08/04/2025
Wato in kana neman mayaudara da sunan addini ko ince munafukai to kazo Arewa kuma kayi magana a kan Hausawa da cin amanar su da akayi lokacin tarzomar Fulani ta 1804 da kuma wadda ake musu yanzu.
In kana son su cigaba da kallonka a Musulmi to karka taɓa ƙalubalantar tarzomar Fulani ta 1804 kuma karka taɓa cewa tafiyar da ake a yanzu tsakanin Hausawa da Fulani akwai zalunci ya kamata a samu daidaito da adalci in ba haka ba nan take zasu cireka daga Musulunci su baka sunan ɗan kwangila mai son raba kan Musulmai musamman in kace Hausawa su haɗa kansu su samu ƙungiya mai ƙarfi da zatayi magana da yawunsu wajen nema musu haƙƙoƙinsu da ake dannewa kuma ku baku yarda da Hausa-fulani ba .
Waƴanda zasu ma wancan jafa'in suna sane da kungiyoyin Fulani wanda akasarinsu manyan Fulani ne da suke mulkin ƙasar Hausa s**a kafa su wasu ma su suke jagorantar su kamar Ƙungiyar tabital pulako international wanda sarki guda dake sarautar a ƙasar Hausa a gidan sarautar Hausawa yake shugabanta na duniya amma duk waƴannan munafukan ba mai magana ba mai ƙalubalantar su da cewa ba Musulmai bane ƴan kwangila ne masu son raba kan Musulmai ne hasalima a wajensu hakan daidai ne sanin mutuncin kai ne da ƙishin ƙabila.
Duk tarukan da Fulani suke yi na kungiyoyin su tare da manyansu da suke mulkar Hausawa a ƙasar su sarakuna da ƴan siyasa ba munafikin da yake ƙalubalantar su bale yayi raddin cewa sufa Musulmai ne ba ruwansu da sha'anin ƙabila hasalima sai da in anyi posting na taron ka samesu a ƙasan comment suna sanbarka da murna haɗi da bada goyon baya.
Duk ta'addancin da Fulani daji suke yi a ƙasar Hausa baka taɓa jinsu ko ganin rubutunsu na caccar su da matsawa gomnati a kan a yaƙesu sai dai ka gansu suna nema musu sulhu da basu kariya a fakaice da uzurorin rainin wayo da cewa a dena ƙiransu da Fulani amma kuma su zaka ganosu suna ƙiran sunan wata ƙabila sukutum da cewa suna yiwa danginsu ta'addanci basu yarda da abinda suke musu ba wanda kuma abinda su dangin nasu suke aikatawa Hausawa a ƙasar su ta Hausa ya ninninka abinda ake musu a can wanda kaso 90% cikin 100 na ƴan ta'addan da suke ta'addanci a ƙasar Hausa danginsu ne amma wai kar ka ƙirasu da sunan ƴan ƙabilar su,sai s**e mai ai basu kaɗai ke yi ba,munsan ba su kaɗai bane amma zuwa ta baiyana suke nuna kansu kowa ya gani s**afi yawa? Sune
Dan haka ni dai banyi magana a kan addini ba,bance wani arn*ne ba,bance ni ɗan ƙungiya ka'za bane bane,bance zamu kafa ƙungiyar addini ba bale kace zan raba kan musulmai dan kungiyoyin da aka kafa da sunan Musulunci su ke raba kan musulmai matuka wanda suke kaiwa ga kafirta juna da mugayen maganganu wa juna.
Kafin kayi magana a kan wani zai raba kan musulmai ka fara aiki da Wa'atasamu bihabdillahi jami'an wala ta farraƙu a aikace kar ka zamu ɗaya daga cikin kungiyoyin da aka kafa da sunan Musulunci.
Muddin kana ɗaya daga cikin waƴannan kungiyoyin bakada bakin magana a kan cewa wani zai raba kan Musulmai dan in akwai mai raba kan musulmai to kune dan a Musulunci ba ƙungiya,shi yasa akace ba ƙabila tsakani musulmai kuma hakan ba yana nuna an shafe kasancewar wane ɗan ƙabila ka'za bane a'a sai dan kuyiwa juna adalci da ku tabbatar da gaskiya da riƙon amana,hakan kuma bai hana in wasu sun fanɗare s**a ɗau makami a kanku ku yaƙesu ba kuyi sulhu dasu ba.
Ni Bahaushe ne kuma Bazamfare jinin gidan Gazau
Allah ya ɗaga Hausa da Hausawa ya haɗan kan al'ummar mu ya kawo mana ƙarshen ta'addancin ƴan ta'adda na daji da na birni 🤲
Hausa Land NG 🖋️