11/05/2025
LABARIN JIMRAU DAN SARKIN NOMA NA BIYU
Cigaban Labarin Sarkin Noma da 'Ya'yansa.
Littafi: Magana Jarice 2
Mawallafi: Margayi Alhaji Abubakar Imam
Jimrau kuwa da ya bi kudu, yana,cikin tafiya, a kwana a tashi har ya kai wani dan gidan gona cikin dokar daji, ya sallama, aka amsa, sai ya ga wani dan yaro mai shekara k**ar bakwai ya kunno kai, ya fito, Jimrau ya dube shi, ya ce, “Ina mai gidan?”
Yaro ya ce, “Me ka ke so da shi?” Jimrau ya ce, “Kai dai yi mini sallama.”
Yaro ya ce, “Me ka ke so na ce, ni ne mai gidan.”
Jimrau ya ce, “Don Allah, samari, shiga ka yi mini sallama. Ka san na wuce wasa da kai.”
Yaro ya ce, “Af, watau ka raina ni ko? Wallahi ni ne mai gidan, tambayi abin da ka ke so, ka ji kuwa na rantse.”
Da Jimrau ya ji haka sai jikinsa ya yi sanyi, ya ce wa yaron, “To, in ka yarda ina so in ruruma nan, da safe in wuce.”
Yaro ya ce, “Shigo mana. Wa zai qi baqo?”
Jimrau ya tashi, ya kai shi wani dan daki, ya ajiye kayansa, duk gabansa na faduwa. Sai ya duba gidan nan ba alamar kowa. Ya sake duban yaro, ya ce, “Don Allah, samari, kai kadai ke gidan nan? Ko kuwa iyayenka sun tafi gona ne, s**a bar ka tsaro?”
Yaro ya ce, “Kana tsammani k**ata ya yi rantsuwa a kan karya?”
Da Jimrau ya ji haka sai ya ce, “In ka yarda, na ji dai na huta, ina so in kara gaba.”
Yaro ya yi murmushi ya ce, “Ka kara gaba ina cikin wannan dare? Ko da safe ka tashi, kafin ka tarad da gari ka kai azahar. In tsoro ka ke ji don na ce ni ke da gidan kada wani abu ya gigita ka.”
Jimrau ya ce, “To, shi ke nan.” Ya kanne ya zauna. Da s**a gaisa yaro ya tambaye shi inda ya yi wa tsinke. Jimrau ya gaya masa labarin abin da ya sa ya baro gida duka. Can da dare yaro ya kawo nama soyayye s**a ci ya kawo abinci kuma iri iri s**a nada. Ga abinci sabo, amma Jimrau bai san sa’ad da yaro ya yi shi ba, bai ko ga wani ya kawo masa ba. Zai tambaya yaron ya kwa6e shi ya ce, “Tsaya. Babban abin da ba na so shi ne tambaya, iya gani iya kyalewa.” Jimrau bai sake cewa kome ba.
Da gari ya waye Jimrau ya ce zai wuce. Yaro ya rarrashe shi ya yi mugama. Cikin ranan nan yaro ya yi ta lallahar Jimrau ya zauna tare da shi, tun da ya ke dai ya ce neman arziki ya zo. Jimrau ya yarda ya zauna. Sannu-sannu yaro na lallaharsa har s**a zama jiki. Ga abubuwan mamaki Jimrau na so ya tambaya, yaro ya kwa6e shi tun da fari. Wasa-wasa Jimrau ya sami k**ar wata goma a gidan. Duk aikace-aikacen da yaron nan ke so ya yi masa. Ya yabe masa gidansa kaf, ya yi masa zaure sabo, ya kara masa wata shigifa, ya kara masa taska domin ajiye abinci. Ya dai bi gidan nan duk ya gyara. Da watan nan goma s**a cika, ya tambayi yaro yana so ya sallame shi ya koma garinsu. Ya gaya masa ya yi wa ubansa alkawari bayan shekara guda zai koma. Yaro ya yi masa godiya mai yawa, ya kawo kyanwa ya ba Jimrau, ya ce, “Ga arziki nan, na sallame ka.”
Koda ya ke Jimrau ya raina wannan ’yar kyanwa, a ce wai ita ce sakayyar aikin nan da ya sha, duk da haka tsoron al’amuran yaron nan ya sa ya ki nuna alamar rainuwa ga fuskarsa. Ya yi masa godiya mai yawa, sai ka ce jaka guda ya ba shi. Ya dauki kyanwa zai tafi, yaro ya ce,.“Tsaya. Da na yi tsammani za ka raina kyanwan nan ne, amma yanzu da na ga ba ka raina ba, ka yi murna da ita, zan gaya maka duk amfanin da za ta yi maka, da kuma inda za ka je da ita ta yi maka amfanin.”
