Jihar Gombe, sai muka zama mu Fulanin Jihar Bauchi ne, a lokaci guda kuma Fulanin Jihar Gombe ne.

Ta wajen mahaifina ni Bafulatanin Jihar Bauchi ne, ta wajen mahaifiyata ni Bafulatanin Nafada ne da ke Jihar Gombe.

“An haife ni ne a watan Janairun 1927, wanda ya yi daidai da watan Muharram 1346 Bayan Hijira, a ranar Laraba.”

Yadda na mayar da karatun Alkur’ani sana’ata’
Ya ce abin da ya fi ba shi sha’awa a rayuwarsa shi ne irin yadda ya mayar da Alkur’ani sana’arsa da kuma yadda ya rungumi Darikar Tijjaniya ta zama rayuwarsa.

“A duk lokacin da nake hutu ina shagaltuwa ne da karatun Alkur’ani da karanta Salatul Fatihi da tasbihi da istigfari da salatin Annabi (SAW) da sauran zikirori,” in ji shi.

Kwarewar Sheikh Dahiru Bauchi

Da aka tambaye shi kan fannonin ilimin da ya fi kwarewa, shehin malamin ya ce, “Na yi dukkan karatuna na addini a karkashin kulawar mahaifina, har na haddace Alkur’ani kuma ta hannunsa ne na karbi Darikar Tijjaniya.

“Shi mahaifina ya karbi Darikar Tijjaniya ne ta hannun wani mutum mai suna Alhaji Gwani Abba, daga baya sai mahaifina ya ba ni izinin na tafi duk inda nake so domin zurfafa ilimina na addini da haddar Alkur’ani mai girma.

“Bangaren da na fi kwarewa sosai shi ne Alkur’ani, daga nan kuma sai bangaren Tafsiri, a nan malaman Tafsiri sun ce lallai na iya tafsiri inji su.

“Sai kuma bangaren Ma’arifa, ma’anar Ma’arifa shi ne ilimin (gyaran) zuciya wanda ake kiran sa Tlimin Tarbiyya.

“A nan ma masu irin ilimin kan ce ina da sani a fannin. Shehu Ibrahim ya ce lallai na san wannan bangare.

“Sauran ilimomi kuma ina tattabawa, su Hadisi da Lugga da Li’irabi da Tasrifi da Fikihu, duk ina tattabawa,” inji shi.

‘Dalilin da nake buga misali kan duk tambayar da aka yi min’
Da aka tambayarsa cewa jama’a na mamakin yadda idan aka yi masa tambaya sai ya ba da misali kafin ya bayar da gundarin amsar, sai ya ce, “Wato shi buga misali wata runduna ce ta Allah mai shigar da ilimi cikin kawunan mutane.

“Idan ka kawo amsar magana sai ka buga misalin da za ta hau kan mutane domin fahimtar da su.

“Shi buga misali yana jawo hankali a fahimci mene ne aka fada. Misali na da matukar muhimmaci wajen ba da amsa.”

Shehin malamin ya zama masanin Tafsirin Alkur’ani Mai Girma wanda ya samu lambobin yabo a wannan bangaren.

Ya kuma samu digirin girmamawa a bangarori daban-daban a Najeriya da ma kasashen waje.

Jami’ar Tarayya da ke Lafiya a Jihar Nasarawa ta ba shi lambar yabo ta Digirin girmamawa, sannan Gwamnatin Tarayya ta ba shi lambar girmamawa ta kasa ta OFR.

Nasarorin Sheikh Dahiru Bauchi

Ga wasu daga cikin nasarorin da Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya samu a tsawon shekarunsa:

1, Ya musuluntar da dubban mutane

2, A duk lokaci bayan lokaci yakan karanta Alkur’ani kuma yana yin saukar Alkur’ani a kwana biyu

3, Ya ba da lazumin Darikar Tijjaniyya wa dubban mutane da dama a fadin duniya

4, Ya kafa makarantun haddar Alkur’ani sama da 1500 a Najeriya da sassan Afirka

5, Sama da mutum 140,924 sun haddace Alkur’ani a makarantunsa a fadin Najeriya

6, Karkashin gidauniyasa, an gina dakunan karatu guda 133,060 a Arewacin Najeriya

7, Mutum ne mai kishin kasarsa Najeriya wanda aduk lokacin da ya bude baki zai yi addu’a sai ya roki Allah Ya ba kasar zaman lafiya da kwanciyar hankali

Bugu da kari, malamin yana cikin wadanda s**a fi kowa dadewa suna tafisirin Alkur’ani da watan azumin Ramadan.

