31/08/2024
An sake Rashe An k**a Ganye!!!
Tabbas Mutane sun bar kyakyawan Dabi'un da s**a gada tun zamanin Iyaye da kakanni.
Idan ka maida hankalinka wuri guda, kayi nazari mai zurfin gaske akan rayuwar Al'umman wannan zamani, zaka fahimci cewa, tabbas Mutane sun sake rashe sun k**a Ganye, domin sun ara wasu mummunan Dabi'un wasu kasashen ketare wayanda suke tunanin cewa su wayenyu ne, amma wayewar banzace, domin Dabi'u ne masu yanke zumunci a tsakanin Al'umman Annabi Muhammadu S.A.W, musamman a tsakanin Yan uwa na jini da kuma makwabta.
Idan ka lura sosai a yan Shekaru 20 zuwa 30 baya a cikin birni da karkara zaka ga yadda alaka ake guduna tsakanin Al'umma cikin aminci da girmamawa, rayuwa ce mai cike da gwanin sha'awa, domin ana bada kulawa ta musamman akan hakkin juna, ana kuma bada hakkin makwabta.
Jama'ar Annabi, bari na muku tambaya, Dan Allah yaushe rabonku daku ga Dottawan unguwarku suna haduwa a maciya ( wajen cin abinci da juna tare) kaga Yara maza da mata suna fito da akwashe da kwanukan abinci daga cikin gidaje zuwa Majalisin Iyaye, musamman a tsakanin sallah Mabgriba zuwa Isha'i?
Shin ko kun lura da cewa hadda man shanun wannan zamanin, ba irin man shanun da muka sani a zamanin baya chan bane, domin ada idan ana soya man shanu a gida daya duk layin unguwarku sai ya game da Kamshi, amma yanzu a cikin gidankuma idan ana soya man shanu, bazaka ji kamshinsa ba.
A Shekarun baya akwai karancin Ilmin addini dana boko a tsakanin Al'umma, amma kuma mutane suna da kokarin sauke hakkin Allah Ta'alah akansu, musamman ta fuskar Ibada, ga rike Amana, ga sada zumunci, kuma mutane suna da hakuri sosai akan Al'amuran rayuwar Yau da kullum.
Amma yanzu ga tarin Ilmin Addini dana boko, amma duk kusan na banza ne, domin ba'a amfani da ilmi wajen tafiyar da rayuwar Addini da kuma rayuwar yau da kullum.
Babban abin takaicinma shine, Al'umma sun nisa a akan tafiyar yar da rayuwar aro, gashi kuma an kasa isowa inda ake son a iso din, kuma yunkurin koma baya kuma ab