20/11/2022
LISSAFI cigaban GIMBIYA RUDDA'U episode 016
_______________________________________
Abdullahi dayyabu tamburawa
[email protected] 08069592193
Al'amarin birnin baitul Salam kuwa bayan da gimbiya lauwat ta durkushe bisa guiwowin ta sakamakon jin cewa dalibin ta shi ne sarki burradu da ta Dade tana nema a duniyar kafirci, sarki Nazir ya kalle ta ya ce ki sarrafa zuciyar ki ya ke ya ta, hakika ya so ya shammace mu, Amma Kuma Allah ya taimake mu akan sa, da izinin Allah musuluncin nasa sai ya Zama na gaske, Dan haka ki kwantar da hankalin ki, kuma Ina rokon ki da kada ki sake ki nuna Masa kinsan komai domin musamu damar Yi Masa rubdugu mu cusa Masa addini, dafatan Zaki rike adduar sassauta bacin Rai, gimbiya lauwat ta mike cikin sanyin jiki da niyar ta shige makwancin ta, sai sarki ya ce ya ke ya ta shin kin manta ne baki ji labarin jahadin Yan uwanki ba Kuma k**e kokarin tafiya, gimbiya lauwat sai a sannan hankalin ta ya dawo jikin ta tadago Kai ta kalli Yan uwanta sai tayi murmushi sannan ta dawo ta zauna,
Sarki Nazir ya koma Kan Yan uwanta sannan ya kalli babban ciki ya ce to kaikuma zaiyan bamu naka labarin jahadin, zaiyan yayi murmushi sannan ya ce ya Kai mahaifi na ai ni karamar kasa aka tura ni domin, su cewa kawai sukayi baza su karbi addinin ba duk abun da Za'a yi musu sai dai ayi, Amma Basu taba malaman da'awa ba, kuma dakarun da'awa sun tabbatatar tawagar da'awa ta dawo gida lafiya, shi ne shugaban da'irar mu sayyid munir ya tura ni akan na kamo sarkin su na zo da shi,
Ya Kai abban mu kasani gaba daya dakarun kasar fa guda milyan shida ne, wato tawaga sittin,
Da fari dai da naje fada na tarar da sarki akan karagar mulki, zagaye da shi wasu manyan dakaru ne su dubu suna ta muzurai, alokacin dariya ta so ta kwace min sakamakon yanda Naga suna kallo na, Amma da na tuna sune masu jayayya da umarnin ubangijin musulunci sai naji Raina ya baci, Dan haka sai na karasa gaban sarkin na tsaya a tsaye, wani dogari ya kalle ni wai ni