14/08/2021
RAYUWA A TERTIARY INSTITUTION
A CIKIN SHIRIN NAMU NA YAU ZAKUJI YADDA HUSSAIN YA BAR KARATUN ANATOMY A LOKACIN DA ZAI SHIGA 300L ,SAIDAI BAWAI YA BAR KARATUN KWATAKWATA BANE,YAJA DA BAYA NE DON SAKE SHIRI.
ASOF: A TAKAICE,ZAMU SO SANIN SUNAN BAKONMU DA TARIHINSA...?
HUSSAIN: Sunana Hussaini Yakubu Yakubu, an haifeni a jihar Bauchi,kuma nayi karatun primary dana secondary a jihar Plateau, sa'annan na wuce zuwa jami'ar Maiduguri a yanzu haka. Inda nake karanta pharmacy,Ina aji daya 100L amma kafin nan da ni dalibi ne na Human Anatomy 200L amma na barshi.
ASOF: KO MAI YASA KABAR ANATOMY KA KOMA PHARMACY ?
HUSSAIN: Abinda yasa nabar Anatomy na koma pharmacy shine,tun Ina primary 5 nake sha'awar zama likitan daya kware wajen sanin magunguna da sarrafa su,kuma sai abin yazomin daidai da mahaifiya ta itama tabani karfin guiwan karanta pharmacy,shiyasa nabar Anatomy na koma pharmacy.
ASOF: A KARON FARKO KA FUSKANCI WANI KALUBALE NE WAJEN NEMAN ADMISSION ?
KANEMI ADMISSION SAU BIYU,YAYA ABUN YAKASANCE ?
HUSSAIN: A gaskiya na fuskanci kalubale sosai,na farko,nayi remedial a university of Maiduguri 2017/2018 session inda nasamu G.P na remedial 4.0 sa'annan nasamu 200 a JAMB. Da zummar karantar pharmacy,bayan admission yafito nasamu pharmacy,amma yakasance mahaifiyata ba tada kudi harda yakai nazo registration latti,harya yakaiga anchanzamin course daga pharmacy zuwa Anatomy.
A lokacin mahaifiya ta tayi baqin ciki ganin haka.
A jamb 2019,naqara yin jamb amma nasamu matsalar computer,nasamu 194 batare da nagama ba,kuma a lokacin Ina shirin gama 100L a Anatomy.
Amma duk da haka ban karaya ba kuma iyayena ma basu karaya ba. Haka naci gaba da Anatomy na ,mutane da wasu daga cikin abokaina har habaici suke min da cewa ni LIKITAN GAWA ne suna min dariya. Amma banyi give up ba.nakara yin JAMB din a 2020 wanda nasamu maki sama da 200+. Wanda Allah yasa nasamu pharmacy dashi. Amma fa duk da haka bantsira ba saboda wasu suna cewa ai bana tausayin iyayena,wasu kuma nacewa ai wannan haukane da dabbanci. Zanje 300L a Anatomy amma indawo 100L pharmacy. Amma addu'ar iyaye na yakan karamin karfin guiwa.
ASOF: YAYA KAKEJI A RANKA YANZU DAKA DAWO AJI DAYA 100L MAIMAKON ZUWA AJI UKU 300L
HUSSAIN: Gaskiya nayiwa ubangiji Allah godiya,kuma nayi murna sosai saboda nayi addu'oi sosai sannan iyayena sunmin kuma sunamin.
ALHAMDULILLAH !
ASOF: MENENE SIRRIN NASARAR CIN JAMB DINKA HAR SAU UKU,KARATU NE KO KUMA WANI NA DABAN ?
HUSSAIN: Nasarar cin jarabawa abu 4 ne kachal :
1. Yin addu'a zuwaga ubangijina domin shike taimako na
2. Yin kokari gurin karatu tun wuri da fadada bincike akan abinda ban gane ba,kamar downloading tutorial a YouTube domin ganewa.
3. Samun malami kwararre mussamman Yayana wanda shi makaho ne amma yakan koyar dani don cimma nasara ta.
4. Sannar addu'ar iyaye shine sirrin nasara ta
ASOF: WASU IRIN KALUBALE KASAMU A RAYUWAR KARATUNKA KO ABUBUWAN DA S**A ZAMA BARAZANA GA KARATUN KA ?
HUSSAIN: Nafarko shine rashin wanda zai tallafamin saboda iyayena basu da karfi sosai kasancewar mu biyar 5 take taimako a jami'a, saboda har dako nakeyi don siyan handout.
Na biyu rashin kayan abinci,sanin yan uwana dalibai ne cewa,hankalinka bazai tashiba har sai lokacin da kaga food stuff dinka sun kare,hankalina yakan tashi sosai kuma bana iya kiran iyayena saboda ina matukar tausaya musu,shiya kaini gayin dako.
Na uku shine rashin wurin zama(accomodation), kasancewar rashin kudi yakansa narasa hostel saidai na kwana a class ko masallaci kafin Allah yasa nasamu gun zama.
