15/04/2026
TABDIJAN: Ɗiyar Attajirin Najeriya Temi Otedola ta koka kan yadda mijinta baya iya yi mata faɗa ko tsawa idan ta ɓata masa rai
Daga Ayau News
Diyar attajirin Najeriya, Temi Otedola ta bayyana takaicin ta kan yadda ta ce mijinta, Mr Eazi, baya iya kallon ta ya yi mata fada ko tsawata mata idan ta ɓata masa rai ya yi fushi, sai dai yayi ta fushi ya daina mata magana, kafin daga baya ya rubuta mata dogon email yana bayyana abin da ya bata masa rai.
A shafinta na intanet amaryar ta ce inda son samu ne ita ta fi son ya yi magana da ita kai tsaye ya yi mata masifa da fada ko tsawa ne a maimakon yin shiru ko rubutu.
Me zaku ce?