MATSIRGA ISLAMIC RESOURCES

MATSIRGA ISLAMIC RESOURCES For advert and education

22/06/2023
NUHU RIBADU YA DACEDaga Malam Bello Muhammad Sharada Matsalar tsaro a Najeriya tana bukatar mai amana, kuma tana bukatar...
20/06/2023

NUHU RIBADU YA DACE

Daga Malam Bello Muhammad Sharada

Matsalar tsaro a Najeriya tana bukatar mai amana, kuma tana bukatar zakakuri. Ana kashe makudan kudaden jama'a a wajen harkar tsaro. Tsaro ya fi komai cin kudaden Najeriya, ya wuce abin da ake kashewa a 'Petrol subsidy.' Samar da tsaro kuma babban wajibin hukuma ne, shi ne abu daya cikin biyu wanda yafi damun kasarmu. MAFI girman dalilin da ya sa aka kasa shawo kan matsalar tsaro akwai rashin jagoranci mai amana.

Baiwa Ruhu Ribadu mukamin National Security Adviser NSA an ajiye kwarya a gurbinta. Kamar saka Janar Buba Marwa ne a NDLEA. Da Nuhu Ribadu da Buba Marwa duk Fulanin jihar Adamawa ne, dukkansu Yan siyasa ne da s**a taba tsayawa takarar shugabancin Najeriya, kuma s**a rike manyan hukumomi EFCC da NDLEA.

Ina zato a karkashin Ribadu za a iya samun canji na alheri a harkar tsaro ta Najeriya.

19/06/2023

Gaskiya muna goyan bayan Tsohon sarki ya koma garinsu kafin sallah dan muma mu dan sarara da katsalandan

19/06/2023

Kwana biyu kenan ana neman Hoto ko Bidiyon Giya da gidan kasa da akace an gani a Ruguzau din Kano Amma an rasa

19/06/2023

DR IDRIS ABDULAZIZ DUTSEN TANSHI BAUCHI
Khairan insha Allaah

ZAI YI KYAU GWAMNA ABBA DA MADUGU SU SAKE NAZARIDaga Malam Bello Muhammad Sharada A dan tsahirta na kwana biyu a duba so...
18/06/2023

ZAI YI KYAU GWAMNA ABBA DA MADUGU SU SAKE NAZARI

Daga Malam Bello Muhammad Sharada

A dan tsahirta na kwana biyu a duba sosai a ga guraren da aka yi kuskure a gyara. A sake dubawa a ga ina aka yi ganganci a dau mataki don a guji gaba. A kalla da idon basira ina ne ya kamata a tabbatar an dauki mataki a yi hakan.

Kada a ji nauyin yin abin da ya dace. Haka Kada a ji kunya ko tsoron masu wargi. Amma kuma shugabanni su sani sun yi rantsuwa da daukar alkawarin zasu yi aiki da adalci da amana. Babu I'll will. Babu sani ko Sabo.

Abin da ya sa na fadi haka, mutanen da ake mulka suna kuka. Ya kamata a saurari kokensu. Sannan kuma jama'a sune gwamnati, aikin farko na gwamnati shi ne samun walwala da tsaron lafiya da rai da dukiyar jama'a. A kula da wannan.

Wata jarida, mallakin kamfanin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta ce a cikin sati biyu Gwamna Abba K Yusuf ya rusa dukiya ta kusan naira biliyan 126. A duba lamarin nan, a kalli salon da ake amfani da shi.

KAI KUMA SSG Dr Baffa Bichi, yanzu mulki kuke yi, ba kamfen ba. An gama siyasa, a maida hankali a cikawa mutane alkawuran da aka dauka. A yi musu abin da ya dace da kudinsu kuma a rike amana. Banda hargagi da zumudi da wauta. KO ina ake son zuwa za a je

WANENE SARKIN SIYASAR KANO ?Daga Malam Bello Muhammad Sharada A ganina shekara 24 sun isa a bayar da kambu na sarautar s...
18/06/2023

WANENE SARKIN SIYASAR KANO ?

