Abdull Hausa Novels-A²

Abdull Hausa Novels-A² Abdull Alhaji Musa 10k

23/05/2026

Halacci Rahama Sadau

23/05/2026
23/05/2026

Tsohuwar ajiya Wasila

*TUKUNYAR MAYU*🏴‍☠️     ```LoVe aNd HoRrOr story```👽Follow the ✍️HAUSA NOVELS🫀WRITERS HUB📚 channel on WhatsApp: https://...
22/05/2026

*TUKUNYAR MAYU*🏴‍☠️

```LoVe aNd HoRrOr story```👽

Follow the ✍️HAUSA NOVELS🫀WRITERS HUB📚 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbCKiP1BA1f0aAySrq2F

By
Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️}*SADAUKARWA :* Fateema Abdou dite Mrs ƙarshen ƙauna🇳🇪*FCWA*☀️________________________

REPUBLISHED BY
Hausa Novels Writters Hub
08169130080 Whatsapp Only ✍️

PAGE 0️⃣0️⃣1️⃣

Idona tab ƙwalla nake kallon Dr Bilal wanda ya kasance shugabanmu ,ina mai sake maimaita kalmar “Gidan gawa Dr ? Wai ni ce zan kwana da gawa?”Ba tare da ya dube ni ba ya ce “nurse Fatee kin fi kowa sanin ba na magana biyu ki wuce kawai ki tafi, wannan gawar babban mutum ce ya zama dole a bata tsaro na musamman sannan ki tabbatar kin yi bincike a tsanake kin gano mene ne silar mutuwarsa”Ji na yi tamkar ya kwaɗa mini guduma,haka na soma tafiya ina waiwayensa ko Allah yasa ya ji tausayina ya ce na dawo amma ina tuni ya shiga sabgar gabansa.Ina buɗe ƙofar ɗakin gidan gawar na yi tsaye ina kallon gadajen da ke ɗauke da gawarwaki kowanne kuwa da likafaninsa in aka cire gawar mutumin da na zo dominsa.Jiki na ɗan kyarma na soma duduba gawar ina rubuta abubuwan da na samu matsayin result,ƙiiii! Na ji ƙofar da na bari a buɗe ta fitar da sautin.Da mugun sauri na juya sai na ga handle na motsi yayin da kuma ƙarar murza key ta ziyarci dodon kunnena.Cike da firgici na motsa da niyyar guduwa sai dai tamkar da akwai wani abu mai mugun ƙarfi da ya riƙe ni na kasa motsi.“A bani giya na sha na ɗan kurɓe” na ji wata murya ta faɗa amma babu alamun wanda yayi ta saboda ni ɗaya ce mai rai a ciki.Fiƙi-fiƙi haka nake baza na mujiyata waɗanda suke tsiyayar da ruwan hawaye k**ar wacce aka zuba wa yaji,dukkan illahirin jikina kuwa rawa yake.Takardar da ke hannuna ce na ji ta soma motsi,dubawar da zan yi sai na ga ta rikiɗa ta zama farin ƙyallen likafani daidai nan kuma na ga abin da ya girmi tunanina.Gawar mutumin ce ta tashi zaune raɗam kan gado,wani irin kallo ne yake jifa ta da shi da wasu IDON SHARRI(MRS SADAUKI) masu matuƙar firgici da kaɗa hantar mutum.Ban san inda ta haihu a ragaya ba sai tsintar kaina na yi kwance a gadon asibitinmu,gefena ƙawata ce Rahinatu ke zaune tana duba yadda ƙarin ruwan da ke maƙale a hannuna ke tafiya.“Ƙawata kin tashi? ” ta furta tana mai tasowa tare da ɗora hannunta kan goshina da nake jin tamkar zai tsage.Ban kai ga bata amsa ba Dr Bilal ya shigo yana mai cewa “baƙonmu ya iso tun da ta tashi ku yi sauri ku fito kafin ya farga babu wani a cikin jerin sunan da za a basa”sai kuma ya fice.Rahinatu ta ja tsuki tana mai cewa“duk duniya na tsani tsatsauran mutum,sam bai da mutumci kawai don ya ga tauraronsa yana haskawa.Kin ga tashi mu tafi don yana iya sawa ma a kore mu” ta ida faɗar haka tana mai cire mini ƙarin ruwan,ina shirin saukowa kuma wata nurse ta sake leƙowa ta ce “Rahinatu Dr Bilal ya ce me k**e jira alhalin ke ce za ki gabatar da kalaman farko na buɗe taro?” da wani irin mugun sauri Rahinatu ta fita tana yarfa hannu.Ni kuwa dakyar na iya ƙoƙartawa na tashi,duk jikina ciwo yake k**ar wacce aka ɗirkawa na jaki.Baƙon da za a yi yau yana da matuƙar muhimmanci wannan ya aka shirya abubuwa da yawa,ciki kuwa har da jawabin da Rahinatu za ta yi sannan ni kaina an bani topic ɗin da zan gabatar amma tsabar yadda aka jijiga ruhina na manta shaf.Ina fitowa direct ofis ɗin Dr Bilal na wuce so nake na yi ɗan watsa ruwa ko zan ji dama,ina buɗe toilet ɗin na yi tsaye ƙyam tamkar wacce aka shuka.Dukkan illahirin jikina kuma rawa yake,na fito da idona tulu-tulu ina kallonsa sam ban farga na yi suman tsaye ba sai da na ji muryar Dr Bilal yana kiran sunana firgigit na dawo hayyacina sai dai babu mutumen da na gani a yanzu yana fitsari.“Me ki ke jira? Me yasa k**e neman hanyoyi da za a kore ki Sweety?” Dr Bilal ya faɗa cikin taushin murya,na turo baki gaba kafin na shige banɗaki na share shi ba tare da na basa amsa ba.Wato Dr Bilal saurayina ne,amma in muna asibiti mancewa yake da wannan alaƙa yana yi mini tsawa k**ar sauran da ke ƙarƙashinsa.Sai da na yi wanka na fito,na ɗauki farar rigar likitoci na ɗora daga sama sannan na nufi can saman bene inda ake gudanar da taron.Ina shiga da fuskar mutumen nan na fara cin karo,fari ne dogo mai cikar ƙasumbar saje da kuma gemu.Sumar kansa doguwa ce sosai ba k**ar ta sauran maza ba,don har sai da ya ɗan toje ta daidai tsakiya.Fuskarsa sam babu alamun wasa,kana ganinsa ka kai matsalalen nan masu baiwa ahalinsu da kuma na kewaye da su wahala.A takaice dai bayan miskilanci akwai izza,girman kai da ɗagawa a tattare da shi,da sauri na ɗauke idona a kansa ganin ya juyo facing inda nake,na