09/06/2026
Wanne ki/ka zaɓa?
A ko B?
Free Hausa Novels Series.
Wanne ki/ka zaɓa?
A ko B?
GARGADI❗️❗️❗️
Labarin 'NI DA KANNENA' taska ce daga fasahar Khadija Aliyu Ibrahim. Kuma kyauta ne.
Satar rubutu ba nishadi ba ne, cin amana ne ga marubuciya da kuma kokarin toshe hasken hazakarta.
Idan ka ga wannan rubutu ba tare da sunana ko link ba, ka sani ba daga gare ni yake ba.
Sannan duk wanda muka k**a da wannan laifin zai fuskanci fushin hukuma.
Saboda haka a kiyaye.
WhatsApp channel 👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCiw48qIzt1JDE4y0l
"BISMILLAHIRRAHMÁNIRRAHEEM!"
"WASSALÁTU WASSALÁMU ALÁ RASULULLÀHI (SALALLÀHU ALAIHI WA SALLAM.)"
'NI DA KANNENA'
CHAPTER FIVE (B)
BAYAN KWANA UKU
Tsawon kwanaki uku kenan Ashraf bai farka ba, hakan ya matuƙar ɗaga musu hankali duk da a baya yasha irin wannan, a baya sai yayi watanni ma a hakan, amma wannan karon hankalin su yayi matuƙar tashi. Daddy ne yake kwana da kan sa a wajen Ashraf kullum cikin yi masa addu'a yake yi.
Sannan yayi waya garin Rano ya saka ake tayi masa saukar Alkur'ani a can da sadakoki, duk da sun bukaci zasu zo dubiya Daddy yace suyi zaman su ba'a samun ganin sa ma. Ita kuwa Mummy jikin ta yayi sauki sosai lokaci zuwa lokaci tana tasowa tazo ɓangaren da Ashraf yake domin ta ganshi, duk lokacin da tazo ganin sa sai tayi kuka sosai hakan ya saka daddy ya hanata zuwa.
Misalin ƙarfe takwas na dare Daddy ya samu shiga ɗakin da Ashraf yake, ya tsaya akan sa ya ƙarewa fuskarsa kallo, yau kam sai ya lura da Ashraf bacci yake yi sosai ba k**ar jiya ba da yake unconscious. Yaji dadin yadda yaga fuskar sa, dandanan ya sunkuya ya fara yi masa karatun Alkur'ani a daidai kunnen sa cikin murya ƙasa ƙasa, ya karanta masa a ƙalla izu biyu na Suratul Baƙrah kasancewar Daddy hafizi ne sosai, sannan ya ɗago ya tada kabbarar sallar Ishaa.
Sai da ya kai raka'a ta biyu yaji na'urorin da suke jikin Ashraf sun fara beeping, kafin kace me likitoci sun cika dakin. A daddafe daddy ya idar da sallar ya taso da gudu yazo in da suke, Ashraf ya hango ya buɗe idon sa, an cire masa na'urar Oxygen muryar sa ƙasa ƙasa yana ta ambaton "innalillahi wa'inna ilahi raji'un"
Da hanzarin sa ya kutsa ya k**a hannun sa ya riƙe sosai yana faɗin:
"Sannu my only son Allah ya baka lafiya" da idon sa Ashraf yai wa Daddy alama, Daddy ba ƙaramin jin dadi yayi ba kasancewar Ashraf ya dawo hayyacin sa. Wasu alluran aka sake yi masa sannan daga bisani wani baccin ya sake daukar sa.
Fito da Ashraf akayi daga ICU aka kai shi ɗakin jinya, cike da farin ciki Daddy ya shiga ɓangaren mummy ya sanar mata halin da ake ciki, tayi farin ciki sosai sannan ta taso ta nufo dakin da Ashraf yake ta tarar da an rage na'urorin jikin sa sosai sannan babu Oxygen a hancin sa.
Hakan ba ƙaramin yi mata daɗi yayi ba, tai ta yiwa Allah godiya cike da farinciki.
Ganin hakan ya saka daddy ya tafi gida domin ya kimtsa kansa saboda yaga itama Mummy ta samu ƙarfi ajikin ta hakan ya saka yaje gida yayi bacci sosai amma lokaci zuwa lokaci yana yawan kiran ta yaji halin da suke ciki.
********************
WASHEGARI
Misalin ƙarfe 5:00 na asuba Ashraf ya farka, ya ƙarewa ɗakin kallo a hankali, a hankali idanun sa s**a kai kan Mummy da take sallar asuba, bayan da tunanin sa ya gama dawowa ne yaji wani hawaye mai zafi yana bin kuncin sa, rintse idon sa yayi tare da faɗin "Allahumma ajirni fiy musibatiy wa'akhlifni khairan min ha" sannan ya ci gaba da faɗin "innalillahi wa'inna ilahi raji'un"
Bayan Mummy ta idar da sallar tayo kansa da sauri tana yi masa sannu, k**a hannun ta yayi fuskar sa cike da hawaye yace:
" Mummy yanzu shikkenan bazan taɓa haihuwa ba a rayuwata? bazan ga ɗa na ba kenan? nima na gaji larurar Daddy innalillahi wa'inna ilahi raji'un, mummy k**ar bazan iya jurewa ba!"
Ban da kuka ba abinda suke yi, cikin shassheƙar kuka Mummy ta kalle shi ta ce:
"Ka kwantar da hankalin ka Ashraf maganar likita ba maganar Allah ba ce, zaka haihu inshaAllahu ba abin da ya gagari Ubangiji."
Kallon ta yayi a raunane sannan yace:
"Nasani Mummy, amma asibiti mafi shahara a duniya ne ya fitar da report ɗi na, nasan bai gagari Ubangiji ba, amma inaso mu ɗora zuciyar mu akan bazan samu ba ɗin sai na zauna lafiya, Mummy don Allah kiyi min addu'a akan Allah ya bani hakuri da juriya."
Yanayin da Ashraf yake magana ko ma waye sai ya tausaya masa musamman mahaifiya. Kuka ta dinga yi k**ar ran ta zai fita, shi kuwa Ashraf rarrashin ta ya dinga yi.
Kusan tare Daddy s**a shigo tare da su Nuratu, kasancewar Ashraf ne ya kirashi a sirrince ya tambayeshi ita. Shine Daddy yai mata waya yace tazo.
Wannan karon har da su Ameerah da Anuwar s**a zo domin su duba shi. Bayan sun g*isa dashi s**a fita sai Nuratu ta shigo tare da junior, Mummy tana ganin ta ta fice daga dakin. A hankali ta ƙarasa inda yake ya buɗe idon sa da yake lumshe ya kalleta fuskar ta tayi fiyau, sannan ya miƙawa junior hannu ya ƙaraso, junior yace:
"Uncle ya jiki?"
"Alhamdulillah"
Ashraf yace sannan ya kalli Nuratu yace:
"Kin rame da yawa ashe daman kina so na, kina tsoro kar na mutu ko?"
Kau da kanta tayi sannan ta mai da hankalin ta kan junior tace:
"Maza kaje gurin su Bibi gani nan nima"
Ba musu junior ya fita daga ɗakin. Ta sake kallon sa tace:
"Ya jikin naka?"
"Alhamdulillah"
ya furta tare da yi mata nuni da ta zauna a gefen gadon da yake kai. Ba musu haka ta ɗan dosana jikin ta.
Hannun sa ya saka ya kamo nata sannan ya kalli fuskarta yace:
"Nuratu bana haihuwa, zaki iya aure na a haka?"
Ɗaga masa kai tayi alamar "eh" cike da ƙwarin gwiwa. Sake kallon ta yayi sosai ya tabbatar babu alamar yaudara ko ƙarya a fuskarta sannan yace mata:
"Meyesa zaki aure ni a hakan?"