Daga Malam Bello Muhammad Sharada

A ganina shekara 24 sun isa a bayar da kambu na sarautar siyasa a Kano, a wannan jamhuriyya ta hudu. An yi masu mulki samfuri guda uku. Wanda Allah ya nufa da ransu da lafiyarsu da shekarunsu, sun ga yadda Injiniya Rabiu Kwankwaso ya mulki Kano a 1999-2003 da kuma 2011-2015. Sun ga yadda Mallam Ibrahim Shekarau ya yi nasa mulkin a jere 2003-2011. Haka kuma kwana 20 da s**a gabata aka ga karshen mulkin Dr Abdullah Ganduje.

Za a iya baiwa Sanata Ibrahim Shekarau CON Sardaunan Kano matsayin sarautar Sarkin Siyasar Kano saboda tsarin siyasar sa hade yake da salon tarihi da addini da siyasa da sarauta da kasuwanci da ya baiwa Kano shuhura a duka fadin duniya. Duk dan siyasar da ya yi daidai a dabi'a da tafarki da tunani da koyarwar magabatan Kano shi ne sarkin siyasar Kano. Sarkin siyasa ba shi ne wanda ya fi cin takara ko shiga zabe ba, A'a, Sarkin Siyasar Kano shi NE; wanda yake siyasa tare da la'akari da yadda na baya s**a yi da kuma yadda ake lala siyasa a sauran sassan duniya, sannan kuma sakamakon siyasarsa yake komawa kan akasarin jama'ar da ya fito daga cikinsu kuma s**a amfana matukar gaske da tsarinsa, ba biyan bukatarsa ko 'yan tsiraru da ke kewaye da shi. Babu mai wannan siffar sai Shekarau, Sardaunan Kano..

Ina da dalilai guda tara:

Na farko, Shekarau ne mutane s**a zabe shi tsabarsa da karfin kuri'ar ra'ayoyi na jama'a masu son sauyi ba a jam'iyyar gwamnati ta jiha, ba kuma ta karfin mulkin tarayya

Na biyu, Shekarau shi ne dan siyasar da ya yi mulkin jama'a basa tsangwamarsa, ya maimaita a jere kuma ya bar mulki ya ci gaba da mu'amala a cikin kowa babu hantara, ana kewarsa.

Na uku shi ne kadai dan siyasar da ya shigo siyasa da manufar sananniya, ta ra'ayoyi na addini, sannan kuma bai sauya daga inda aka san shi. Shi din nan dai shi ne.

Na hudu shi ne kawai dan siyasar Kano da babu wani jinsin jama'ar Kano da bai tafi da shi ba, kuma har zuwa yau ake buga misali da shi. Ya tafi Sarki da malami da talaka da attajiri da mata da matasa da 'yan boko da 'yan gargajiya.

Na biyar shi ne dan siyasar Kano mai tsananin bin tsarin dimokuradiyya da ka'idojin jam'iyya a kan mulki da wajen mulki.

Na shida shi ne dan siyasar Kano kacal mai bin tsarin aikin gwamnati a mulki da mu'amala kuma mai mutunta umarnin kotu uwar kowa.

Na bakwai shi ne dan siyasar da ya baiwa jama'a dama da jawo su kusa da gwamnati da basu 'yancin fadar albarkacin bakinsu da walwala ba tauye hakki. Bai zama dodo ba a gurin jama'a.

Na takwas shi ne dan siyasar jihar Kano Mai koyi da Sardaunan Sakkwato a tausayi da kyauta. Mai dabi'a ta kishin na kasa kamar Aminu Kano. Mai yafiya da rangwame ba ramuwar gayya kamar Abubakar Rimi, mai tsabtar zancen siyasa kamar Musan Musawa.

Na tara shi ne dan siyasar jihar Kano da bai tara dukiya ba a Kanon da wajenta, kuma bai yi amfani da gwamnati don gina tuwonsa da miyarsa. Sannan a siyasarsa babu yaudara da farfaganda da jamhuru da bita da kulli. Siyasarsa ta tawaliu ce da maida komai gurin Allah da jama'a.