nemi wuri na zauna ina mai sunne kai zuciyata na ɗan dokawa yayin da idona ke hasko mini irin yanayin da na same shi.Zaune dai nake a cikin ɗakin taron amma sam hankalina bai wajensu,tunani ne barkatai ke kai komo a cikin laɓuɓuwar kwanyata da ba ta san komai ba sai soyayya.Ina cikin tunanin wasiƙar jaki na ji muryar Dr Rashid na cewa “Nurse Fateema ta zo kan dandamali domin gabatar mana da jawaben da ta samu dangane da binciken gawar da ta yi”Wani irin rasss na ji,yayin da kuma na ɗago kaina da mugun sauri ina kallon mutanen da ke wurin waɗanda kusan duk kallonsu ya dawo kaina.Dr Bilal na kalla sai na ga yana yi mini wani kallo,sai kuma a yanzu na tuna cewa lokacin da ina toilet ya ce na ɗauki takarda na nan kan teburi.Dakyar na iya miƙewa tsaye na nufi wurin,ƙafafuna na harɗewa cike da tsoro na ƙarasa Dr Rashid ya miƙo mini sifika.Shiru na yi kafin na ɗan lumshe idona nan take kuma na soma jin wasu jawabai na shigo mini kwanya waɗanda tabbas su ne s**a faru da ni a lokacin da na shiga ɗakin gawa.“Kamar yadda kuka sani ire-iren mutuwar nan ta zama ruwan dare game duniya,to yau ma irin ta ce ta faru ga yalaɓai Alhaji Lawan.A binciken da na yi na samu raunuka a wasu sassa na jikinsa waɗanda ido ba su iya ganinsu sai dai kyakkyawan ruhi.A takaice dai ƙafarsa ta hagu babu ita,sannan an cire sinadarin idonsa,hatta jinin jikinsa babu globules rouges/red blood cell hakan shi ya baiwa igiyar saita numfashinsa damar tsayawa cak,huhunsa kuma ya bushe ƙamas jijiyoyinsa kuma duk s**a tsinke.Waɗannan hare-hare da ruhinsa ya samu su ne kuma s**a bai wa shararrun likitocinmu damar saka masa oxygene sai dai abin da ba su sani ba shi wannan bututun iskan ba komai ba ne sai ...sai...sai...” yadda na ji an shaƙe mini wuya ya hana ni ƙarasa abin da nake so,a dole na buɗe idona sai dai babu kowa kusa da ni amma kuma tabbas ina jin hannu a maƙoshina.Cikin abin da bai fi minti biyu ba na fita hayyacina,na zube ƙasa da sauri aka soma bani taimako ina jin muryar baƙon namu yana cewa “ku ɗauke ta ku fitar da ita tana ɓata mana lokaci alhalin da sauran aiki gabanmu”Nurse Rahinatu ce da wata nurse ɗin s**a k**a ni don fitar da ni,duk da ina cikin mugun hali bai hana ni zuba masa raunatatun idona ba ina kallonsa a matsayin mugu wanda bai da tausayi.“Ku kai ta ofis ɗina ina zuwa” muka ji muryar Dr Bilal a bayanmu,hakan s**a yi kuwa.Kan gadon da yake duba marar lafiya s**a kwantar da ni,ita ɗayar ta yi tafiyarta yayin da Rahinatu ta zauna tana duba ni.Murya can ƙasan maƙoshi na ce “miƙo mini takardar da ke kan teburi” Zuwa ta yi ta ɗauko tare da miƙo mini,na karɓa na karanta jawaben ƙaryar da Dr Bilal ya rubuta waɗanda su ne yake so na gabatar.Ina riƙe da takardar ya shigo,da sauri Rahinatu ta fita yayin da shi kuma ya matso cikin masifa yana cewa “me kika yi haka? Kin sha ƙwaya ne ko me? Wato ba don na dakatar da ke ba dukkan sirrin za ki sanar?”“Me na yi? Wani sirri kuma kake faɗa Sweety?” na faɗa don ni sam ban ga aibun abin da na faɗa a ɗakin taron ba.“Dalla yi mini shiru kin wani buɗe baki sai zuba k**e yi k**ar an kunna rediyo mtsww! Tashi ki fita” ya daka mini tsawar da na ji har ƙasan raina.Idona tab da hawaye na ce “amma sweet...” cikin masifa ya katse ni “kin ga Fateema ki fita na ce,ki je gida zan neme ki daga baya”A yadda nake ganin tsantsar ɓacin rai a idonsa yasa ban ƙara minti guda ba na fito ina kuka,idona sun rufe sam ban gani hakan yasa ban ga tawowarsa ba sai ji na yi na kai ma abu karo.Na yi baya zan faɗi ya taro ni,kafin kuma na ida tsayuwa kan ƙafafuna ya yaɓo mini wata baƙar magana cikin amon sautinsa mai matuƙar firgitarwa.“Jarababbiya kawai!” sai ya yarɓa ni gefe,na yi tangal-tangal zan faɗi amma Allah ya tsare ban faɗin ba.Ta ƙasan gashin idona da ya jiƙe sharkaf da hawaye nake kallon lokacin da aka buɗe masa baƙar motarsa ya shiga.Sai da motar ta fita daga harabar asibitin kafin na ɗaga ƙafata na fito,taxi na samu ya kai ni gida sai bayan na sauka ma ne na tuna cewa na baro jakata can asibiti.Sai da na karɓo masa kuɗinsa wurin Mama wacce duk ta rikice na ganina da ta yi cikin halin baƙin ciki.Ina shiga can uwar ɗaka na shige na rufe ƙofa,na ci gaba da rera kukana wiwi tsakanin kalaman Dr Bilal da kuma na baƙonmu sai na rasa na wanne s**a fi yi mini ciwo.“Anty Fatee don Allah ki fito ki sanar da mu abin da ke damunki,kin ga muna cikin murna amma kin zo kin ɓata mana tsari” ƙanwata Maryam ta faɗa daga can bakin ƙofa tana ɗan bubugawa.Tashi na yi na buɗe,sai kuma na ƙanƙame Mama na fashe da sabon kuka tare da yi mata bayanin Dr Bilal ya yi fushi da ni.Sanin matsayinsa a zuciyata,yadda nake mugun ƙaunarsa da sonsa yasa Mama ta kira shi a waya don jin abin da ya haɗa mu amma sai da ta jera masa kira kusan biyar a ƙarshe ma sai ya dinga maido mata kiran kafin ya kashe wayarsa gaba ɗaya.Duk ina zaune komai ya faru,abin da ya yi sai ya haifar mini da mugun zazzaɓi.Magani ma ƙin sha na yi,don na gwammaci na mutu kan na rasa Dr Bilal.Towel Mama ke jiƙawa da ruwan sanyi tana ɗora mini a goshi,yayin da kuma ƙanwata Maryam ke yi mini sannu.Ban san lokacin da bacci ya ɗauke ni ba,ko da na farka jakata na gani ina shirin tambaya sai ga na tsinkayi Rahinatu kan sallaya.Na ja ajiyar zuciya,ta juyo muna haɗa ido sai ta kawar da kai.Sai na ji jikina ya ƙara yin sanyi,miƙewa na yi ni ma don yin sallah sai dai ina shiga toilet na samu baƙon watana ya zo .Wanka kawai na yi na saka kaya maras nauyi na kimtsa sai na fito,kusa da Rahinatu na zauna ba tare da na ce komai ba.