Buɗe bakin ta tayi ta fara magana:
"Bazan taɓa barin jinin Daddy ya shiga damuwa ba kuma inda halin da zan iya taimakawa ballantana kai Ashraf ko ba don Daddy ba dole na kula da kai saboda ka nuna min kulawa ta soyayya, abinda nake so ka kwantar da hankalin ka baka da matsala da ni kaji"
Wata sanyayyiyar ajiyar zuciya yayi sannan yace:
"Nagode Nuratu, inshaAllahu zan kula dake sosai zan kula da junior duk da ba isasshiyar lafiya gare ni ba, sannan don Allah Nuratu ki daure ki kula da ni."
Ya numfasa sannan yaci gaba da magana:
" Nuratu na ɗaɗe ina fama da larura tun ina yaro ƙarami nake shan wahala haka iyayena kullum cikin fargaba suke, na zaɓe ki ne kasancewar ki mai tausayi da haƙuri da juriya don Allah karki bani kunya kinji."
Cikin ƙwarin gwiwa Nuratu ta amsa masa tare da yi masa alkawarin zama dashi na har abada, duk da ita kanta tasan ƙarya tai masa kuma zuciyarta tana gargaɗinta tare da raya mata cewar "yaudara ba halinki bane" amma haka ta daure bata bari ya fahimci hakan ba.
Ƙura mata ido kawai yayi yana kallon ta, ya rasa dalilin da ya saka yake jin ta fiye da ransa, yana tunanin kuma ta yadda zai ɓullowa da Mummy cewar ya kamu da son ta, tabbas Nuratu Mutum ce, duk da taƙi sakin jikin ta dashi amma ta amince zata aure shi saboda tausayi da karamci irin nata.
Ita kuwa a nata ɓangaren tayi masa alkawarin rayuwa dashi ne kawai ba don zata iya ba, kawai saboda ta rusa shirin su shi da mahaifiyar sa da kuma wani dalili nata na kai da kai, batasan cewar Ashraf ya kamu da matsanancin sonta ba na gaskiya.
*****************
BAYAN KWANA BIYU
Yau tsawon kwanaki biyu da farkawar Ashraf, Nuratu tana ta sintiri akan Ashraf wajen kai masa abinci da takura masa sai yaci saboda in dai bata zo ba baya iya cin komai. Wannan wasan nasa yana yiwa Mummy daɗi tun da ita duk a tunanin ta yana cikin shirin da s**a shirya da Ashraf.
Saboda haka itama Mummy ta bangaren ta ta fara rage abinda take yiwa Nuratu, idan tazo sai ta basu waje duk da hakan ba yayi mata daɗi amma tasan zai taimaka sosai wajen tafiyar da shirin su. Duk da bata sakarwa Nuratu fuska sosai amma kuma hakan yayi musu dadi ita da Daddy.
Daddy ya buƙaci ya karawa manyan ma'aikata hutun sati biyu kafin Ashraf ya samu sauki saboda wasu abubuwan ba zasu tafi dai dai ba idan ba Nuratu saboda kai kawon da take yi akan Ashraf, sauran kananun ma'aikata kuwa musamman masu ɓamgaren sai da kaya akayi musu umarnin da su koma aiki.
Jikin Ashraf yanayin sauki sosai musamman yadda Nuratu take bashi kulawa yana taimaka masa matuka.
Yau ma k**ar kullum Nuratu ta shirya breakfast zata tafi asibiti wajen Ashraf, ta manta ta bar wayar ta a bedroom da saurin ta ta nufi sama domin ta ɗakko. Tana ƙarasawa taji wayar tana vibration, wata baƙuwar number ta gani, sai da tayi k**ar bazata ɗaga ba sai kuma dai ta kara a kunnen ta tare da yin sallama.
Muryar da taji ta doki dodon kunnen ta ta matukar razana ta, take jikin ta ya hau tsuma ta nemi waje ta zauna a gefen gadon ta. Ta ɗaya bangaren kuwa wata dariya akayi ta mugunta sannan akace:
" Hmm Nuratu kenan daga yanayin shurun ki na tabbatar kin gane mai magana, to ina raye ban mutu ba maciya amana ke da uban gidan ki, wallahi sai na tona muku asiri gashi nan na fara ta kan ɗan nasa da yafi ji dashi saura ke."
"Saboda haka inaso ku shirya kuɗi nan da awa ɗaya kimanin doller dubu ɗari da hamsin ki kawo min a yau, idan kuka faɗawa hukuma wallahi zakiga abinda zan iya yi, zan faɗa miki inda zaki kawo kuɗin ke kaɗai sannan ki tahomin da wannan yaron junior don nayi kewar sa."
Ya ƙarasa maganar tare da kashe wayar.
Jefar da wayar Nuratu tayi akan gadon ta tare da rufe bakinta da hannayen ta guda biyu cike da firgici da tashin hankali, jikin ta sai tsuma yakeyi ta duburburce, ta miƙe zata fita ta juyo da sauri ta ɗakko wayar ta ta fara kiran layin Daddy, bayan ya ɗauka muryar ta a harɗe tace:
"Daddy Dr Sabo yana raye...."
Zumbur Daddy yayi ya miƙe daga kan gadon sa tare da faɗin:
"What!"
Cikin sauri da kaɗuwa tace:
"Eh Daddy ganinan zuwa karka fita Please!"
Ta faɗa tare da kashe wayar ta nufin hanyar fita da gudu. Kasancewar babu kowa a ƙasan ya saka ta fice gidan ba tare da kowa ya lura da halin da take ciki ba.
A palour ta tarar da Daddy yana kaiwa yana kawowa, da gudu ta shiga ta durƙushe a ƙasa tana faɗin:
"Daddy na shiga uku shikkenan asiri na ya tonu wallahi shine Daddy na tabbata kuma banda shi daman babu wanda zai turawa da Ashraf text"
Duk da Daddy shima yana cikin tsananin tashin hankali amma haka ya daure ya tambayi Nuratu duk yadda s**ayi ta labarta masa komai.
Yayi ajiyar zuciya sannan yace:
"dDman nayi tunani ko bai mutu ba saboda sak**akon binciken da na saka aimin yana nuna k**ar yana raye, saboda haka abinda nake so da ke shine kije ki shirya kuɗin yanzu aje a kai masa."
Miƙewa Nuratu tayi zumbur tace:
"Daddy kuɗin sunyi yawa is equivalent fa da kusan million 250..."
Katse ta yayi tare da faɗin:
"Kije ki shirya kuɗin."
Ba yadda zata yi haka ta miƙe ta nufi wata matattakala da take gefen palour wadda ta sada ta da wani katafaren palour, ta sunkuya ta janye Centre carpet ɗin da yake malale a tsakiyar palour ta ɗora hannunta daidai kan wani tile, take biometric key ya bayyana ta ɗora tafin hannun ta na dama kawai sai ƙasan ya fara ɓuɗewa, kan kace me hanya ta bayyana a tsakiyar palour ciki da wata matattakala ta shiga inda ya sada ta da wani killataccen ɗakin ajiya na sirri mai ɗauke da ɗakuna guda biyu.
Ɗakin da yake kallon ta ta shiga, nan ma sai da ta ɗora tafin hannun ta sannan ya buɗe ta shiga, akwatunan tsaro ne na ajiya aƙalla guda biyar a ɗakin maƙare da dukiya ta ban mamaki, na farkon ta nufa tare da danna madannan sirri.
Bayan ta buɗe tayi arba da kuɗi cash in dollars sababbi k**ar buɗewar ido, nan ta fara ƙirga adadin da take buƙata kai da kai ta fito dasu, sannan ta buɗe wata drawer ta ɗakko wata irin leda mai duhu ta zuba kuɗin a ciki ta dauko ta fito ƙofar ɗakin ta koma ta rufe.
