15/02/2022
MIHAMMANCIN ONLINE BUSINESS
Online business kasuwancin ne Mai matukar mihimmanci acikin rayuwar Al'umma yataka mihimiyar rawa wajen bunkasa tatttalin Arziki, daga cikin mihimmanci online business
1- business dazaka farashi ko da baka da shago ko da baka da jari, Kuma ba dole Sai kaje kasuwaba.
2- Kasuwanci ne da ya saukawawa mutanen da bazasu iya zuwa kasuwaba saboda yanayin na aiki da sauransu kana office zaka Yi siyayaya a
kawomaka ko a kawoma har Gida
3- Kasuwanci ne da ya temaka wajen fito da hajjjoji Wanda Galibi a manyan shaguna da manyan gurare zaka iya ganinsu, Amma yanzu dakashiga Facebook zakaga wanan hajjojin kasaya cikin sauki.
4- Kasuwanci ne da ya matso da nesa Kusa, kanacikin lungun kauye zaka iya siyayaya a manyan birane har Abun yazo wajenka , idan Banda online business dayawa mutanen Dake kauyuka basa iya siyan kayayyakin zamani na birni Wanda kawai a birni ake sayardasu bazaka samesu a kauye ba.
5- Kasuwanci ne da ya temaka wajen Tsaro, Galibi da idan mutum zaiyi siyayaya Haka zai dauko kudadensa ya nufo manyan birane, Akan iya gamuwa da Yan fashi, ko masu Garkuwa da Mutane, Amma online business ya temaka kana zaune a garinka zaka Yi siyayyaya a manyan birane ko a kamfani a kawomaka kayanka har inda kake.
6- business online, ya temakawa Mata, Galibi bazasu iya zuwa kasuwa aiyi gogggayya dasu ba Amma online business ya temaka musu wajen tallata hajjojinsu, kafin zuwan online business Mata a arewacin nijeriya basa Shiga harkokin kasuwanci online business ya taka mihimiyar rawa wajen kawowa Mata mafita a bangaren kasuwanci Wanda har yakai ga Mata suna kasuwanci sosai, Kuma suna samun riba Mai yawa.
7- kasuwancin online ya temakawa dalibai Wanda suke kasuwanci , a shekarun Baya idan zakayi karatu sedai ka ajiye kasuwanci, Amma zuwan online business yasa zakaga matashi Yana jami'a ko kwaleji Amma yanayin kasuwancin sa cikin kwanciyar hankali zai tallata hajjar sa a platform na zamani yasamu customer ya siyar dasu cikin sauki
8- kasuwancin online ya temakawa Yan kasuwa dayawa Wanda Basu da karfin jari, zakaga Dan Kasuwa yasamu hajoji daga makota da Abokan kasuwanci ya tallata yasamu masu saye, Wanda kafin zuwan online business idan baka da jari a kasuwa kana ganin ciniki zai wuceka saboda baka da hajjojin da customer din suke bukata.
9- kasuwancin online ya temakawa mutanen arewacin nijeriya Dake zaune a wasu kasashe da Kuma wasu garuruwa na kudancin Ƙasar nan, Wanda Galibi irin kayayyakin da suke amfani dasu a gida bazasu samesu a garuruwan da suke zaune ba, Amma zuwan online business ya temaka musu wajen, samun wadanan Abubuwan a online business su saya a aika musu dashi.
10- online business yana temakawa ma'aikata wadanda Basu da lokacin zuwa kasuwa, Galibi a shekarun Baya idan mutum Yana aikin Gwawmnati baya kasuwanci, Amma yanzu ta hanyar online business ma'aikata Gwabnati suna gudanar da Kasuwanci online.
Wadanan kadan ne daga cikin amfani da Kuma mihammancin kasuwancin zamani na online, hakika business online ya temakawa Al'umma kwarai dagaske fannoni na rayuwa, matasa dayawa da idan sun sa data a wayarsu suna tafiyar da ita a shirme, Amma yanzu zakaga matasa masu smartphone sun mayar da ita kasuwar su, suna kasuwanci suna samun riba, Abun takaicine kaga matashi yana dawaya Yana Bata lokaci me yawa da ita Yana Kona data Amma bata Samar Masa ko sisi, tabbas wanan yayi asara lokaci ya shige da matashi zai zauna Wai bashida aikinyi Al'hali ga hanyoyin samu kudade masu yawan gaske
Arewa business online, mun yunkuro don tallafawa matasa da dabaru da hanyoyin da zasu gudanar da kasuwancin online Mai nema Karin bayani zai iya zuwa office dinmu Dake No GF22 shy plaza Gadon Kaya kano ko lambar waya 07064624880
Ko kayi joining group dinmu kazama memba na Arewa Business online
https://chat.whatsapp.com/LvknNg55oPm6gXc07IOTzA
Abdulrashid Abdullahi Kano