“An bai wa Dr Bilal hutun wani lokaci,yana cikin fushi sosai duk ya farfasa abubuwa da dama.A shawarce ki ɗan basa lokaci har ya sauko” Rahinatu ta faɗa cike da rauni . Idona s**a kawo ruwa na ce “ke ma laifina ki ke gani?”Ta ce “eh to kusan haka ne,ke ma me yasa za ki faɗi abubuwan nan alhalin kin san faɗi tashin da ake yi na ƙaryata cewa akwai BAƘIN RUHI (MRS SADAUKI) a kaf asibitocin garin nan mai shayen jini?”Murya a raunace na ce “amma ai abin da na gani ne na faɗa ”“A'a ki ka dai ƙirƙiro,saboda a some aka kawo mana ke kowa ya san yadda k**e da tsoron mutuwa da kuma gawa.Abin da ki ka faɗa kuma sam bai taɓa faruwa ba a cikin asibitinmu ba”Na ɗaga kai na dube ta da kyau kafin na ce “ina so ki yarda da ni,wallahi duk abubuwan da na faɗa gaskiya ne”“Kenan ke mayya cewa?”k**ar subutar baki hakan Rahinatu ta faɗa ,sosai kuma kalmar mayya ta bugi zuciyata sai na ji k**ar na shaƙe ta.Amma na yi shiru na ci gaba da juya na mujiyata ina kallonta da su,cikin tsarguwa da kallon da nake yi mata ta ci gaba da cewa “to in dai ba haka ba ta ya aka yi kika san da duk abubuwan nan da s**a faru da Alhaji Lawan? Kuma in ba ki manta ba kwanan baya an yi mana darasin ceton kai inda aka faɗa mana siffofin Mayu da kuma yadda za mu gane mutum mugu ne,ke kuma ba ki da ko ɗaya ko kuwa kin taɓa jin sha'awar cin naman mutum?”“Da a ce ni mayya ce da wallahi babu abin da zai hana na damƙe kurwar Dr Bilal ” na faɗa ina cije leɓe.Rahinatu ta yi murmushi ta ce “yanzu dai zan wuce gida sai mun yi waya”Sai da na yi mata rakiya har bakin ƙofar gida inda motarta take sannan na dawo ciki.Jakata na buɗe na ciro wayata,nan na ci karo da saƙon Dr Bilal wai rabu da ni na je na nemi maye irina.Saƙon na dinga maimataiwa ina karanta shi k**ar mai lesson kafin na tambayi kaina “kenan yana nufin ni mayya ce?” sai kuma ga hawaye shaaaa...

MRS SADAUKI:

For More Information 08169130080 ✍️

TALLA TALLA TALLADukan kofar ake da karfin tsiya,yayin da kowannensu ke kokarin tokare kofar da karfin jikinsa, kowace b...
20/05/2026

TALLA TALLA TALLA

Dukan kofar ake da karfin tsiya,yayin da kowannensu ke kokarin tokare kofar da karfin jikinsa, kowace bugawa tana ratsa jikinsu k**ar tsawa, har sai da kura ta rika fadowa daga silin din dakin.
kafafunsu na karkarwa a kasa, Amma abin mamaki, duk da wannan yanayi na firgici da suke a ciki, ihu kawai suke yi na neman tsira babu daya daga cikinsu da ya tuna ya ambaci sunan Mahalicci.
Duhu ya mamaye dakin, sai kawai karan numfashinsu da sautin katakon kofar da ke shirin tsagewa,Ba zato ba tsammani sai aka daina dukan kofar.
Shuru ya gauraye dakin shurun da ya fi dukan kofar ban tsoro, Sun tsaya cak suna kallon kofar yayin da gumi ya jika sassan jikinsu,Can kuma sai s**a ji wani nishi mai nauyi daga bayan kofar wanda yasa hanjin cikinsu kaɗawa.
​Kwatsam! Sai s**a jiyo wani irin kara k**ar ana yakusan kofar da farce,Katakon kofar ya fara tsastsagewa tsamkar bulon da ruwa taiwa karanci, A daidai wannan lokacin ne wutar dakin ya fara daukewa yana dawowa (flickering), yana nuna musu inuwar wani katon abu da ke kokarin bankado kofar, tsoro da fargaba ne ya hana su ko da kalma daya ta ambaton Allah, sai ihu mara sauti da ke fita daga makogwaronsu.
​Daidai lokacin da katakon kofar ya fara rarrabewa, sai daya daga cikinsu mai suna [Fahad] ya farga, Duk da karkarwar da jikinsa yake yi, haka ya nufi wasu kayan tsafi da ke jere a tsakiyar dakin, wanda yake kyautata zaton sune s**a haddasa faruwan wannan abu, Ya kwashe su da kafa sannan ya kifar da wata kwarya a kasa mai dauke da bakin garin magani, sannan ya tattake kasusuwan dake wannan guri da kuma kyandir da aka shirya a gun.
​Nan take, sai dukan kofar ya tsaya cak! Gurin yayi shiru mai ban tsoro,Wutar da take ta daukewa ta tsaya cif, ta haske dakin radau, Sun rage su kadai a dakin, kowannensu na kallon kofar da ta rabe, zuciyansu na bugun uku uku.
Duk da cewa hatsarin ya kau, amma kowannensu ya san cewa shuru ya dawo ne kawai saboda an bata tsarin bakin Tsafin, amma abin da ke wajen har yanzu yana nan a kusa.

​Shurun bai dade ba, sai wani sanyi mai ratsa jiki ya ratsa dakin. Ba zato ba tsammani, sai tagar dakin ta hantsace da karfin gaske—BAM!—ta bugu da bango ta dawo ta rufe. Kafin su numfasa, sauran kofofin kabad da ke dakin s**a fara budewa da kansu suna rufewa cikin wani irin zafin rai da sauri.