IDAN DA MAI JAYAYYA
GA FILI, GA MAI DOKI

DA KYAW ABBA GIDA GIDA DA TALLAFIN KARATU Yau Abban Kanawa ya wayi gari da bude damar karo karatu ga mabukata na lungu d...
17/06/2023

DA KYAW ABBA GIDA GIDA DA TALLAFIN KARATU

Yau Abban Kanawa ya wayi gari da bude damar karo karatu ga mabukata na lungu da sakon jihar Kano Musamman masu first class

Kuma maganar gaskiya wannan na daga dalilai da s**a sanya galibin Kanawa musamman matasa yin tsayuwar daka na zaben Abba dayi masa aikin dan ganin yayi nasara

Kuma shima wannan na daga cikin alkawurran daya dauka a lokacin yakin neman zabensa a 2019 da kuma 2023
Allaah yayi masa jagoranci kan hakan da sauran manufofinsa na Alheri

Amma ni a irin nawa tsokaci da karamin sanin a fannin ilimi (Education) da muke yan farawa

Da farko tsakanin mai fara Digirin farko da mai cigaba dana biyu wanne yafi bukatar tallafi ?

Na biyu mai first class da wanda ya Gama da pass Digiri wanne yafi bukatar tallafi?

Na uku masu fara Digirin farko dana biyu zuwa uku wanne s**afi yawan da in an rage an samu cigaba?

Dalilina kuwa shekarun baya munyi wata Daura (seminar) bayan an kammala masu rabo s**a samu mu da bamu da rabo muka rasa dan mutum goma 10 kacal za'a dauka

sai hukumar shirya jarrabawar s**ayi la'akari da Dalubai mabukata wannan karatu amfi mutum dari 100 wurin jarrabawar sai s**ayi duk mai yiwuwa aka dauki mutum 50

Na biyu shekaru 4 da s**a wuce mun sake wata Daurar ta larabci za'a dauki mutum 20 masu Digirin farko
Mutum 20 masu Digiri na biyu a Abuja zuwa Turkiyya

Bayan an kammala sai s**ayi la'akari da Dalubai masu son Digirin farko sunfi yawa sai s**a sake daukan 20 cikin wanda makinsu ya kai cikin masu Digirin farko a wannan 20 na biyu da aka kara nima sunana Usman Matsirga ya fito Alhamdulillah ban samu tafiya ba sabida wasu dalilai masu karfi
kaga kenan sun dauki 40 a Digirin farko 20 a Masu Digiri na biyu

Tambayan da galibin Dalubai masu Digiri na biyu s**ayiwa FARFESA Hamaduddeen kenan yaya su ba'a kara dauka cikin su ba?

Amsar kenan da yayita baiwa kowa mai son Digirin farko yafi mai son Digiri na biyu bukatar karatu da kuma Tallafi.

Da wannan nake ganin mai Tatata yafi bukatar tallafi sama da wanda ya iya tafiya harda guje guje

Ina fatan yan uwa zasu fahimce ni

In kuma akwai wani Karin Haske a fannin ilimi da ban sanshi ba?
Ko ta Bangaren gwamnatin Kano a taimaka mana dashi dan mu karu kuma mu karar
Dan mun san Gwamnati nada FARFESOSHI DAKTOCI da GOGAGGUN Ma'aikata a Fannin Gudanarwar ilimi ( EDUCATION )

Allaah Muke roko ya dafawa gwamnatin Abba bisa kudurinta na ilimi da ilmantarwa dama kowace gwamnati
Allaah ka dafawa gwamnatocinmu kan alheransu ka kare mu daga sharrori da munanan manufofin da baza su amfani Al'ummah ba.

[email protected]
27/11/1444 Hijrah 16/06/2023 Miladi.

Assalamu Alaikum
31/08/2022

Assalamu Alaikum

For advert and education

Address

Opp Liman Street Along Madalla Die Die Dakwa Niger/Abuja
Utako

Telephone

+2348173344986

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when MATSIRGA ISLAMIC RESOURCES posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to MATSIRGA ISLAMIC RESOURCES:

Share

Category