A gaskiya wadannan abubuwan suna matukar dagamin hankali.
ASOF: SHIN AKWAI BANBANCI DA TUN YANZU KA FARA FUSKANTA TSAKANIN KARATUN ANATOMY DA PHARMACY ?
HUSSAIN: Eh, akwai banbanci. A gaskiya ita Anatomy tana koyarwa ne akan sanin sassa na jikin Dan_adam,kuma ita ba course din dogaro dakai bane(professional course). Ita kuma pharmacy course ce da take koyarda hada magunguna da badasu. Shi course din dogaro dakaine (professional course ) ne.
ASOF: AKWAI WANI ALFANU DAKA HANGO TATTARE DA PHARMACY DAZAKA IYA TAIMAKAWA AL'UMMA NE KO DAI KAWAI KANA RA'AYIN KAZAMA PHARMACIST NE ?
HUSSAIN: Gaskiya akwai alfanu dana hango. Ni Ina matukar son tallafawa bayin Allah musamman talakawa da basuda lafiya wajen taimakamusu ta hanyar ceto rayukan su.
ASOF: KA BAYYANA CEWA DAYA DAGA CIKIN NASARAR CIN JARABAWAR KA SHINE YAYAN KA WANDA KACE YANA TAIMAKA MAKA ALHALINSHI MAKAHO NE .
KO TAYA HAKAN KE YIWUWA ?
HUSSAIN: EH,kwarai kuwa. Da yanada idanu kuma yana gani har yagama secondary School. Bayan ya kammala secondary School,yasamu admission zuwa ABU Zaria,inda yake karanta veterinary medicine 2012_2013. Daga baya ya samu matsalar idanu wanda takaishi ga makanta. So ganin daman ya iya lissafi nasu maths, chemistry da physics nakan karanta mai questions na calculation yaji sa'annan na bashi paper yayi solving don nakoya hakama theory aspect. Yanzu haka yana ABU Zaria yana karanta Mass Communication 400L da makantarsa.
ASOF: KA BAYYANA MANA IRIN KALUBALEN DAKA FUSKANTA A RAYUWAR KARATUNKA,SHIN WADANNAN MATSALOLIN BASU SA KAJI KARATU YA FITANMA A RAI BA ?
HUSSAIN: Wallahi ko kadan banajin karatu yafitanmun akai,saboda babu wanda yake samun abu mai anfani ta hanyan sauki,musamman idan akace kai dalibi ne. Kawai saidai yakaramin karfin guiwa na dage don kar in watsa wa iyayena kasa a ido.
Kuma nakan tuna da cewa annabi MUHAMMAD (saw) ma baisamu karatu da sauki ba. Wannan kesa naji dadin dagewa.
ASOF: A TAKAICE WACE SHAWARA ZAKA BAWA YAN'UWA DALIBAN ILIMI ?
HUSSAIN: Ina mai basu shawara cewa suyi karatu kuma su jure duk wahala dake cikin karatun don bamai dawwama bane.
Sannan karda su cuce iyayensu ta kudin makaranta.
ASOF: DUBA DA CEWA INDA KAKE KARATU NA AREWA MASO GABASHIN KASAR NAJERIYA,KUMA SUNA FAMA DA MATSALAR TSARO MUSAMMAN A BAYA.
SHIN BA WANI KALUBALE DA WANNAN RASHIN TSARO YAKAWO MAKA ?
HUSSAIN: A gaskiya akwai,amma Allah shike karewa saboda akwai lokacin da kana karatu sai kaji ana harbi ko tashin Bomb. Amma Alhamdulillah yanzu dasauki sosai.
ASOF: KAFIN KAFARA DEGREE KAYI KARATUN REMEDIAL,MAI ZAKACE GAME DA KARATUN REMEDIAL ?
HUSSAIN: Karatun remedial karatu ne dake karawa dalibi ilimi bayan kammala secondary school kuma shine hanya mafi sauki gun samun admission bayan dalibi yayi kokari yaci remedial da JAMB dinshi.
ASOF: MAI ZAKACE GAME DA WANNAN KUNGIYAR ASOF ....WANI ABUNE DA TAKEYI YAFI BAURGEKA ?
HUSSAIN: A gaskiya babu abun da zance saidai Allah ubangiji yasakamata da alkhairi da wanda suke jajircewa Don ganin dalibai sunyi nasara.
Abunda yake burgeni da ita takan wayar ma da ddalibai kai don gudun kuskure.
ASOF: WACE SHAWARA ZAKA IYA BAWA KUNGIYAR ASOF ?
HUSSAIN:Shawarata itace,adinga hakuri da dalibai gun tambayoyinsu,kuma Dan Allah su taimaka wajen nemawa 'ya'yan talakawa daman shiga jami'a a karkashin ASOF gun gomnati da sauran masu haalin taimakawa.
ASOF: MUNGODE SOSAI DA AMSA GAYYATA,ALLAH YASA AFI HAKA,SAIMUNZO CONVOCATION DINKA AS PHARMACIST....
HUSSAIN: Nagode sosa,ameen ya rahman