LITTAFIN RUMBUN SHEƊAN ZAI FARA ZUWAN MUKU ASHIRIN DA BIYAR GA WATAN JULI DAGA MATASHIN MARUBUCI ABDUL ALHAJI MUSA

20/05/2026

YAR GARUWALittafin Hauwa U M Smasher,Hauwa Muh'd Usman Real Smasher +2348125527472 *Y'AR GARUWA...........
25/03/2026

YAR GARUWA
Littafin Hauwa U M Smasher,Hauwa Muh'd Usman Real Smasher +2348125527472

 *Y'AR GARUWA........*
_{ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ ơʄ ąmąʑıŋɠ wąɬɛr ۷ɛŋɖơr women}._

*STORY,WRITTEN & EDITING*
*BY*
_HAWWA M.U {®ɛąl $mąʂɧɛr}._

*COPIED BY.*
_HAWWA M.U (REAL $MASHER)._

 💠💠💠💠💠

*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*

🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹

*©®2018*

*8/mąrcɧ,2018*

*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_

🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹

_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._

*Da ѕυnayen υвangιjιnмυ tsarkaka naĸe ғara rυвυтa wnn laвarι, wanda ѕнι ya вanι daмa,laғιya,тare da вaιwar da a ĸυllυм nake godiya gareshi....*

*Aminci,tsira su k'ara tabbata ga fiyayyen halitta,Annabi Muhammad (S.A.W) tare da ahalinsa da sahabbansa da wad'anda s**a biyosu da kyautatawa har i zuwa ranar sak**ako....*

*~___________________________~*

*wannan laвarι ĸ'ιĸ'ιrarѕa nayι,ѕaι daι yana d'auke da darussan rayuwa iri²,ina fata Allah ya bani ikon kammalawa lafiya....*

*ban yarda a juyamin labariba ta kowace fuska,wanda yayi haka na barshi da Allah...*

*Idan kunga kuskure aciki ina fata za kumin uzuri,Allah ya yafe mana baki d'aya, wanda yaga wani abu da yayi dai² da rayuwarsa yamin uzuri badon cin fuska nayi ba....*

*Allah yasa mu dace.... Ameen thumma ameen...*

*~___________________________~*

_YA ALLAH INA ROK'ONKA DA SUNAYENKA TSARKAKA KA BAWA MAHAIFANMU LAFIYA,INGANTACCIYA MAI 'DOREWA,KAJI K'ANSU,KAYI MUSU RAHAMA......._

_WANNAN LITTAFI NA SADAUKAR DASHI GA MAHAIFANMU,NA GIDA DANA ASUBITI......._

*_•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°_*

*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_

*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._
*AND*
_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._

*0⃣1⃣*

*S*allama take tayi tun daga k'ofar gidan,amma ko tari ba ayiba,ga rana dake dukan kanta...

Banda maik'o babu abunda take,jin ank'i ansawa,yasa ta d'aga allonta dake hannunta ta d'ora akanta,don kare ranar da ta addabeta...

Zuwa can ta sake maimaita yin sallamar,nanma dai shiru aka mata babu amsa....

Hakan ne yasata tsugunawa,ta cire silifanta ta zauna akai k**ar mai d'aukan darasi.....

Tun daga nesa dattijon dake tahowa,yake kallonta,sauri ya K'arawa k'afarsa dan tabbatar da zatonsa....

Daf da ita ya k'araso,tare da fad'in *"NANA KHADIJATU*, Uwata me k**eyi a cikin wannan ranar da kowa yake gudunta???"

'Dagowa tayi da saurinta jin muryan mahaifinta dake tsaye,da murnarta ta kalli mahaifin nata tana fad'in "Abba na dawo ina sallama,ba a amsaba shi yasa na zauna anan ban saniba ko ba kowa a gida"....

Banda abunki kuma uwata sai kizo cikin wannan ranar ki zauna k**ar an miki dole...

"Tashi maza mu shiga ciki,kar kuma ki sake zuwa ki zauna kinji ko,wannan ai sai wani ciwon ya k**aki"...
Fad'in abban *KHADIJATUL KHUBRA*.....

Hannunta ya k**a s**a k**a hanyar shiga gidan....

Tun daga bakin k'ofar gidan yayi sallama,jin shiru ba a amsaba,yasa abban yaci gaba da kutsa kai cikin gidan had'e da sake yin wata sallamar....

Abunda ya matuk'ar bawa abba mamaki bai wuce ganin da mutum a tsakar gidanba.....

K'arasawa yayi yana k'are mata kallo,kafin ya iya furta ‘’ladiyo dama kina zaune muke sallama,amma amsawa ta gagareki‘’.....

Fuska ta yatsina (tamkar kayan miyan da yaso lalacewa).....

kafin ta bashi amsa da cewa ‘’ina ji sai me??
ko kuwa cewa akayi an ajiyeni ne dan na amsa muku sallama?''......

Ganin zata kunyata shi gaban y'arsa yasa yabar maganar ta hanyar fad'in ''Allah ya kyauta''......

Bud'ar bakin ladiyo sai cewa tayi ''ya kyauta abinda yafi haka''.....

Bai kuma tanka mataba,ya juya yana girgiza kai,ya shige d'akinsa.....

Duk wannan budurin da ake a gaban KUBRA ake,kanta na k'asa sai hawaye dake tsiyayowa daga ciki......

Ganin abbanta ya bar gurin itama ta juya da niyyar barin gurin....

Sai dai muryar ladiyo ta rigata k'arasawa bakin k'ofar d'akin,ta hanyar mako mata mula²n zagi......

Da sauri ta k'arasa shigewa,gabanta na dukan 9²....

Can ku'ryar D'akin ta nemi guri ta zauna,tana jiran gawon shanu....

Cikin d'akin da baida wadataccen haske,take zaune,tayi shiru sai kalle² take tamkar wata bak'uwa,ko wacce ta fara rayuwa inda bata saniba,haka taketa fama ita kad'ai,a haka bacci yayi awon gaba da ita.......

Wani k'ayataccen guri ta hango mai kyan gaske....

Sauri take ta k'arasa gurin,amma duk da haka ta kasa k'arasawa gurin,saima gajiya da tayi......
Haka ne yasata neman guri ta zauna,tana k'arewa gurin kallo ko zata hango inda ruwa yake.....