Dab da hawanta matattakalar da zata fito da ita ta tsaya ta kalli ɗaya ɗakin sirrin da yake a rufe, take tayi wata sanyayyiyar ajiyar zuciya tare da jinjina kai, sannan ta k**a matattakalar ta fito ƙofar ta koma ta rufe k**ar ba'a halicci komai a wajen ba sannan ta mai da carpet ɗin.
A tsaye ta tarar da Daddy in da ta barshi, sannan ta kalke shi tace masa:
"Gasu na ɗebo"
Kallon ta yayi sannan ya gyaɗa mata kai daga bisani yace:
" Ji tabbata kin biya kin ɗakko junior a makaranta ki tafi dashi, yana gidan gona ta na bayan gari yanzu nima yai min text ..."
Wani irin firgici Nuratu ta shiga da taji yace ta tafi da junior, ta kalli Daddy zatai magana yace da ita:
"K kwantar da hankalin ki, Dr Sabo bazai taɓa cutar dashi ba."
Jinjina masa kai tayi ba don ta so ba ta juya ta fita ta hau motar ta zuciyar ta k**ar ta fashe don tsoro ta biya ta ɗakko junior a makaranta s**a nufi gidan gonar.
Iya kewayen ta da tayi ba taga alamar sa ba, ta tambayi masu gadi da ma'aikatan wajen babu wanda yace ya ga baƙo, dawowa tayi cikin mota ta zauna ta rasa me zata yi.
Wayar ta da take hannun junior yana game ce ta fara ringing, da sauri ta karba ta kara a kunnen ta, muryarsa taji yana cewa:
"Ki ƙaraso bayan gidan gonar."
Kafin tace komai ya kashe wayar.
Iya Sanin ta bayan gidan gonar jeji ne sosai, amma haka ta danne tsoron ta ta nufi wajen, text message ne ya sake shigowa wayar ta in da akai mata umurnin da tayi parking a in da take ta fito.
Tsaida motar tayi tai ta maza ta fito da ledar kudin a hannun ta ɗaya hannun kuma rike da junior zuciyar ta sai bugawa takeyi take ta fara ambaton "Hasbunallahu wani'imal wakeel."
Tana tsaye kimanin mintuna biyar ba wanda yazo, sai zuwa can taji maganar sa ta bayanta:
"Lllai yaro ya girma."
A tsorace ta juya s**ayi ido biyu dashi zuciyar ta tana bugawa da ƙarfi jikinta ya fara rawa, tabbas shine amma tayi mamaki matuƙa da ya kasance a raye.
Kamar yasan abinda yake ranta ne yayi murmushin takaici yace:
"Jina mamakin gani na a raye ko?"
Sannan ya sunkuya ya rage tsawon sa dai dai dana junior ya saka hannunsa ya shafa kansa yace:
"Boy kana lafiya, amma kayi saurin girma fa.."
Para ƙanƙame junior tayi a jikin ta wanda shima hakan yayi ya ɓoye fuskarsa a tsakanin ƙafafuwan ta.
Miƙewa yayi sannan ya kalketa fuska a ɗaure yace:
"Ku hanzarta bayyanawa duniya abinda kuke ɓoyewa Nuratu saboda kullum a cikin fushin Ubangiji kuke musamman ma ke, idan baku ɗauki mataki ba to ni zan ɗauka."
Ya saka hannunsa ya fizgi ledar kuɗin daga hannun ta sannan ya miƙe ya nufi cikin jejin har sai da ta daina ganin sa.
Nuratu tana tsaye tana nazarin maganganun sa, tabbas ya faɗi gaskiya duk da tayi wa Daddy alkawarin ba za'a ji zancen nan a bakin ta ba amma tabbas jikin ta yana bata lokacin bayyanar sirrin su duniya ta sani yazo. Juyawa tayi ta shiga motar ta ta bar wajen da gudu.
Bayan ta shigo cikin gari ta fara labartawa Daddy yadda s**ayi a waya, sannan ta sanar masa da cewar ta tafi asibiti wajen Ashraf saboda taga missedcall ɗin sa rututu.
Shigar ta asibitin ke da wuya ta haɗu da Mummy ta rako aminiyar ta zata tafi tazo ta duba Ashraf, durƙusawa tayi har ƙasa ta g*ishe su, sama sama s**a amsa mata ta wuce ta barsu a wajen hannun ta riƙe da junior ko a jikin ta in da sabo ta saba.
Ɗakin da Ashraf yake ta nufa a zaune ta ganshi ya jingina bayansa da katifar gadon da yake kai gaban sa ga plate ɗin abinci, faten dankalin turawa ne a ciki da naman kaza sai juya cokalin yake yi ya kasa ci, ganin shigowar ta yasa ya ɗaure fuska ya ɗauke kansa alamar fushi yake da ita. Can cikin ran sa kuma daɗi yaji da zuwan ta.
Ƙarasawa in da yake tayi ta zauna a kujerar da take bakin gadon, sannan tace:
"Ina wuni"
Juyowa yayi ya kalleta ido cikin ido yace:
"Ina kika je?"
Sunkuyar da kanta tayi tana kokarin daidaita yanayin ta sannan ta ɗago tace:
"Daddy ne ya aike ni."
Ɓata rai yayi sannan ya buɗe bakin sa a hasale yace:
"Wai ko munyi aure haka zai dinga kiran ki lokacin da yake so ya aike ki?"
Murumushi Nuratu tayi sannan ta kalleshi tace:
"Ai shiyasa ake so ka iya komai saboda komai ya dawo hannunka tunda kai ya k**ata kayidaman bani ba."
Ƙara hade fuskar sa yayi a sigar shagwaɓa yace:
"Shine kuma zaki barni da yunwa har yanzu Ban karya ba inata kiran ki kinƙi ɗagawa"
Murmushin tsokana ta kuma yi masa fuskar ta da alamar sun fara nasara sannan tace:
"Kayi haƙuri gani nazo kaci abincin ka kawai."
Wani mugun kallo yai mata fuska ɗaure yace:
"Kin sani sarai na daina cin abincin kowa in ba ke kika yi da kanki ba ko?"
Ya faɗa tare da saka hannunsa ya ture plate ɗin da yake gaban sa. Sai sannan Nuratu ta tuna da girkin da tayi masa, tashin hankali yasa ta manta shi a gida.
Ta kalleshi duk ya rikice k**ar wani yaro tasan halinsa tun da yace bazai ci ba to bazai cin ba.
"Nayi maka girki na manta a gida ban dauka zan daɗe a inda naje ba da naga na dau lokaci sai na biyo ta nan, amma bari na saka Ameerah ta kawo maka nasan yanzu ta dawo daga school."
Ta ƙarasa maganar tare ds fara lalubo number Ameerah a wayarta.
Jinjina mata kai yayi kawai, sannan ya maida hankalin sa kan junior da yake game a ɗaya wayar Nuratu tun da s**a shigo.
Bayan Ameera ta kawo kayan abincin Nuratu tace mata ta tafi da junior gida haka kuwa akayi s**a tafi gida tare.
****************
BAYAN SATI BIYU
Satin Ashraf biyu a asibiti aka sallameshi saboda babu laifi ya samu lafiya sosai, Nuratu kuwa tun da aka sallameshi daga asibiti ta rage zuwa gidan ta k**a kanta tun daga ranar da za'a sallameshi daga asibiti ta k**asu shida Mummy suna tattaunawa k**ar haka:
"Ashraf yadda kake zaƙewa yarinyar nan ya farw bani tsoro, anya baka kamu da son ta ba kuwa?"
