25/05/2022
✍️ MAWAKI NAZIFI ASNANIC YA SAMU NASARAR ZAMA MAWAKIN KANNYWOOD NAFARQ DA YAKE DA WIKIPEDIA PROFILE.
✍️ Nazifi Asnanic fitaccen mawaki ne na soyayya da nishadi a kasar Nigeria musanman akan abinda ya shafi masana'antar shirya fina-finan Hausa (KANNYWOOD). Hakika kannywood bazata manta da irin gudumuwar da mawaki Nazifi Asnanic ya bayar a kannywood ba.
✍️ Mawakin yara wakane a wajajen shekara ta 2000 Tauraruwar mawakin ta fara haskewa sosai a wajajen 2002 lokacin da yayi waka mai taken “soyayya in zaka so dan uwanka " ta film din FKD PRODUCTION mai suna Fil,azal .
✍️ Daga nan ne yaci gaba da wakokin da su kayi tashe irinsu “TARALIYA" da “DAUSAYI" da “ZOMU ZAUNA" da sauransu.
✍️ Nazifi Asnanic ya samu babbar nasara lokacin da kamfanin AMINU SAIRA MOVIES s**a fito da manya fina-finai irinsu “DAWO-DAWO" da “JAMILA DA JAMILU" inda wakar sa ta shirin dawo-dawo ta zama waka wanda akafin jinta a tarihin fina-finan hausa a wancan lokaci.
✍️ Nazifi Asnanic ya zama lamba daya CIKIN mawakan hausa da wakokin fina-finai irinsu “GADU da HASKE " da “SAI WATA RANA " da “RAI DA BURI" da “DAN SARKI" da “ LADIDIN BABA" da sauransu.
✍️ Ba'a iya wakokin film ya tsayaba,NAZIFI ASNANIC yana yin wakokin masu zaman kansu.misali wakarsa mai taken “AMINA" da “DARE DA YAWA" da “TUSHEN LABARINA" wadannan wakoki har yanzu jama'a Basu daina sauraron su ba.
✍️ A fagen wakoki siyasa ba'a barshi ba baya ba, Nazifi Asnanic shine mawakin kannywood na farko wanda yayi wakar siyasa da ba'a tava yin mai tashe irin taba A tarihin wakokin siyasa na zamani. WANNAN waka itace “DAWO-DAWO" wanda ta taka muhimmiyar rawa a samun nasara Rabi,u musa kwankwaso a zave 2011
✍️ To a ranar 26/5/2019 ne dai.Nazifi Asnanic ya samun shiga cikin jerin muhimman mutane na Duniya wadanda tarihinsu yake kunshe a kafar “WIKIPEDIA"
congratulation Nazifi Asnanic.
✍️ writing by umar bala jega
umar bala rini jega
doctor love
P.R.O NAZIFI ASNANIC FANS 👈🏿