Rashin ganin alamar ruwa yasata,juyawa ta kalli hanyar da ta biyo.....
hanyace mik'ak'kiya wacce ko farkonta bata ganiba,bare k'arshenta,hakan yasata kifa kanta ta fara rera kukan rashin Madafa....

Tun daga nesa ta fara jiyo hayaniyar mutane had'e da wani daddad'an k'amshi da yasata saurin d'ago kai,tana bin hanyar da hancinta.....

Ayarine na mutane da suke da mayuk'ar yawa suke shirin giftawa ta kusa da ita......

Da sauri ta mik'e tabisu duk da suna kan abun hawa,hakan bai hanata shiga gabansuba,tana fad'in
"Dan Allah ku taimakamin"....

Babu wanda ya saurareta,sai zagayeta da s**ayi s**a ci gaba da tafiya......

Da gudu² ta sake shiga gabansu,tana rok'onsu.....
Wannan karon kam saboda haushi da ta bawa wasu daga cikinsu yasa su yi mata tsawa....

A firgice,jikinta har rawa yake saboda tsoro take kallonsu,wani k'ato da yayiwo kanta d'auke da bulala yasata fara kuka....

tana bashi hak'uri,d'aga bulalar ya d'aga da niyyar sauke mata a jikinta......

Kafin ya k'arasa ida nufinsa,wata siririyar murya daga bayansa take fad'in kada ka kuskura ka aikata abunda kake k'ok'arin yi .....

Da hanzarinsa ya juya don ganin mai magana,sai dai ganin fuskar wanda yayi maganar yasa shi kaucewa daga kusa da ita,jikinsa na kad'awa tamkar Mazari.......

Kyakykyawan matashi ne ya bayyana daga inda ya kauce,yana sanye cikin fararen tufafi,tafiyarsa cike da k'asaita,har ya k'araso Inda suke.....

Kallon k'aton yayi kafin ya bud'e baki,har ya rigashi cikin ladabi da girmamawa yake fad'in ''tuba nake ranka ya dad'e''......

Hannu ya d'aga masa,ba tare da ya sake yunk'urin yin maganaba,ya juya da nufin barin gurin............

*~_KEEP MOVING 😍😍😍……………_~*

*_REAL SMASHER 🤞🏻😘.._*
💠💠💠💠💠

*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*

🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹

*©®2018*

*9/mąrcɧ,2018*

*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_

🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹

_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._

*__________________________*

_Godiya gareki *FATEEY TAMBARIY* tabbas y'an *TIME WRITER'S* muna godiya marar adadi gareki,Allah ya kara baseera,hazaka da kuma daukaka..._
_Ki jima kiyi karko tawan,Allah ya bar zumunci da kauna..._

*__________________________*

*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_

*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._

*AND*

_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._

*0⃣2⃣*

*C*ikin sauri tabi bayansa,tana k`ok`arin tsayar da shi,sai dai hak`anta bai cimma ruwaba…....

Duk da bawai sauri yakeba,haka take binsa tana fad`in *"BAWAN ALLAH* ka tsaya"......
Ganin ta kasa cimmasa,kuma baiyi kokarin tsayawaba,yasa taci gaba da binsa....
Sai dai k**ar wanda yake tafiya a cikin iska,haka ta kasa riskarsa,tsayawa tayi,lokacin ne ta hangoshi har ya...
Domin cigaba da karantawa sai ku danna shudin rubutun da ke nan kasa. ko a duba comment a'a samu link na downloading acan...

https://thnovels.com.ng/novel/yar-garuwa

**Kashi Na 13: Gidan Macijiya da Sabon Kisan da ke Cikin Makarantar** # # # **Sashe na Farko: Komawa Cikin Daji da Baraz...
23/12/2025

**Kashi Na 13: Gidan Macijiya da Sabon Kisan da ke Cikin Makarantar**

# # # **Sashe na Farko: Komawa Cikin Daji da Barazanar Ruwan Barci**

Salim da Safiya sun fito daga Kogin Benue. Hasken rana yana haskaka fuskokinsu, amma ba su ji dumin rana ba. Sun ji sanyin ruwa a jikinsu. Safiya ta kalli Salim. Ba ta ga tsoro a idanunsa ba. Ta ga karfi da soyayya.

"Salim, mun dawo inda aka yi mana hari," Safiya ta ce, muryarta a hankali. "Amma yanzu mun san cewa ba mu kadai ba ne. Babban Maciji ya ba mu kariya. Amma ina jin tsoro. Ina jin tsoron abin da ke cikin kaina, wanda Babban Maciji ya ce dole in gano."

Salim ya rike hannunta. Ya kalli zoben da ke hannunsa. Zoben yana haskawa da kalar shuɗi mai zurfi. "Ba za mu tafi makarantar a yanzu ba," Salim ya ce. "Dole ne mu san wanene wannan Sabon Kisa. Kuma dole ne mu san me k**e boyewa, Safiya."

Safiya ta girgiza kai. "Babban Maciji ya ce dole mu koma. Ya ce yaki yana faruwa a can. Kuma Zainab za ta zo da sabon makami. Idan muka gudu, za mu zama marasa karfi."

S**a yi tafiya na tsawon mintuna. Sun dawo makarantar, amma ba su dawo k**ar yadda s**a tafi ba. Yanzu sun san cewa makarantar ba gida ba ce, wani filin yaki ne.

A cikin dakin Zainab, tana zaune tana murmushi. Ruwan barci mai kisa yana kan teburinta. Tana shirin kai hari. Amma tana buƙatar wani abu. Tana buƙatar wani ya taimaka mata.

"Wannan ruwan ba zai kashe Safiya nan take ba," mahaifinta ya ce mata a waya. "Za ta fada cikin barci ne mai zurfi. Kuma a lokacin ne za mu iya cire abin da ke cikin kanta. Kuma dole ne ki yi hankali. Sabon Kisa zai shigo cikin makarantar nan da 'yan sa'o'i kadan. Kada ki shiga tsakaninsa da Safiya."

Zainab ta ce: "Mahaifi, me zai yi? Ba na son raba kisa da wani."

"Sabon Kisa yana da hanyoyi na daban," mahaifinta ya ce. "Shi ne babban mai farauta. Zai yi amfani da hankali. Kuma zai sa Safiya ta yarda da shi. Amma dole ne mu yi aiki tare."

# # # **Sashe na Biyu: Ganawar Farkon Zainab da Salim**

Salim da Safiya sun shiga cikin harabar makarantar. Dalibai suna ganinsu, amma ba su san abin da ya faru ba. Suna ganin Safiya tana da kyau, amma ba su san cewa tana da karfi ba.