Masallacin da yake tafsirin da ke unguwar Tudun Wada a Kaduna, na daya daga cikin manyan masallatan da ke cikin garin, kuma za a iya cewa a tsawon shekaru, malamin yakan zauna a garin kusan fiye da a ko ina.

Wani bincike da wani wanda yayi Nazari kan rayuwar malamin ya kuma rubuta littafi a kansa mai suna Shehu Dahiru Bauchi Ginin Allah, shekaru uku da s**a wuce, Farfesa Khalid Abdullahi Zaria, ya ce

Daya daga cikin almajiran shehin, Mallam Ahmad Tijjani Kolo, ya ce a yanzu an sami karin mahaddata a cikin zuri’arsa, inda yanzu s**a doshi 300. Ya ce da wahala a sami mai irin wannan a tarihi.

Shugaban Kungiyar Daliban Sheikh Dahiru Bauchi, Mallam Ibrahim Imam Ismaila, ya ce a tarihi babu wanda ya taba samun irin baiwarsa.

‘Rayuwarsa gaba daya makaranta ce’

Shi kuwa Daraktan Wakafi a Hukumar Shari’a na Jihar Bauchi, Mallam Ahmad Tijjani Sa’id, ya ce rayuwar shehun malamin gaba dayanta makaranta ce.

Ya ce rayuwar malamin ta raya ilimi da kuma tarbiyyantar da al’umma, saboda a yau a raye a cikin malamai da ya yi tafiya daga Fataskum zuwa Filato a kafa don yada addinin Musulunci.

Ya kuma ce malamin ya yi tafiya daga Arewa har kasashen Kudu a kan jaki da doki don yada addinin.

Sannan ya yi tafiya a kan keke zuwa kauyuka da dama kamar Tafawa Balewa da yankunan Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma don yada addinin Musulunci.

‘Gidajensa 1,000 da ake zama kyauta’

Malam Ahmad Tijjani Sa’id ya ci gaba da cewa babu abin mamaki cikin sha’anin malamin kamar yadda yake daukar nauyi ba tare da jin tsoron hidima ba.

“Yana da gidaje fiye da dubu daya a fadin kasar nan, amma ba inda ake haya, bayin Allah masu neman ilimi yake zubawa a ciki kyauta.

“Jama’ar da yake ciyarwa Allah kadai Ya san adadinsu. A kullum idan Shehi zai fito zai sallami baki fiye da 3,000 da s**a zo ziyarar sa daga ciki da wajen Najeriya, kuma za ka samu dalibansa ya yi musu auren fari ya musu suna kuma bai gaji ba.

“Ya maka mace ta biyu ya dauki nauyinku. Ire-iren wadannan halaye na Shehi da wuya ka samu wanda zai iya yin haka.”

01/12/2020
13/11/2020

Allah Ya Gafartawa Chairman 😂😂😂 Gayu Mutanen mu.
SalSalisu Salisu MuhammadlSalisu Salisu MuhammadhSalisu Salisu MuhammadlSalihu Tanko YakasainSalihu Tanko YakasaikSalihu Tanko Yakasai

13/11/2020

*KARATUKAN PROF IBRAHIM AHMAD MAQARI NA AUDIO*

_Zaka iya saukar da karatukan Prof Ibrahim Ahmad Maqari anan_

Littafi: *Attajul Jami'u Lil Usul*
https://bit.ly/3gxfDdx

Littafi: *Bulughul Maram*
https://bit.ly/32sRY9f

Littafi: *Muwadda Malik*
https://bit.ly/3gysZpS

Littafi: *Sahihul Bukhari*
https://bit.ly/31zuxf4

Littafi: *Sahihul Bukhari (Bita Tare Da Malamai)*
https://bit.ly/3gtFy5S

Littafi: *Ihya'u Ulumiddeen*
https://bit.ly/3lhSzTE

Littafi: *Jam'ul Jawami'i Fi Ilmi Usulil Fiqh*
https://bit.ly/3gHchoB

Samu *Ramadan Tafsir da sauran karatukan* anan https://sheikhmaqary.com.ng/audios

Don Allah ayaɗa domin anfanuwar Al-Ummah

Address

Mariri Beside Colanut Market Opp Maidugori Road
Kano

Telephone

+2348069230369

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hyzango69 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Hyzango69:

Share