12/12/2015
MATSALOLIN MA'AURATA.
1. DUK SANDA MIJINA ZAI KUSANCENI SAI NAJI ZAFI.
*****
mata da dama suna fama da wannan matsala duk sanda mazajensu zasu kusancesu sai sunji azaba, lallai akwai dalilai da yawa dake kawo wannan matsalar, kadan daga cikinsu sune:
i. RASHIN NI'IMA: Idan mace bata da ni'ima a jikinta gabanta ya bushe duk sanda mijinta zaikusanceta lallai zataji zafi, kuma shi ma kansa mijin ba zai gamsu ba. Zakaga miji ya na gudun mace musamman idan yana da wata sai a ringa zargin waccen ta asirce shi. A'a matsalar daga mata ne dan haka akwai abubuwan da zaki yi amfani da su dan kawo gyara tsakaninki da mijinki.
MACE MAI IRIN WANNAN MATSALAR:
** ki samu rake ki matse ruwan ki hada da zuma ki rinka sha da yamma.
** ki sami kwai kifasa shi da garin bawon ruman da nikakken ifas ki saka albasa da yawa ki soyasu ruwa2 ki danga ci.
ii. CUTAR SANYIN GABAN MACE: ita cutar sanyi gaban mace itace idan mace zata zauna zataga tana jikewa har idan kayi korafi kace bata da ni'ima sai kaji tace haba dai ko da yaushe a jike nake to akwai lalura (ciwo) wacce da zaran mijinta ya kusanceta zata ji zafi ga magani kamar haka:
** ki samu ganyen magarya da garin hulba ki tafasa su kitace ringa tsarki da ruwan amma ruwan da dumi zaki ringa amfani da shi.
** ki samu nonon kurciya (ciyawa) da tumatur da ruwan zogale da tafarnuwa da karas ki hadesu ki dinga sha.