26/11/2022
Allah ne yayi halitta, halitarki dabam ce cikin jinsin yan mata. Kina da faren idanu tas mai dauke da yalwatar bakin gashin gira, a kan su. Gaki da dogon hanci kamar ke kika wa kanki, dai dai tuwar labban bakin ki akan dogowar fuskar ki shi ya fito da cikar kyawun ki, ta yadda ko bakiyi kwalliya ba kyawun dirin ki hada da kyawun fuskarki zai iya sa gayu karo a kan t**i.