18/03/2026
RAHOTO....
Ma’aikatar Leken Asiri ta Iran ta bayyana yadda ta yi nasarar murkushe wasu manyan ayyukan ‘yan leƙen asiri da masu cin amanar ƙasa da ke da alaƙa da Izra@ila, waɗanda s**a yi ƙoƙarin anfani da yanayin yaƙi a cikin ƙasar.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba, ma’aikatar ta ce bayan sa ido mai tsauri kan mutanen da ake zargi da yi wa Isra’ila aiki tare da taimakawa shirye-shiryen adawa da Iran, an k**a akalla mutane daei da sha daya (111) masu cin amanar ƙasa da ke cikin ƙungiyoyin masu goyon bayan sarauta a wasu hare-haren rigakafi da aka kai a jihohi 26 na ƙasar.
Sanarwar ta bayyana waɗannan a matsayin “makiyan Iran masu alaka da Izra@ila ”, inda aka ce suna ƙoƙarin tada tarzoma a cikin ƙasar. Haka kuma an ƙwace mak**ai da dama ciki har da bindigogi, wuƙaƙe, sanduna, na’urorin lantarki masu girgiza jiki, feshi, tutoci na bogi da sauransu.
Jami’an leƙen asiri tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro sun kuma gano tare da k**a wasu ‘yan leƙen asiri guda huɗu da ke aiki ga Amurka da abokan haɗin gwiwarta, ciki har da mutum biyu a lardin Hamadan.
An bayyana cewa waɗannan ‘yan leƙen asirin sun samu horo na musamman a ƙarƙashin wata cibiyar al’adun Amurka a wata ƙasa makwabciya, inda s**a rika tura bayanai kan wuraren ajiyar mak**an sojojin Iran zuwa ga abokan gaba na Amurka da Isra’ila.
Haka kuma an k**a wasu biyu a lardin West Azarbaijan, waɗanda ke aiki da wata cibiyar leƙen asiri da ke yankin Kurdistan na Iraq.
Ma’aikatar ta ƙara da cewa an k**a wasu manyan kayan mak**ai guda biyu, ciki har da bindigogi 29, bindigogin AK-47 guda biyu tare da harsasai masu yawa, yayin da ake ƙoƙarin shigo da su daga Kurdistan na Iraq zuwa lardin Kermanshah.
A wani samame daban, an ƙwace wasu mak**ai a lardin Khorasan Razavi, ciki har da bindigogi guda 8, harsasai 161, na’urar sadarwa ta rediyo da kuma kwalaben wuta (Molotov cocktails) guda 21, tare da k**a wasu mutane da dama.
Bugu da ƙari, mutane 21 sun shiga hannu a jihohin Tehran, Hamadan, Fars da West Azarbaijan bisa zargin aikawa da hotuna, bidiyo da bayanai masu muhimmanci ga tashar talabijin ta “Iran International” da ake dangantawa da Izra@ila.
Haka kuma jami’an tsaro sun gano tare da k**a manyan na’urorin sadarwa na tauraron dan adam guda 350 (Starlink), waɗanda ake ƙoƙarin shigo da su ba bisa ƙa’ida ba daga wasu ƙasashen Larabawa na Tekun Fasha zuwa lardin Hormozgan.
Siyasar Zamani