10/09/2019
ZUCIYAR MACE
LABARIN SIMON DA PERO
BAYAN MAI KARATU YA KALLI WANNAN HOTON, ABUBUWA DA DAMA ZASU IYA GITTAWA A ZUCIYAR SHI, AMMANA DAGA BISANI BAYAN SANIN DALILIN HOTON, WANI ZAI IYA ZUBDA QWALLA.
A zamanin da, a kasar Girka, anyi wani tsoho mai suna Simon wanda aka yankewa hukunci na horo da yunwa har ya mutu a gida yari.
Wata 'yarsa mai suna Pero ta roqi hukumar garin da ta bata dama tana duba mahaifinta kullum har ya mutu. Hukumar ta bata daman hakan inda a kullum idan tazo ana dubata kota ina domin a tabbatar bata shigo da wani abinci ko abun sha ba.
Pero bazata iya ganin mahaifinta yunwa zata kashe shi ba. Saita Kalli mahaifin nata da idanu irin na Uwa. Don haka domin ta ceci rayuwar shi, shine sai take shayar dashi nononta a kullum idan tazo dubashi.
Da hukumar garin taga Simon yana raye na tsawon lokaci bai mutu ba saboda yunwa, sai s**a fara zargin Pero.
Watarana kwatsam sai gandiroba (prison guard) yayi caraf ya damqe Pero tana bawa mahaifinta nono.
Sai itama aka makata a kotu, ammana saboda yadda ta nuna rashin son kanta ta so mahaifinta, hakan sai yayi galaba a zuciyar alqalin kotun inda ya yanke hukuncin bada belin Babanta da ita kanta.
Wannan Zane yana daya daga cikin zanuka mafiya tsada a turai.
Wato ita mace cike take da soyayya da qauna da kuma sadaukarwa a duk irin role din da take playing a rayuwar mutum. Wani zubin ta zamto Uwa, Yar'uwa, Mata, Malama, Qawa, Uwardaki, da dai sauransu.
Mata sunfi maza tausayi, shiyasa ma s**a kasance sune Uwaye.
Ya Ubangiji Ka yiwa mata albarka