Suna tafiya ne, sai Safiya ta ji wani irin ciwo a kanta. Ciwon ba ciwo ne na jiki ba, ciwo ne na tunani. Ta ji muryar Babban Maciji a cikin zuciyarta.

*"Kada ki yarda da mutane,"* muryar ta ce. *"Kada ki yarda da kowa. Kuma ki kalli mutanen da ke kusa da ke. Akwai wani wanda zai zo ya raba ki da Salim."*

Safiya ta kalli Salim. Salim yana kokarin rike hannunta. Amma Safiya ta ji wata karfi tana janyota daga Salim. Ta ji tsoro.

Zainab ta fito daga dakinta. Tana murmushi. Ta nufo Salim da Safiya. Ta yi k**ar tana son suyi sulhu.

"Salim, Safiya," Zainab ta ce. "Na yi nadama. Na yi kokarin cutar da ku. Amma yanzu na gane cewa ba haka ba ne."

Salim ya kalli fuskarta. Zoben da ke hannunsa ya fara zafi. Zoben ya nuna masa cewa Zainab tana yin karya.

"Meye k**e so, Zainab?" Salim ya tambaya. "Idan har da gaske k**e so mu yi sulhu, to, ki fadi gaskiya. Ki fadi gaskiya game da abin da k**e shirin yi."

Zainab ta kalli Safiya. "Safiya, ina so in ba ki wani abu. Wata kyauta ce. Na san cewa ki tana son shan ruwan lemo. Na sayo miki."

Zainab ta fitar da wata kwalba mai ruwan lemo. Kwalbar ta yi k**ar ruwan lemo ne na al'ada. Amma a ciki, akwai ruwan barci mai kisa.

Salim ya yi kokarin tsayar da ita. Amma Zainab ta kasance mai sauri. Ta mika wa Safiya kwalbar. Safiya ta karba, amma ta ji wani irin sanyi a hannunta.

# # # **Sashe na Uku: Fitowar Sabon Kisa**

Kafin Safiya ta bude kwalbar, sai wani sabon mutum ya shigo makarantar. Mutumin ya kasance dogo, yana da gashi mai kyau, kuma yana sanye da kayan makaranta. Ya kasance k**ar dalibi. Amma a idanunsa, akwai wani irin haske mai duhu.

Ya nufo Safiya da Zainab. Ya yi k**ar yana son Safiya. "Sannu, Safiya," Sabon Kisa ya ce, muryarsa mai dadi. "Ni ne Sabon Kisa. Amma ba wanda zai kashe ki ba ne."

Zainab ta kalli Sabon Kisa da mamaki. Ta san cewa shi ne wanda mahaifinta ya aika. Amma ba ta san cewa zai shigo cikin makarantar a matsayin dalibi ba.

Safiya ta kalli Sabon Kisa. Ta ji wani irin dumi a jikinta. Tana jin cewa za ta iya amincewa da shi.

Salim ya rike hannun Safiya. "Waye kai? Me kake so?" Salim ya ce, muryarsa tana girgiza.

Sabon Kisa ya kalli Salim. Ya yi murmushi. "Salim, na san cewa kana son Safiya. Amma ba za ka iya kare ta ba. Ni ne zan iya kare ta. Ni ne zan iya ba ta abin da take bukata."

Sabon Kisa ya juya zuwa Safiya. "Na san cewa kana da karfin macijiya. Amma kana da karfin mutum. Dole ne ki zabi hanya daya. Idan kika zabi zama mutum, to ki zo tare da ni. Ni ne zan iya ba ki duk abin da k**e bukata."

Safiya ta kalli Salim. Tana jin cewa Sabon Kisa yana fadi gaskiya. Ta kalli Zainab. Zainab tana tsaye a gefe, tana murmushi. Tana jiran Safiya ta sha ruwan lemo.

Salim ya rike hannun Safiya da karfi. Ya tuna da abin da Babban Maciji ya fada masa: *"Akwi wani abu da kake boyewa, Salim."* Salim ya san cewa Babban Maciji yana nufin cewa Safiya tana da sirri a jikinta. Kuma Sabon Kisa ya san sirrin.

"Safiya, kada ki yarda da shi," Salim ya ce. "Kada ki yarda da Sabon Kisa. Shi ne zai kashe ki. Ba Zainab kadai ba ce mai son cutar da ke."

Sabon Kisa ya kalli Salim. Ya numfasa. Ya fito da wani abu daga aljihunsa. Wani dan karamin kwalba ne mai cike da ruwan guba. Ruwan guba yana haskawa da kalar shuɗi.

"Idan har kana son Safiya, to, dole ne ka bar ta," Sabon Kisa ya ce. "Idan ba haka ba, zan kashe ki da wannan gubar. Ba wai guba ce da za ta kashe ki nan take ba. Wani abu ne da zai canza ki har abada."

# # # **Sashe na Hudu: Tunanin Safiya da Sirrin Babban Maciji**

Safiya tana tsaye a tsakiyar su. Tana jin cewa duniyarta tana girgiza. Tana jin cewa dole ne ta yanke shawara. Za ta iya zama mutum, ko kuma ta zama macijiya.

Zainab tana jiran Safiya ta sha ruwan lemo. Sabon Kisa yana jiran Safiya ta bi shi. Salim yana jiran Safiya ta gudu.

"Na san cewa kuna so ku kashe ni," Safiya ta ce. "Amma ba za ku kashe ni ba. Ni ne zan kashe ku. Ni ce sarkin macizai."

Safiya ta jefa kwalbar ruwan lemo a kasa. Ruwan lemo ya zube a kasa. Ya zama ruwan guba. Ruwan ya fara cinye duwatsu a kasa.

Sabon Kisa ya yi mamaki. Ya kalli Safiya da mamaki. Ya san cewa Safiya tana da karfi. Amma bai san cewa tana da karfi haka ba.

"Safiya, kin zabi zama macijiya," Sabon Kisa ya ce. "Yanzu zan fara yaki da ke. Kuma zan nuna miki cewa ni ne Sabon Kisa. Ni ne ke da gaskiya."

Sabon Kisa ya shiga cikin Safiya. Ba ya shiga cikin jikinta. Yana shiga cikin zuciyarta. Yana shiga cikin tunaninta. Yana shiga cikin sirrin da take boyewa.

Safiya ta fada kasa. Salim ya k**a ta. Safiya tana rike da hannunsa. Tana numfashi da sauri. Tana ganin abubuwan da ba su faru ba. Tana ganin Kogin Benue. Tana ganin Babban Maciji.