Murmushi yayi sannan yace:
"Lallai Mummy da wuri za'a ciki da yaƙi, ai shi yaƙi ɗan zambo ne, tukunna ma kuwa sai kinga ta fara narkemim sannan zakisha mamaki, nifa sam bata tsarin matan da nakeso yaudara ce kawai so nake mu cika burin mu kawai"
Wata irin dariya Mummy tayi mai cike da nishadi.
Jin hakan ya saka Nuratu ta shiga taitayin ta, tun da daman ita duk abinda takeyi saboda Daddy takeyi ko ƙaɗan bata taɓa jin tana son Ashraf ba, kuma ta san sharrin Mummy kala kala daman za'a rina.
Haka ta duƙufa sosai wajen nemawa kanta mafita, da kawo cigaba a aikin ta, tayi alƙawarin itama zata nuna masa nata salon ta hanyar ƙauracewa masa domin ya tabbatar da ita ma ba kanwar lasa bace.
A wannan satin dandazon ƴan Rano ne s**ai ta tururuwar zuwa domin duba Ashraf daga waje waje kasancewar Daddy mutumin kirki ne, alkhairan sa babu inda basa isa lungu da saƙo. Har Malam Muhammadu sai da yazo duk da tsufa ya k**ashi sosai amma haka aka rako shi yazo duba Ashraf.
Rashin zuwan da Nuratu take yi ba ƙaramin ɗagawa Ashraf hankali yake ba amma haka dole ya jure ya ƙagu da ya samu sauki ya koma office atleast zai dinga ganin ta akai akai.
Bayan ƴan kwanaki hutun su ya ƙare ta koma bakin aiki, ta bada himma sosai wajen kula da komai fiye da da, Daddy a kullum ƙwazon ta sake birgeshi yake yi. Musamman yadda yaga take sake zagewa sosai wajen kawo wa harkokin sa ci gaba.
Wannan shekarar da tafiye-tafiye ta zowa Nuratu, hakan take daurewa tayi tafiyar, sai dai duk inda taje tana ƙoƙarin kare mutuncin ta sannan sam bata bada ƙofar da za'a kawo mata raini.
Shikuwa Ashraf hankalin sa yanzu ya kwanta sosai bashi da wata matsala, a kullum Mummy da ɗa kwantar masa da hankali takeyi tana bashi ƙwarin gwiwa, babban abinda yafi damun sa shine yadda zai bijiro mata da yana son NURATU.
**********************
BAYAN WATA SHIDA
Komai na rayuwa ya fara yiwa Daddy dai-dai musamman ganin yadda Nuratu ta shigo cikin rayuwar su ta canza shi ta canja ɗan sa. Ashraf ya nutsu sosai ya mai da hankalin sa kan aiki ya samu gogewa sosai a wadannan watannin, mutane da dama har mamakin hazaƙa da kwakwalwar Ashraf suke yi, zuwa yanzu majority na tafiye-tafiyen da s**a shafi harkokin su Ashraf ne yake yi saboda yana jin kishi idan Nuratu ta tafi.
Hankalin sa ya kwanta sosai yanzu babbar matsalar sa shine yadda zai tunkari Mummy da yana son auren Nuratu. Gaba ɗaya a yanzu bashi da damuwar da ta wuce wannan ya rasa yaya zai yi, dai dai da ma'aikatan office ɗin sun fahimci Ashraf yana son Nuratu.
Sam baya ɓoye yadda yake jin ta, duk da akwai masu sawa Mummy ido sosai a kansa, duk sanda s**a kai mata rahoto tana bagarar dasu ne da cewar "Ashraf yasan me yake yi bazai bani kunya ba."
Hankalin Ashraf ya gaza kwanciya kwanannan, gani yake yi k**ar za'a zo a ƙwace masa Nuratu ya rasa yadda zai yi can sai wata dabara ta faɗo masa a ransa yace koma wacce ce sai anyi ta dani a sati nan.
Ita kuwa Nuratu ta daɗa yin taka tsantsan da lamarin sa, tana mu'amala dashi babu yabo babu fallasa, ta kame kanta saboda ita a yanzu duk abinda zai bata matsala a rayuwar ta gudun sa takeyi.
Ranar wata safiyar Asabar Nuratu suna zaune k**ar yadda s**a saba suna hira bayan sun gama breakfast, Daddy ya kirata a waya yace tazo yana son ganinta tazo tare dasu Anuwar. Duk da tayi mamakin wannan kira na Daddy amma ta kawar da tunanin, ta kalli su Anuwar tace musu:
"Ku shirya mu tafi Daddy yana kira."
Haka s**a shirya gaba dayan su s**a tafi.
Isar su gidan ke da wuya Nuratu tayi mamakin yadda taga mutane a babban palour Daddy, su malam Muhammadu ne da yayan mahaifin Daddy da duk wani babba na family Daddy, can kuma Ashraf ta hango zaune kusa da Mummy. Da mamakin ta ta ƙarasa ta durƙusa ta g*i da kowa sannan ta nemi waje ta zauna.
Daddy ya ɗago ya kalleta yace:
"Nuratu nasan zakiyi mamakin wannan kiran da kuma ganin mutane hakan, to Ashraf ne yaje ya dakko su wai lallai sai an daura muku aure a yau, shiyasa na saka a kirawo ku idan kin amince za'a daura auren yanzu ga Anuwar nan sai ya bada auren."
Duk Maganar da Daddy yake yi kan Nuratu a ƙasa ta kasa cewa komai kanta ya kulle ta rasa me zata ce, "innalillahi wa'inna ilahi raji'un" kawai take ambato a ranta tare da faɗin "me Daddy yake shirin yi?"
Gaba ɗaya ta rasa nutsuwar ta ta rasa me zata ce, ta ina zata fara, zuciyar ta kawai bugawa takeyi da sauri, ganin hakan yasa Ashraf ya taso daga inda yake ya zo ya tsuguna a gabanta yace:
"Ya kikayi shiru, ko bakyaso na ne? Kin yi min alƙawarin fa zaki rayu da ni."
Zata buɗe bakin ta kenan akayi sallama aka shigo palour, miƙewa Daddy da Nuratu s**ayi tsaye da sauri cike da tashin hankalin ganin wanda yake shigowa.
Dr Sabo ne ya shigo tare da wani saurayi da bai wuce shekara 30 ba dagani kasan ɗan sa ne saboda k**annin da suke yi ya ɓaci.
Shigowar sa ke da wuya ya nufi inda Daddy yake ran sa a ɓace yace:
"Amma Ahmadu kasan da cewar wannan daurin auren da zaka yi kuskure ne, kuma ka sani haramun ne ɗaura aure kan wani auren ko?"
Hankalin kowa na wajen yayi masifar tashi musamman Ashraf da ya tsaya cak ya kasa fahimtar me ake nufi, a hankali ya ƙarasa in da Dr Sabo yake ya cakumi wuyan rigar sa yace:
"Kai kuma waye kazo ka wargaza min maganar aure na, waye kai?" Ashraf ya faɗa cike da ƙaraji.
Fincike wuyan rigar sa yayi daga hannun Ashraf sannan yace:
"Nine wanda nayi maka text message akan medical report ɗin ka, nasan abubuwa da dama game dakai wanda kai baka sani ba.."
Ya ƙarasa ya finciko junior daga hannun Nuratu da tun da ya shigo ta rukunƙume dan ta tana kuka sannan ya zo ya k**a hannun Ashraf ya damƙa masa junior yace:
"WANNAN YARON ƊAN KA NE NA CIKIN KA..."
Wani irin wawan mari Ashraf ya kaiwa Dr Sabo ya goce, sannan ya kalkeshi fuskarsa cike da tashin hankali yace:
"Mahaukacin ina ne kai..."