To, akwai wata dodanniya wadda ta ke tare fatake, tana kashe su ta cinye, ta kwace kayan, ta tara dukiya mai yawa da kudi jakunkuna a gidan jibge. Yaro ya kwashe labarin dodanniyan nan da yadda ta ke rikida ya gaya wa Jimrau, ya kuma gaya masa dawan da ta ke, ya ba shi dabarun da zai yi duka, kyanwan nan ta taimake shı ya sami nasara ga dodanniyan nan, ya kashe ta ya kwashe dukiyar da ta tara.
Jimrau ya yi godiya, ya yi shiri ya nufi dawan da dodanniyar ta ke, yana cewa a ransa, “Mahaqurci mawadaci, in dai abin da yaron nan ya fadi gaskiya ne, bana wannan dodanniya ta gamu da gamonta.”
Da abokan tafiyarsa s**a ga kullum yana fama da daukar kyanwa sai s**a ce masa, “Me za ka yi da kyanwan nan girin- girin haka kullum?”
Jimrau ya ce, “Idon matambayi.” Sai s**a shafa masa lafiya.
Da s**a kawo mararrabar zuwa gidan dodanniya, suna sauri su surare su wuce, sai s**a ga Jimrau ya dauki hanya ya nufi gidan. Abokan tafiyarsa na mamaki, sai s**a qara mai, kada wani abu ya same shi ya ce ya san su.
Da ya isa tungar da azahar sai ya nufi gidan dodanniyar, duk ’yar kyanwar nan tana boye. Tun a kan hanyar ya ke ganin kasusuwan mutane bargaja. Ya yi sallama, dodanniya ta fito hakoran nan zago-zago. Jimrau ya durkusa ya gaishe ta, ta tambaye shi inda za shi da inda ya fito, tana murna, tana lashe- lashen baki, tana ce, “Maraba gasasshe!”
Jimrau na cewa, “Mhm.” Yadube ta, ya ce da ma gareta ya zo tun daga kasar Sudan. Ta tambaye shi abin da ya zo nema garin tun daga can.
Jimrau ya ce, “ Labarinki ne fatake ke barbadawa ko ina har ya kai Sudan, suna cewa wai kina iya rikida kome ki ke so. Saboda haka ne na zo in gani ko gaskiya ne, don an ce gani ya kori ji. Ni ban kula ba da ki kashe ni, muddin dai na ga abin mamaki.”
Dadodanniyan nan ta ji haka ta san shahararta ba inda ba ta kai ba, sai ta yi kyakkyewa, ta dubi Jimrau kuma ta ga alama ya yi mai, sai murna ta qara kashe ta. Ta sake dubansa, ta ce, “To, kada fa ka ji tsoro, kai din ma yanzu ka ga abin da ka ke jin labarinsa duk ya bazu a duniya. Duk yadda ka ji an fadi labarina sai abin da aka rage. Ni ce Dandakwarya, Dodanniya Uwar Dodanni!” Nan da nan ta girgiza jikinta, sai ta zama giwa shirim a cikin zauren da su ke. Ta sake girgizawa sai ta zama zaki, sai kura, sai bauna, sai kanki, har da su jimina. Da ta gama ta koma mutum sosai yadda ta ke da. Jimrau ya dube ta, ya ce, “Ai! Wani abu sai mai shi. Yanzu kina iya rikida kananan dabbobi k**ar su bera ko?”
Dodanniya ta ce, “Af, beran me kuma? An rikida giwa b***e bera’?” Sai ta girgiza jikinta, ta zama bera. Da ganin ta zama bera sai Jimrau ya yi farat ya saki kyanwarsa yadda yaron nan ya gaya masa. Ko da kyanwa ta ga bera sai ta yi tsalle ta k**a shi ta kashe ta cinye. Ko da ta cinye dodanniya, sai ya ji gidan ya dauka “Haa! Jimrau, babu kuskure, ka yi nasara.”
Da ya ji haka, da har ya sha jinin jikinsa, sai ya tuna yaron nan ya riga ya gaya masa haka zai auku. Saboda haka ya tashi ya kutsa kai cikin gidan, ya kwashe duk abin da lalatattan nan ta tara kaya kyankyandi-kyankyandi ga su nan cike da wani daki, ga wani ingarmar kili, ga jakai, k**ar goma sha bakwai duk ya jibga musu kayan nan, ya shiga in da ta ke boye kudi ya tarad da su ris. Kai, ya bi kayan gidan nan dai, ko allura bai bari ba, ya dora wa jakunansa, ya haye dokinsa barde, ya kora su ya nufi gida, yana waka, bukata ta biya.
****
Zamu dora cigansa LABARIN KOSAU DAN SARKIN NOMA NA FARI
Manu Fagge