27/05/2026
“Dan uwa, idan za’a yi adalci dole ne a kalli aiki da impact dinsa, ba wai siyasa kawai ba. A lokacin da Professor Isa Ali Pantami yake shugaban NITDA, daya daga cikin manyan abubuwan da ya jagoranta shine Nigeria Data Protection Regulation (NDPR). Wannan dokar ta kawo tsarin kare bayanan mutanen Nigeria a internet, apps da kuma bankuna. Kafin wannan lokaci kamfanoni da yawa suna amfani da bayanan mutane ba tare da cikakken tsari ba, kuma Nigeria bata da karfin gwiwa a idon manyan investors na tech saboda rashin data protection.
Amma bayan NDPR, an bude wata sabuwar hanya a digital economy. An samar da sabbin ayyukan yi ga matasa masu IT, cybersecurity da data protection. Haka kuma fintech companies kamar Paystack da Flutterwave s**a samu karin karbuwa saboda akwai tsarin kare bayanan users. Wannan ya kara yarda da online banking, e-commerce da sauran harkokin internet business. Wannan ba karamin abu bane ga economy saboda duniya yanzu data da technology suna daga cikin manyan ginshikan tattalin arziki.
Lokacin da kuma ya zama Minister, ya kara mayar da hankali wajen gina digital economy ta Nigeria. A karkashin jagorancinsa aka tura tsarin National Digital Economy Policy, aka fara 5G a Nigeria, aka kara broadband expansion, sannan aka bude kofar manyan digital transformation programs. Wannan shine foundation din da ya sa yau matasa da yawa suke samun damar coding, freelancing, graphics design, online business, YouTube, TikTok, fintech da remote jobs suna samun kudade daga internet har da dollar.
Mutane da yawa suna kallon 5G kamar internet ne kawai, alhali kuwa yana da alaka da AI, smart business, online education, telemedicine, agriculture technology da sauran manyan abubuwan da kasashen duniya suke amfani dasu wajen bunkasa tattalin arzikinsu. A lokacin COVID-19 ma ICT sector ya taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa economy din Nigeria, har aka bayyana cewa contribution dinsa zuwa GDP ya kai kusan 17.92%, wanda ya kasance daya daga cikin mafi girma a tarihin kasar.
Mu talakawa ma muna cin moriyar irin wadannan abubuwan ko da wasu basu lura ba. Yau matashi zai iya zama a gida yana aiki da kamfani a kasashen waje ta internet, wani yana siyarwa online, wani yana koyon skill kyauta ta internet, wani yana samun kudi daga content creation ko freelancing. Duk wadannan abubuwa suna bukatar strong digital infrastructure da shugabanci mai hangen nesa.
Irin wannan tunani ba tunanin politician na yau da kullum bane. Tunani ne na mutum mai fahimtar yadda duniya take tafiya a wannan digital era. Kasashe masu tasiri yanzu suna gina tattalin arzikinsu ne akan technology, innovation da digital economy, ba mai kawai ba. Shi yasa ake bukatar leaders masu ilimi, hangen nesa da fahimtar future technology domin su gina systems da zasu anfani matasa da kasa baki daya.”
----------------
Mubarak Musa - Mubarakeey