Dr Sabo ya katse shi da faɗin:
"Ni ba mahaukaci bane da hankali na idan kana da musu akan hakan tafe nake da likitocin da zasu tabbatar maka da hakan saboda na lura wannan Mmhaifin naka so yake ya kashe ka da ranka."
Ya ƙarasa maganar yana nuna Daddy da hannunsa. Sannan ya juya ya kalli Anuwar yace:
"Nasan kai likita ne zaka iya tabbatar mana da hakan?" Amsawa Anuwar yayi cike da ƙwarin gwiwa.
Dr Sabo ya juya ya kalli su Malam Muhammadu yace don Allah Baba kuyi mana afuwa zamu warware komai inshaAllahu. Gaba ɗayan su shiru s**ayi, ba wanda yake iyayi yin magana, Mummy kuwa komawa tayi ta zauna tunanin ta ya tsaya cak!
Banda sautin kukan Nuratu babu abinda yake tashi a dakin k**ar wadda ake yankar naman jikin ta. Fita waje Dr Sambo yayi ya shigo da kayan aiki dana gwaji kala-kala yai wa Anuwar umarni da ya dauko jinin Ashraf da na junior, haka kuwa akayi, ya ɗauka bayan ya kammala gwaje-gwajen sa jikin sa a sanyaye ya zare safar hannunsa ya zube akan kujera ya k**a kansa da hannunsa biyu yana faɗin "innalillahi wa'inna ilahi raji'un."
Sannan Dr Sabo ya kirawo wasu daga cikin ma'aikatan da yazo dasu s**a fitar da sak**akon ya miƙawa Ashraf. Cike da tashin hankali Ashraf ya karanta sak**akon sannan ya kalli Anuwar yace:
"Don Allah da gaske ɗa na ne k**ar yadda na gani yanzu?"
Jinjina kansa Anuwar yayi alamar "eh" cike da jimami.
Sannan Ashraf ya mai da hankalinsa kan Daddy wanda sai kai kawo yake acikin ɗakin cike da jimami, ya ƙaraso dab da Daddy hannun sa riƙe da junior yace:
"Daddy... da gaske ne..."
Ya faɗa bakin sa yana sarƙewa, ɗagowa yayi ya kalleshi sannan ya mai da hankalin sa kan Nuratu ba tare da yace komai ba.
A hankali Ashraf ya nufi inda Nuratu take ta faman kuka ya durƙusa a gaban ta k**ar wani sususu hannun sa still riƙe da junior da shima yake ta rusa kuka tun dayaga Nuratu ta fara kuka shima yake yi, yace mata:
"Dagaske ne Nuratu...?"
Hannunta ta saka ta fizge junior a hannun sa ta rukunƙume shi k**ar wata zararriya ta zaro idon ta tace masa:
"Baku isa ku rabani da ɗana ba."
Su Malam Muhammadu da s**a gaji da kallon wannan drama tasu s**a magantu, Malam Muhammadu ya kalli Dr Sabo yace:
"Bawan Allah harkar arziki ce ta kawo mu nan, kazo ka kawo mana ruɗani don Allah ka faɗa mana me yake faruwa"
Gaba ɗaya ƴan uwan Daddy s**a fara faɗin:
"Ai shine sai kayi bayani tun da kai kazo da maganar."
Gyaran murya yayi sannan yace:
"Kuyi haƙuri wannan lamari ne mai cike da sarkakiya da ruɗani amma babu wanda zai warware wannan matsalar sama da Nuratu ita kaɗai ce kawai zata bada labarin yadda komai ya wakana."
Hankalin kowa kan Nuratu yayi ana tambayar ta, gaba ɗaya wani irin kallo ta bisu dashi k**ar bata gane me suke cewa. Miƙewa Daddy yayi ya nufi fridge ya dakko robar ruwa mai sanyi ya nufo in da take ya sukuya ya buɗe sannan ya miƙa mata ta karɓa tasha ta zuba a fuskarta, a hankali ta fara dawowa cikin hayyacin ta, sannan Daddy ya kalle ta yace:
"Nuratu! ranar wanka ba'a ɓoyon cibi dukkanin mu mun san da zuwan wannan ranar, ki kwantar da hankalinki kiyi musu bayani kinji."
Girgiza kanta tayi alamar "to" sannan ta juyo ta kalli Ashraf dayake durƙushe a gabanta k**ar wani gunki ta k**a hannunsa ta haɗa dana junior tace:
"junior ɗan ka ne na cikin ka kuma ni na haifeshi a cikina..."
Kuka mai ƙarfi ne ya sarƙe mata murya, ta miƙe da gudu ta nufi toilet Ameera da Mummy s**a bi bayan ta.
Written by:
Khadija Aliyu Ibrahim
(The Healer's Pen)
[email protected]
Read our free Books 👇
https://www.arewapen.com/book?id=6973a231b4ed2df0425189c7
Whattpad 👇
https://www.wattpad.com/user/khadijaaliyuibrahim?utm_source=ios&utm_medium=link&utm_content=share_profile&utm_campaign=invitefriends&wp_page=home&wp_uname=khadijaaliyuibrahim
Facebook 👇
https://www.facebook.com/hennabykdj
GARGADI❗️❗️❗️
Labarin 'NI DA KANNENA' taska ce daga fasahar Khadija Aliyu Ibrahim. Kuma kyauta ne.
Satar rubutu ba nishadi ba ne, cin amana ne ga marubuciya da kuma kokarin toshe hasken hazakarta.
Idan ka ga wannan rubutu ba tare da sunana ko link ba, ka sani ba daga gare ni yake ba.
Sannan duk wanda muka k**a da wannan laifin zai fuskanci fushin hukuma.
Saboda haka a kiyaye.
WhatsApp channel 👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCiw48qIzt1JDE4y0l
"BISMILLAHIRRAHMÁNIRRAHEEM!"
"WASSALÁTU WASSALÁMU ALÁ RASULULLÀHI (SALALLÀHU ALAIHI WA SALLAM.)"
'NI DA KANNENA'
CHAPTER FIVE (A)
WAYE DADDY?
Asalin sunan sa shine 'Alhaji Ahmad Abubakar Maihula' asalin sa mutumin Kano ne a ƙaramar hukumar Rano, mahaifinsa Malam Habu ya kasance bafulatani mahaifiyar sa kuma Halimatu cikakkiyar bahaushiya ce.
Su biyar iyayen su s**a haifa uku maza biyu mata, Daddy shine ɗa na biyu, sai babbar yayar su Hajiya Asiya wanda Allah yai mata rasuwa bata taɓa haihuwa ba, sai wanda yake bin Daddy malam Abdullahi, sai na huɗun malam Mahmuda sai ƙaramar su A'ishah da sukewa laƙabi da A'i.
Gaba ɗaya mahaifiyar su ce ta haifesu, mahaifiyar su ta rasu tun suna ƙanana, wanda hakan wasu suna faɗin yana da alaƙa da mutuwar mahaifin su, saboda tun da ta rasu shima ya kamu da rashin lafiyar da aka kasa gane kanta, bayan shekara uku da rasuwar ta shima Allah yai masa rasuwa, haka kulawar su kacokam ta koma hannun yayan mahaifinsu tilo wanda shi ya riƙe su tare da matarsa riƙo na tsakani da Allah.
Kasancewar Daddy shi yafi faran faran da mutane hakan ya saka jinin su ya hadu da wani abokin mahaifin sa malam Muhammadu wanda shi kuma sana'ar sa fatauci ce, yana sarar huluna kala kala musamman a garin Maiduguri ya kai su garuruwan kudu, hakan ya saka ya fara jan Daddy a jikin sa ya koya masa harkar kasuwanci sannan ya saka shi a makarantar boko yana tafiya dashi fataucin idan anyi hutun makaranta.