Babban Maciji ya fito daga ruwan. Ya kalli Safiya. Ya ce: *"Kada ki yarda da Sabon Kisa. Shi ne wanda ya kashe mahaifiyarki. Kuma yana so ya kashe ki. Amma dole ne ki gano asalin ki."*

Safiya ta tashi tsaye. Tana cike da fushi. Tana cike da karfi. Tana cike da sirri. Ta kalli Sabon Kisa. Ta ce: "Kai ne Sabon Kisa. Amma ba za ka kashe ni ba. Ni ne zan kashe ka."

**--- KARSHE KASHI NA 13 ---**

**Mai zai faru a Kashi na 14?**

* **Yaƙin Sarauta:** Sabon Kisa da Safiya za su yi yaƙi a makarantar. Wanene zai ci nasara? Shin Safiya za ta gano asalin gaskiyarta a cikin wannan faɗan?
* **Wanda Salim ya Boye:** Shin Salim zai fadi gaskiya game da abin da Babban Maciji ya ce masa? Shin zai iya kare Safiya daga Zainab da Sabon Kisa?
* **Sirrin Kogin Benue:** Me Babban Maciji yake son Salim ya kawo masa? Shin zai iya samo mahaifiyar Safiya?

**Labari yana kara zafi. Kada ku sake a baku labari!** DOMIN CIGABA LABARIN KUYI COMMENTS DA NEXT AND LIKE AND SHARE 🙏

THE SNAKE GIRLS SCHOOL **Babi Na 12: Rukunan Kogin Benue da Barazanar Zainab** # # # **Sashe na Farko: Tafiya Cikin Ruwa...
22/12/2025

THE SNAKE GIRLS SCHOOL
**Babi Na 12: Rukunan Kogin Benue da Barazanar Zainab**

# # # **Sashe na Farko: Tafiya Cikin Ruwa da Sirrin Kogo**

Salim da Safiya sun tsaya a bakin Kogin Benue. Ruwan ya zama duhu sosai, wanda ya nuna cewa ba ruwa na al'ada ba ne. Muryar da s**a ji tana sake maimaita kiran su.

"Salim, kada ka tsorata," Safiya ta ce, tana rike da hannunsa. "Idan na zama abin da na zama a baya, dole ne in koma ruwa. Wannan shine asalinmu."

Salim ya numfasa. Ya kalli gefen kogin, inda maharban s**a gudu. Ya tuna da abin da Safiya ta yi, da kuma yadda ta kusan kashe shi.

"Safiya, na yarda da ke," Salim ya ce. "Amma ina jin tsoro. Idan Babban Maciji ya fito, za mu iya tsira kuwa?"

Safiya ta girgiza kai. "Kaka ta ce, Babban Maciji ba abokin gaba bane. Shi ne ke kare gidanmu. Kuma idan har ina so in san wanene ni, dole ne in fuskance shi."

Salim ya kalli fuskarta. Fuskarta tana canzawa, tana zama k**ar kifin teku. Hasken wata ya haskaka idanunta, idanunta s**a zama kalar zinare.

"Tafi, Salim, shiga cikin ruwan," Safiya ta ce.

Salim ya shiga cikin ruwan. Ruwan ya shiga jikinsa, amma ba ya jin sanyi. Ya ji wani irin dumi mai dadi. Yana jin k**ar ruwan ya karbe shi.

Safiya ta shiga ruwan a bayan sa. Nan take, jikinta ya canza. Wutsiyarta ta zama mai kalar shuɗi, k**ar ruwan teku. Ta k**a Salim, s**a fara nutsewa cikin ruwan.

Kamar yadda s**a nutse, s**a ga hasken wuta yana fitowa daga zurfin ruwan. Ba wuta bace ta al'ada, haske ne mai kalar shuɗi da kore. Ruwan ya zama k**ar wata hanya mai tsayi, wacce take kai su wata duniyar daban.

S**a nutse na tsawon mintuna. Salim ya bude idanunsa, sai ya ga wata duniyar daban. Ba daji ba ne a nan, wani gari ne a karkashin ruwa. Gine-gine ne masu tsayi, wadanda aka gina da duwatsu masu haske. A tsakiyar garin, akwai wani haske mai girma, wanda yake fitowa daga wani babban kogo.

"Mun zo," Safiya ta yi magana, muryarta a can karkashin ruwa tana girgiza. "Mun zo wurin Babban Maciji."

# # # **Sashe na Biyu: Ganawa da Babban Maciji**

Salim da Safiya sun fito daga ruwan, s**a fito a bakin wani kogo. Kogon ba duhu ba ne. Hasken wuta ne ke haskaka shi. A ciki, akwai wani gungun macizai masu girman gaske, wadanda ke zaune a gefen kogon.

A tsakiyar kogon, akwai wani maciji mai girman da ba zai iya shiga cikin makaranta ba. Ya fi kogi girma. Idanunsa suna kalar zinare, fatarsa tana kalar shuɗi. Macijin ya kalli Safiya da Salim.

"Safiya, yar sarkin macizai," Muryar Babban Maciji ta fito daga bakinsa. Muryar tana da nauyi, tana girgiza duwatsu. "Kin dawo gida."

Safiya ta durkusa a gabansa. "Na dawo ne domin in nemi mafita. Su mutane suna so su kashe ni. Kuma ina tsoron zama macijiya har abada."

Babban Maciji ya kalli Salim. "Yaro, me kake yi a nan? Me yasa kake tare da macijiya? Ba ka san cewa mutane da macizai ba za su taba zama tare ba?"

Salim ya tashi tsaye. Bai ji tsoro ba. "Ni Salim ne. Ina son Safiya. Ba ruwanka da asalinmu. Ina nan ne don in taimaka mata."

Babban Maciji ya kalli Salim. Ya numfasa, sai wani iska mai zafi ya fito daga bakinsa. Iskar ta cika kogon. Salim ya ji cewa yana kokarin cire masa rai ne. Amma sai ya gani cewa ba haka ba ne. Babban Maciji yana gwada karfin soyayyarsa.

"Mutum mai karfi ne," Babban Maciji ya ce. "Amma soyayya ba za ta iya kare ki daga mutane ba. Zainab tana shirin kashe ki. Kuma ba Zainab kadai ba ce. Mahaifinta yana da karfi fiye da yadda k**e tunani."

Babban Maciji ya fara magana game da tarihin dangin Safiya. Ya ce: "Kaka ki ta boye ki ne domin ta kare ki daga wani. Amma yanzu lokaci ya kure. Dole ne ki fuskanci kaddararki."

