06/03/2026
RAHOTO: Yadda Aka Yi Yakin Badar Babban Yaki Na Farko A Tarihin Musulunci
A rana irin ta yau, 17 ga watan Ramadana, ne aka yi babban yakin farko tsakanin Musulmai da kafiran Makka, wato Battle of Badr.
Yakin ya faru ne shekaru biyu bayan hijirar Annabi Muhammad (SAW) daga Makka zuwa Madina. Wurin da aka fafata wannan yaki, wato Badar, yana kusan kilomita 130 daga birnin Madina.
A lokacin wannan yaki, rundunar Musulmi ta kunshi kimanin mutane 313 kacal, yayin da rundunar kafiran Makka ta kai kusan mutane 1000. Duk da karancin adadin Musulmai, Allah Ya ba su nasara a kan makiyansu.
A wannan yaki, sahabbai 14 ne s**a yi shahada suna kare addinin Musulunci. Wannan lamari ya nuna jarumtaka da sadaukarwar sahabban Annabi wajen daga darajar addinin Allah.
Yakin Badar ya kasance daya daga cikin manyan al'amuran tarihi da s**a karfafa Musulunci, tare da nuna yadda taimakon Allah ke zuwa ga bayinsa masu imani.
Allah ya kara tsira da aminci ga Annabi Muhammad, Ya kuma yarda da sahabbansa wadanda s**a sadaukar da rayuwarsu domin kare addinin Musulunci.
Idan aka kwatanta da halin da musulmi ke ciki yau, wanne darasi yakin Badar ke koyarwa?
Daily News Hausa 24