Hakan ya saka daddy ya ƙara ƙwarewa sosai a harkar kasuwanci ya goge matuƙa, bayan ya kammala secoundry school ne s**a tsunduma harkar kasuwanci ka'in da na'in har takai ga Malam Muhammadu bai cika fita ba duk inda ya k**ata Daddy ne yake zuwa kasancewar sa yana da nasibin kasuwanci sosai.
Kwanci tashi kasuwancin su Daddy ya haɓaka har ta kai ga suna fitar da kayan su zuwa maƙotan ƙasashen Nigeria k**ar su Nijar Cameroon da Chadi. Ganin yadda kasuwancin ya karɓi Daddy sosai ya saka Alhaji Muhammadu ya shawarci yayan mahaifinsu akan a raba musu gado domin a sallami Daddy ya zuba kuɗin sa a kasuwa a wannan lokacin ma duk ƴan uwansa sunyi aure.
Haka kuwa akayi aka raba gado kowa aka bashi kason sa shi kuma Daddy ya zuba masa a harkar kasuwancin huluna, daga baya ya faɗa harkar fata, a hankali Ubangiji ya saka masa albarka ya fara tara dukiya.
Bayan Daddy yaga ya fara samun dukiya sai hankalinsa kuma ya koma kan karatu, kasancewar yana da sha'awar sa sosai kuma yafi zuwa garin Maiduguri sai kawai ya yanke shawarar ya samu admission awannan makarantar hakan zai fi masa sauƙi a ɓangaren kasuwancin sa.
Haka kuwa akayi bayan ya shawarci yayan mahaifinsa da Alhaji Muhammadu s**a yarje masa ya shiga jami'ar Maiduguri ya fara degree sa na farko a fannin kasuwanci.
Sai da yayi nisa sosai yana shekarar ƙarshe Allah ya hada shi da Mummy wato asalin sunan ta 'Suwaiba' wadda ita kuma ƴar asalin Maiduguri ce itama tazo karatu lokacin tana ajin farko a bangaren Shari'ah,.
Soyayya mai ƙarfi ta ƙullu a tsakanin su, bayan Daddy ya kammala karatun sa ya aure ta ya kawo ta nan Kano tare da nema mata transfer taci gaba da karatun ta a jami'ar BUK.
Bayan shekara guda da yin auren su ta haifo dan ta namiji wanda Daddy ya saka masa sunan Malam Muhammadu ake masa laƙabi da 'Ashraf' tun daga haihuwar Ashraf dukiyar Alhaji take ƙaruwa yake ta zuba kuɗi a kasuwanci kala kala wanda hakan ya daɗa bunƙasa dukiyar sa, daɗin daɗawa ga alkhairai da yake wa ƴan uwa da abokan arziƙi musamman yadda yayi dacen mata, Mummy mace ce mai kirki da son mutane bata bambantawa tsakanin dangin ta da nasa.
Har Ashraf ya kai shekaru goma a duniya ko ɓatan wata Mummy bata ƙara yi ba, gashi ya gamu da larurar ciwon zuciya yasha wahala sosai yana ƙarami, saboda likitoci sun tabbatar da cewar zuciyar sa na da rauni saboda wani rami da yake a tsakiyar ta, shikuma idan aka samu irin wannan sai dai ayi haƙuri a lallaɓa mutum, kasancewar da gata ya saka aka dinga kula da Ashraf har ya samu sauki amma ko da yaushe yana ƙarƙashin kulawar likitoci.
Hakanne ya saka hankalin su ya tashi, ga rashin haihuwa, sai s**a shiga neman shawarwarin likitoci bayan gwaje gwajen da akayi musu aka tabbatar musu da cewar Daddy ba zai ƙara haihuwa ba saboda gaba ɗaya kwayoyin haihuwar sa sunyi rauni.
Wannan matsalar ba ƙaramin daga masa hankali tayi ba hakan ya jefa shi cikin damuwa matuƙa musamman da s**a je kasashen waje har uku aka ƙara tabbatar musu da hakan.
Ita kuwa Mummy rarrashin sa ta shiga yi tare da yi masa alƙawarin zata zauna dashi a hakan har tsawon rayuwar ta. Hakan da take masa akodayaushe ya saka yake ƙara masa ƙwarin gwiwa wanda ya koma kan kasuwancin sa ka'in da na'in ya fara buɗe kamfanoni guda biyu wanda daga baya ya fara buɗe wasu a ciki da wajen Kano sannan ya ɗebo ƴaƴan ƴan uwan sa da na ƴan uwan Mummy ya zuba su a kai kasancewar duk ya ɗau nauyin karatun su.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafi masa a yadda yakeso kasuwancin sa yana haɓaka har zuwa lokacin da NURATU ta shigo rayuwar sa s**a ƙulla wata yarjejeniya ta sirri wanda hakan ya kawo sauye sauye masu yawa a rayuwar sa.
********************
BAYAN SATI ƊAYA DA YIN WALEEMA
Acikin sati guda zuwa yanzu banda matsin lamba babu abinda Nuratu take fuskanta a wajen Ashraf. Duk lokacin da yake buƙata haka zai kirata a waya ko ya tako yazo, duk kokarin da take yi na kai zuciyar ta nesa abun ya fara isar ta, musamman Anuwar da Ameerah duk da ta ja musu kunne sosai akan ko da wasa kar su nuna masa wani abu.
Ita Ameera bata da matsala amma shi Anuwar kwanannan ya rage zama ma a gida yawanci a asibitin su yake wuni ko da bashi da aiki ya gwammace ya tsaya ya taya abokin aikin sa nasa aikin.
Duk da matakin da Anuwar ya ɗauka baiwa Nuratu daɗi ba amma da ta tabbatar ga a inda yake wuni sai ta kwantar da hankalin ta kasancewar bata so wata rana wani abun ya haɗo su da Ashraf tun da ta lura kallon kallo suke yiwa juna.
Yau ma k**ar kullum Nuratu tana zaune a palour ƙasa tana aikace-aikacen ta a computer, misalin ƙarfe 4:00 na yamma Ashraf ya shigo tare da yin sallama, ɗagowa tayi a sanyaye ta amsa masa, bai nemi izini ba ya zauna kujerar da take kallon inda take, sai da ya ƙare mata kallo sannan yace:
"Ina kiran ki baki ɗaga ba."
Sai sannan ta ɗakko wayar ta taga missedcall ɗin sa har biyar sannan tace:
"A silent take ina aiki saboda an kusa komawa aiki."
Kau da kansa yayi sannan ya miƙe ya nufi fridge ya ɗauko coke ya buɗe ya dawo ya zauna, ganin abinda yayi ne yasa tayi saurin cewa:
"I'm sorry na sha'afa, gidan ne ba kowa, bari na kawo maka abinci."
Miƙewa tayi bai ce komai ba ya bi bayan ta da kallo. Bayan ta shiga kitchen ɗin ne ta tuna tuwon shinkafa s**a yi da rana miyar egusi, to ba ta da tabbacin ko Ashraf na cin tuwo hakan ya saka ta dawo domin tambayar sa.
Da mamakinta ta ga wayar ta a hannun sa, tsayawa tayi tana kallon sa da mamakin ya'akai ya iya buɗe wayar, duk da yasan Ashraf software engineer ne amma abun ya matuƙar bata mamaki.
Kallon sa tayi da kanar bata lura da abinda yake ba sannan tace:
"Tuwon shinkafa ne miyar egusi zakaci?"
Gyaɗa mata kai yayi alamar"eh" yana danna wayar ba tare da ya ɗago ba.
Tayi mamakin yadda Ashraf yaci tuwo sosai, ƙura masa ido tayi tana kallon sa da mamakin ta taga ya rame a wannan yʼan kwanakin bata san dalili ba.