Ya nuna wa Safiya wani abu a cikin ruwan. "Iyaye ki ba su mutu ba. Suna nan a tsakiyar kogin. Amma dole ne ki zabi hanyar da za ki bi. Za ki iya zama mutum, ko kuma ki zama macijiya."

Safiya ta kalli Salim. Ta ce: "Ina son zama mutum. Amma idan na zabi zama mutum, shin zan iya kare Salim daga Zainab?"

Babban Maciji ya girgiza kai. "Ba za ki iya kare shi ba. Amma Salim ya zaɓi hanyar da zai bi. Zai iya zama abokin gaba ko kuma abokin tafiya. Sai dai... akwai wani abu da kake boyewa, Salim."

Salim ya yi mamaki. Ya ce: "Me nake boyewa?"

Babban Maciji ya ce: "Kibiyar guba da s**a harba Safiya, an samo ta daga gubar da aka yi amfani da ita a yakin da aka yi shekaru da s**a wuce. Amma ba Zainab bace ta samo ta. Wani ne ya bata."

# # # **Sashe na Uku: Shirin Kashe Safiya a Makarantar Sakandare**

A makarantar sakandare, Zainab tana zaune a dakinta. Tana fushi. Wayarta ta yi kara. Mahaifinta ne ke kiranta.

"Zainab, me ya faru? Me yasa ba ku k**a Safiya ba?" Muryar mahaifinta ta fito.

Zainab ta ce: "Mahaifi, mun yi kokari. Amma macijiyar ta canza. Ta zama wata dabba mai girma. Kuma Salim ya kare ta."

Mahaifinta ya numfasa. "Yanzu, ki bar wa Salim da Safiya. Za mu dawo da su makarantar. Amma ba za mu yi yaki da su a daji ba. Za mu yi yaki da su a inda ba su da karfi."

"A ina?" Zainab ta tambaya.

"A makaranta," mahaifinta ya ce. "Kada ki damu. Ina da wani abu da zan ba ki. Wani sabon makami. Wani abu da zai iya kashe macijiya ko da tana mutum."

Mahaifinta ya shiga dakin. Ya kawo mata wani abu. Wannan abu ya yi k**a da wani dan karamin kwalba. Ciki, akwai wani ruwa mai duhu, kalar jini.

"Wannan shi ne 'Ruwan Barci Mai Kisa,'" mahaifinta ya ce. "Wannan ruwan ba guba bane kawai. Ruwan ne da aka samo daga gubar macizai. Idan kika sa wannan ruwan a jikinta, za ta zama k**ar mutum, amma gubar za ta kashe ta a hankali."

Zainab ta kalli mahaifinta. "Me yasa za ta dawo makarantar?"

"Domin tana da wani abu da nake so," mahaifinta ya ce. "Wani abu da ke cikin kanta. Kaka ta boye shi. Kuma dole ne mu same shi."

Mahaifinta ya kara da cewa: "Kuma ki yi hankali. Akwai wani wanda zai zo ya shiga cikin makarantar. Shi ne 'Sabon Kisa.' Wani ne wanda ya san yadda za a kashe macizai. Kuma idan har Safiya ta fito daga kogin, shi ne zai fuskance ta."

Zainab ta yi mamaki. "Wani kuma?"

"Na'am," mahaifinta ya ce. "Wannan Sabon Kisa zai yi amfani da hanyoyin da ba mu sani ba. Zai sa Safiya ta yarda da shi. Kuma zai kashe ta daga ciki."

Zainab ta kalli kwalbar. "Yanzu zan koma makaranta. Zan nuna wa Safiya cewa ba ni kadai ba ce mai karfi."

# # # **Sashe na Hudu: Sabuwar Tafiya da Sabon Alkawari**

A cikin kogon Babban Maciji, Safiya da Salim sun fito. Babban Maciji ya basu wani abu. Wani zobe ne mai haske.

"Wannan zobe, Salim, zai kare ka daga guba," Babban Maciji ya ce. "Kuma zai kare ka daga sihiri. Amma Safiya, dole ne ki yi amfani da karfin ki. Idan kika koma makaranta, dole ne ki fuskanci Zainab da Sabon Kisa."

Safiya ta karbi zoben. Ta sa shi a hannunta. Tana jin karfi a jikinta.

"Babban Maciji, me ya sa kake taimaka mana?" Safiya ta tambaya.

Babban Maciji ya ce: "Na taimaka muku ne domin in kare dangina. Kuma Salim, ina son ka. Ka nuna min cewa mutane za su iya zama abokan macizai. Amma akwai wani abu da nake so ka yi."

Salim ya ce: "Meye shi?"

"Ka kawo min mahaifiyar Safiya," Babban Maciji ya ce. "Tana cikin daji, tana jirana. Kuma dole ne mu dawo da ita domin mu hada karfinmu."

Salim da Safiya sun fito daga kogin. Ruwan kogin ya dawo k**ar yadda yake. Sun yi tafiya cikin daji. Suna jin cewa an canza su.

"Salim, yanzu mun zama mutum da maciji," Safiya ta ce. "Ba mu da inda za mu zauna. Amma mun san cewa za mu iya yin yaki tare."

Salim ya ce: "Mun dawo makarantar. Amma ba mu dawo k**ar yadda muka tafi ba. Yanzu mun san cewa akwai wani yaki da ke faruwa. Kuma ba mu kadai ba ne."

Suna magana ne, sai s**a ji wata murya a karkashin kogi. Muryar tana cewa: *"Ku dawo wurina, ku biyo ni. Ku zo wurin Babban Maciji. Za a gane wanene ke da gaskiya."*

Safiya ta kalli Salim. "Ina jin tsoro, Salim. Amma na san cewa za mu fita daga cikin wannan. Amma kafin mu fita, ki gaya min abin da k**e boyewa. Me yasa suke neman ki har cikin daji?"

**--- KARSHE KASHI NA 12 ---**

**Mai zai faru a Kashi na 13?**
**Yakin Benue da Sirrin Babban Maciji:** Shin Safiya da Salim za su iya samun Babban Maciji a cikin kogin?
**Bincike a Makarantar:** Zainab za ta koma makaranta, kuma za ta fuskanci Salim. Shin Salim zai fadi gaskiya?
**Fitowar Sabon Kisa:** Wani sabon makami zai bayyana. Wani ne zai shiga yaki tsakanin Salim da Safiya?

**Labari yana kara zafi. Kada ku sake a baku labari!**
**© KM GALLERY FASHION**

Address

Kano
246

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Abdull Hausa Novels-A² posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Abdull Hausa Novels-A²:

Share