01/10/2025
π An fasa Auren saboda abubuwa biyu, wai yace baza'ayi fulani day ba, sai maman budurwar tace bazai yiwu ba, ai Auren kawayenta ma anyi
Haka kuma yace bazai k**a hall ayi dinner ba, mahaifinta yace yana supporting Ιinsa, sai mahaifiyar ta tace to gaskiya saidai a fasa Auren, yanzu haka Ζ΄arta tana neman Aure abin yaΖi, shekarunta yakai 34 amma kowa yaΖi zuwa da niyan Aure, sai Ζ΄an Amore, manyan gayu yan karya, masu Ιaukanta zuwa club π
Yanzu ta samu ciki, Kuma mahaifiyarta ta koreta, shine take cewa ita mamanta ce ta lalata mata rayuwa Kuma ta cuceta, Sannan tace ta Saba da Maza wajen saduwa, ma'ana ZINA yabi jikinta.
Gashi bata da baffanu da suke sonta saboda yadda mahaifiyarta take nuna soyayyarta gareta, tayi waya da wani baffanta da yake wani gari sai yace A'a Kar taje saboda bayanan, tace wallahi tasan yananan kawai gudun fitina yake saboda yadda yasan mahaifiyar ta.
Yace tanason a samu wani me kasada da zai Aureta, Amma dai ta fara shaye shaye, tace ta koyi hakane a club da take fita ta window, tace ta koyi zuwa club ne tun lokacin datayita gyara saboda Aurenta yazo dab, tace sha'awarta ya Karu, ta zama mace da gaske, Sannan Kuma ta kwallafa rai cikin bukatar na miji, bayan hakan ya faru da ita sai mahaifinta ya rasu, shine ta samu kanta cikin zuwa club!
Ya Ubangiji kayi mana kariya da bin duniya, sannan ka sanya Albarka cikin rayuwar mu ka rabamu da fitinan da zai nisantamu daga gareka Ya Rabb.
Bilal Omar Baba Gombe βοΈ