Har yanzu wayar ta tana hannun sa ta rasa me yake yi da ita, can da ya gama abinda zai yi kawai ya miƙa mata, hannu tasa ta karɓa ba tace komai ba sai daga baya tace:
"Yak**ata mu fara training tun da kaga yanzu an ware maka special part da zaka kula dashi a office, is better kasan wasu abubuwan."
Sai sannan ya ɗago kai ya kalleta a dai dai lokacin da ya miƙe yana wanke hannunsa a sink ɗin kusa da dinning ɗin sannan yace:
"Ba wannan bane a gaba na tukunna, kece a gaba na idan munyi aure sai ki koya min a hankali."
Murmushin yaƙe tayi, tare da jinjina wannan kalar yaudara ta Ashraf sannan tace:
"Amma dai kasan Daddy yace sai ka maida hankali ka fara aiki sosai a office ya yaba da ƙwazon ka sannan zamuyi aure ko?"
Kallon ta kawai yayi tare da ƙura mata ido yace:
"Wannan nasani ke kika sauya masa ra'ayi, da ai ba haka yace ba, saboda ba kya so na shiyasa."
Ya numfasa yaci gaba da cewa:
"Nuratu ko me zakuyi ke dashi wallahi sai na aure ki."
Sunkuyar da kanta kawai tayi tana faɗaɗa tunanin ta, tabbas har ga Allah tasan ko da wasa bata son Ashraf tana biye masa ne kawai saboda a zauna lafiya kuma su samu nasara akan sa don ya mai da hankalinsa a office.
Ɗago kam ta tayi sannan tace:
"Ni ai bance bazan aure ka ba, amma kawai ka fara maida hankalin ka akan office tukunna, sannan me kayi min acikin wayata? banaso ka dinga monitoring komai nawa, wasu abubuwan sirri ne kuma babu kyau."
Murumshin rainin hankali yayi sannan ya kalleta yace:
"idan zan yi monitoring calls ɗinki sai na taɓa wayar ki? Ni bana yin haka, kawai hotunan ki na tura a wayata."
Kallon sa kawai tayi da dukkan alamu bata yarda ba. Miƙewa tayi ta bar dinning ɗin shima daga bisani ya biyo bayanta a dai dai lokacin da Ameerah s**a shigo tare da junior.
Hannun sa ya budewa junior alamar ya taho, shikuwa bai je ba sai daya kalli Nuratu tayi masa alama da ido sannan ya tafi ya rungume Ashraf.
Nuratu tsayawa tayi tana kallon su tana murmushi saboda ta lura tun da Ashraf ya fara zuwa gidan yake jan junior a jikin sa. Haka s**a ci gaba da wasannin su sai da akayi sallar magrib sannan Ashraf ya tafi.
A bangaren Mummy kuwa, nunawa daddy take batason auren Ashraf da Nuratu duk da har cikin zuciyar ta bata so amma tayi imani ita kaɗaice hanyar da zasu bi don su rabasu don idan idan ta nuna tana so ayi dole zasuyi zargin suna shirya wani abu.
Yadda ta ɗauki lamarin da zafi, har mamakin ta Daddy yake yi, tun yana yi mata faɗa har ya dawo yi mata nasiha, yana yawan nusashheta akan bata saba yiwa Ashraf abu ta ƙarfin tsiya ba saboda haka ta dai na hakan bazai taɓa sawa ta tanƙwara shi ba, amma ko a jikin ta sai ƙara ɗaukar zafi takeyi.
Shikuwa Ashraf bayan ya dawo direct ɓangaren Daddy ya nufa cikin wani yanayi na tashin hankali da firgici, ashe Mummy ta ganshi ta biyo bayan sa.
Hargitsa komai na ɗakin ya fara yi hankalin sa a tashe, sai sannan ya hango wani safe da Daddy yake ajiyar mahimman takardu ya fara ƙoƙarin buɗewa. Ga mamakin sa yaji safe ɗin a buɗe alamar an manta ba'a danna lambobin sirrin ba, bai jira ba ya hau bincike a ciki.
Cike da mamaki Mummy ta ƙaraso inda yake tana faɗin:
"Meye haka?"
Saboda iya sanin ta tasan duk fitinar Ashraf bai taɓa yi musu sata ba saboda duk abinsa yake bukata tana bashi ko da Daddy ya hana.
Ɗagowa yayi idon sa jajir ya kalleta tare da nuna mata wani text message da akayi masa a wayar sa a hanyar dawowarsa daga wajen Nuratu.
Cikin sauri ta saka hannu ta karɓa ta fara karantawa k**ar haka:
"ASHRAF KA BINCIKI MAHAIFIN KA AKAN YA FAƊA MAKA WAYE KAI, SANNAN KA BINCIKI MEDICAL REPORT DIN KA A WAJEN SA ZAKA GA ABINDA YAKE ƁOYE MUKU KAI DA MAHAIFIYAR KA NA TSAWON LOKACI."
Da ƙyar Mummy ta iya sarrafa kanta sannan ta nemi waje ta zauna, ta kalli Ashraf a dai dai lokacin da ya zaro wani file ɗin asibiti wanda sunan sa ne ajiki. Ya juya cikin tashin hankali yace:
"Mummy na ga wannan file a hannun Daddy yana rungume shi yana kuka lokacin ina asibiti a London, nayi nayi ya fadamin na meye ya ƙi, Mummy dole akwai abinda yake ɓoye mana!"
Girgiza kan ta tayi cike da tashin hankali sannan tace :
"Waye yai maka wannan text ɗin?"
Cikin sauri yace:
"Ban sani ba Mummy, ban san ko waye ba!"
Ya faɗa yana ƙoƙarin karanta abinda yake ƙunshe a file ɗin.
Wata irin muguwar ƙara Ashraf yayi tare da watsar da takardun da suke ciki yayi gefe ya durƙushe ya kifa kansa da bango.
Lokacin da Mummy tayi arba da abinda yake ciki, itama salati ta fara yi jikinta na rawa tayo kan Ashraf wanda ta ga sam baya motsi ga kuma jini yana biyowa ta hancinsa.
Wata muguwar ƙara itama ta saki tare da jijjiga shi iya ƙarfin ta. A dai dai wannan lokacin Daddy ya shigo bedroom ɗin nasa inda yayi arba da Ashraf a wannan halin sannan idon sa ya kai kan wannan file ɗin take Daddy ya fara kiran:
"Innalillahi wa'inna ilahi raji'un!"
Ba shiri ya sunkuci Ashraf a kafaɗar sa yayi waje dashi.
Daddy bai jira ambulance ba, ya dai yi musu waya cewar gashi nan jikin Ashraf ya tashi, da kansa ya tuƙa motar zuwa asibiti.
Ita kuwa Mummy ko takalmi babu haka s**a tafi. Shigar su asibitin ke da wuya s**a tarar da ma'aikatan suna jiran zuwan su cikin gaggawa aka shiga da Ashraf wani daki na musamman aka fara bashi taimakon gaggawa.
Mummy banda kuka ba abinda take yi tare da yiwa Allah kirari akan kar ya karbi ran Ashraf a wannan lokacin. Shikuwa Daddy banda "innalillahi wa'inna ilahi raji'un" ba abinda yake yi, ya kasa zaune ya kasa tsaye sai kaiwa da komowa yakeyi yana da na sanin yadda akayi ya dawo da takardun nan gida.
Juyowa yayi a fusace yace da Mummy:
"Wai ya akayi yasan da wannan file ɗin?"
Nan fa ta labarta masa yadda akayi, Daddy ya cika da mamakin waye wannan zai yiwa ASHRAF text?
