Zauren Hadisi

Zauren Hadisi ILIMIN HADISI SHINE MAFIFICIN ILIMI BAYAN ALQUR'ANI MAI GIRMA. Atakaice don yan uwa daliban ilimi.

An bude wannan shafi mai albarkane don a karawa juna sani dangane da abinda ya shafi Ilimin sanin Hadisin Annabi Alaihis Salam.

01/04/2022

Ba'ayin azumi sai anga wata. Haka Kuma Ba'a ajiye azumi sai anga wata. Idan Kuma akayi Hadari ko Hazo, to sai acika lissafin watan sha'aban yakai kwana Talatin 30.

06/05/2019

من قام رمضان إيمانا واحتسابا غفر له ما تقدم من ذنبه.
الحدث

06/05/2019

Ma'anar Azumi:
A fassara ta kai tsaye (lugga) shine kamewa kamar yabda Allah madaukaki yake fada a hakkin Nana Maryam انى نذرت للرحمن صوما .

A fassara ta Shari:a shine kamewa ga Baron ci da sha da dukkan nau'in saduwa, tun daga bullowar alfijir zuwa faduwar ranar da niyyar yin ibada ga Allah madaukaki.



Mutum yana yin niyyar yin Azumin daga ranar farko, wato shine yayi niyyar yin Azumin kwana 29 ko kuma 30 (udan wata yayi nusan), ba wajibi bane lallai sai mutum yayi niyya kullum saidai Wanda ya aauke Azumin saboda wani dalili na rashin lafiya ko kuma mata masu al'ada.

Daga littafin Risala

اللهم صلى وسلم على سيدنا رسول الله

05/05/2019

Duk Wanda ya azimci ranar kokwanto, to ya sabi Abal Kasim.
Hadith.

05/05/2019

Ciyarda abinci ga mabukaci yafi adinkawa ka'aba Riga.
Al-Hadith.

05/05/2019

Azumin Ramadan yana tabbata ne da cikar Sha'aban kwana 29 amma idan wata yayi nusan sai acika kwana 30.
Hadith

04/05/2019

اللهم بلغنا رهضان

14/02/2016

بسم الله الرخمن الرحيم
Yau Insha Allah zamuyi magana akan wadannan Hadisai:-
1-MUNKARI
2-MA'ARUFI
3-SHAZIY
4-MAHFUZI
5-MATRUKI
1:- Abinda fasiqi ya rawaito ko Marafkani ko Mai alfasha, Kuma ya zama ya wadanda s**a fishi inganci, to wannan shi ake kira da MUNKARUL HADITH منكر حديث
2:- Idan amintacce daga matawaita yayi ruwaya kuma ta sabawa marawaici mai rauni, wannan shi ake kira da MA'ARUFIمعروف
3:-Idan amintacce ya rawaito wani kari acikin Hadisi kuma ya zamo ya sabawa abinda amintattu s**a rawaito ko kuma wadanda s**a fishi aminci. Wannan Hadisi shi ake kira da SHAZIY ش*ذ
4:-Idan amintattu da yawa s**a rawaici abinda ya sabawa amintacce mutum daya to Hadisinsu ya zama shine MAHFUZI .محفوظ
5:-Idan ya zama marawaicin Hadisi ana tuhumarsa dayin karya acikin zantukansa da mutane . To Hadisinsa shine MATRUKI متروك

Mu hadu a Darasi na gaba
Allah yasa mu dace.

اللهم صل على كاشف الغمت

05/02/2016

Assalamu Alaikum.
Menene Hadisi MURSALI?
Hadisi MURSALI shine Hadisin da aka sarayar da Sahabi, wato inda aka sami Tabi'i yace "Annabi yace" kai tsaye.
Hadisi GARIBI shine Hadisin marawaici daya tak ne ya kadaita da ruwayarsa. misali a Dabakar sahabbai ko Tabi'ai, Kamar Hadisin انما الاعمال بنيات
sayyadina Umar ne kawai ya kadaita da ruwayarsa duk da cewa ansami sahabbai da yawa sun rawaiceshi, amma ta hanyar sayyadina Umar tafi inganci.
Duk Hadisin da isnadinsa bai saduba,ta kowane hali to wannan shi ake MUNQADI'I Ma'ana inda aka samu an sarayar da mutum daya acikin tsakiyar isnadi.
-Idan kuma aka sarayar da mutum biyu ajere acikin tsakiyar isnadi to wannan sunansa MU'UDHALI معضل
Dafatan Allah ya fahimtar damu.
اللهم صل على نبي الرحمة

Address

City Centre
Kano
KANOCITY,

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Zauren Hadisi posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share