Wayar sa ya zaro daga aljihun sa ya fita ya kirawo Nuratu ya sanar mata da halin da ake ciki, aikuwa a rude itama ta fito ta nufo asibitin. Shigowar ta ke da wuya Mummy ta k**ata tana jijjigata tana faɗin:
"Zaki kashe min ɗa, in ba ke ba waye yasan sirrin Alhaji na tabbatar kece ki kai masa wannan text ɗin muguwa azzaluma ki fita ki bani waje."
Ta faɗa tana hankaɗata, ita kuwa ban da haƙuri ba abinda take bata tare da yi mata rantsuwa akan bata san ma me yake faruwa ba.
Yanayin birkicewar da Mummy tayi tana kaiwa Nuratu duka tare da hankaɗa ta yayi yawa, duk da Daddy ya shiga tsakani amma ya rasa yadda zai yi, dole Nuratu ta haƙura ta koma gida tana kuka shaɓe shaɓe.
Kusan awa uku kenan da kawo Ashraf babu likitan da ya fito daga ICU ɗin duk hankalin Daddy ya tashi ita kuwa Mummy ta sandare a waje ɗaya ko motsi bata yi. Muryarta ta dashe ba abinda take ambato k**ar "Allah ka duba Ni, ya Allah ka dubani..." k**ar awa hudu da shigar da Ashraf likitan ya fito fuskar sa da alamar nasara, zumbur s**a miƙe s**a bi bayan sa.
Suna zaune a kujerun da suke office ɗin nasa fuskar su cike da damuwa da son sanin halin da ɗan su yake ciki. Dr Abdul ya kallesu cike da jimami yace:
"Alhaji munyi nasara mun ceto shi da ƙyar da taimakon Ubangiji..."
Wata ajiyar zuciya dukan su s**ayi sannan Mummy ta k**a kanta saboda wani sara mata da taji yayi.
Sannan Dr Abdul ya ci gaba da maganar sa:
"Amma Alhaji ya akayi akai sake haka har Ashraf ya sake shiga wannan yanayin? Kasan fa zuciyar ɗan adam sau daya kawai take bugawa, idan mutum ya rayu to ana biyu dole mutuwa zai yi."
"Ashraf ya hadu da first attack shekarun baya bai k**ata ace yanzu kun ƙara saka shi a damuwa ba, sannan jinin sa akwai kayan maye aciki wanda hakan ne ya saka shi fita daga hayyacin sa dandanan, gaskiya ya k**ata ku kiyaye nan gaba in ba haka ba zaku iya rasa shi."
"Zamu kiyaye inshaAllahu!"
Iya abinda Daddy ya iya faɗa kenan sannan ya juyo ya kalli Mummy wadda take riƙe da kanta ga jiri yana ɗaukar ta saura ƙiris ta faɗi daga kan kujerar da take kai, da sauri Daddy ya tallafota aka saka ta a wheelchair itama aka bata gado.
Ƙarin ruwa aka shiga yi mata da allurai kasancewar jinin ta ne ya hau sosai sannan akai mata allurar bacci daga baya.
Shi kuwa Daddy reception ya dawo ya zauna yayi tagumi zuciyar sa ta rasa tunanin me ma zatayi, wayar sa ce ta fara ringing, sunan Nuratu ya gani a jiki ba shiri ya ɗaga tare da da daidaita muryar sa.
Ta can bangare Nuratu kuwa ban da kuka ba abinda take yi, cikin dabara Daddy ya kwantar mata da hankali tare da faɗin "an samu nasarar ceto shi yana bacci zuwa da safe zai sanar mata da halin da ake ciki", amsa masa tayi tare da kashe wayar tana sharar ƙwallah.
Daddy mikewa yayi ya nufi ɗakin da Ashraf yake ya hangoshi ta window glass a kwance gaba ɗaya jikin sa na'urori ne a daure ko ta ina musamman ƙirjin sa, sannan ga iskar Oxygen a hancin sa.
Wani irin kuka ne ya ƙwace masa ƙasa ƙasa, ya durƙusa yana tausayin halin da ɗan sa yake ciki, musamman idan ya farka da wanne ido zai iya kallon sa.
Can kuma tunanin wanda ya turawa da Ashraf text ne ya fara dawo masa, laluben wata number ya fara yi a wayarsa tare da kira, ta wancan bangare aka amsa cike da ladabi sannan Daddy ya labarta masa abinda ya faru sannan yace yana buƙatar a binciko masa ko waye yayi hakan, cikin ladabi aka amsa tare da yi masa alƙawarin zuwa da safe zai ji komai, Daddy ya kashe wayar sa hankalin sa na kan Ashraf.
******************
WASHEGARI
Tun misalin ƙarfe 6:00 na safe Nuratu ta baro gida ta nufo asibitin, isar ta ke da wuya ta hango Daddy a zaune a wani ƙaramin palour yana lazimi. A hankali ta ƙarasa in da yake ta zauna fuskarta duk a kumbure ga dukkan alamu tasha kuka kuma bata samu isasshen bacci ba.
Bayan ya kammala addu'o'in sa ya ɗago ya kalleta, s**a g*isa ya hau bata haƙuri da lallashin ta, hakan yayi mata daɗi sosai, sannan s**a miƙe s**a nufi ɗakin da Ashraf yake ciki.
Yadda ta hango Ashraf ta window abun ya matuƙar ɗaga mata hankali, ko ba komai ta fara jin kewar sa, ta fara tuno zaman da s**ayi a gidan gona da yawan zuwa gidan ta da yakeyi, tabbas akace sabo tirken wawa. Duk da tasan wannan soyayyar da yake mata ta shiri ce amma ta tausaya masa sosai.
Wani kuka mai ƙarfi ne ya ƙufce mata ta juyo ta kalli Daddy tace:
"Wai me ya faru da shi ne haka?"
Nan fa Daddy ya faɗa mata labarin text message ɗin da akayi masa da yadda ya binciko medical report ɗin.
Hankalin Nuratu ba ƙaramin tashi yayi ba, ta juyo ta kalli Daddy cike da firgici tace:
"Meyesa Daddy ka karbo takardun daga banki? Daddy dole akwai wani mutum na uku da yasan sirrin mu.."
Ta durƙushe a ƙasa.
"Daddy don Allah kayi wani abu ina tsoron asirina ya tonu bana son a rabani da ɗana, duk wanda yasan wannan yasan sirri na Daddy, don Allah ka taimake ni..."
Wani azababben kuka ta cigaba dayi. Sunkuyawa Daddy yayi sannan yace:
"Ki kwantar da hankalin ki Nuratu wannan bashi da alaƙa da sirrin mu, nafi tunanin binciken da Suwaiba ta saka ake mata ne ya zo a hakan ya saka suke razana ta, amma banda ma'aikatan banki babu wanda yasan na karɓi wannan takardun amma inaso ki kwantar da hankalin ki na saka a bincika min ko ma waye sai ya ɗanɗana kuɗar sa."
Ajiyar zuciya Nuratu ta fara yi daga bisani Daddy ya umarce ta da taje ta duba Mummy. Bayan sun shiga s**a tarar da ita tana bacci hakan ya saka s**a fito sannan Daddy yayi mata umarni da ta koma gida.
Written by:
Khadija Aliyu Ibrahim
(The Healer's Pen)
[email protected]
Read our free Books 👇
https://www.arewapen.com/book?id=6973a231b4ed2df0425189c7
Whattpad 👇
https://www.wattpad.com/user/khadijaaliyuibrahim?utm_source=ios&utm_medium=link&utm_content=share_profile&utm_campaign=invitefriends&wp_page=home&wp_uname=khadijaaliyuibrahim
Facebook 👇
https://www.facebook.com/hennabykdj
Kano
Be the first to know and let us send you an email when The Healer’s Pen Hausa Novels posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.