28/01/2026
WANNAN LABARIN YA GIRGIZA NI MATUQA
Wani Bawan ALLAH Da Yake Kan Gargarar MUTUWA, Sai Dangi S**a Kewaye Shi Suna
Ta Kuka.
Sai Ya Ce:"Ku Tashe Ni Zaune"
Sai S**a Zaunar Da Shi Sai Ya Fuskance Su
Ya Dubi Mahaifinsa Ya Ce:"Baba! Me Yasa
Kake Kukan Rabuwa Da Ni???"
Ya Ce:"Ina Jimamin Rashinka Da Yadda Zanyi
Da Kewarka Bayan Ka Rasu!"
Sai Ya Juya Ga Mahaifiyarsa Ya Ce:"Umma!
Me Yasa K**e Kukan Rasa Ni???"
Ta Ce:"Saboda Zan Shiga Quncin Rayuwar
Rasaka!"
Sai Ya Juya Ga Matarsa Kefa Me Yasa Ki
Kuka???
Sai Ta Ce:"Zan Rasa Dadin Zaman Da Muka Yi
Gashi Kuma Ban San Hannun Wanda Zan
Fada Ba".
Sai Ya Juya Ga 'Yayansa Kufa Me Yasa Ku
Kuka???
S**a Ce:"Saboda Zamu Zama Marayu Bamu
San Irin Wahalar Da Zamu Shigaba Bayan
Baka Nan"
Daga Nan Sai Ya Dube Su Ya Fashe Da
Matsanancin Kuka Gaba Daya S**a Dube Shi
Kai Kuma Me Yasa Ka Kuka???
Ya Ce:"Naga Kowa Yana Kukan Rasa Ni Ne
Saboda Bukatar Qashin Kansa.
Shin a Cikinku Akwai Wanda Yake Kuka
Saboda Doguwar Tafiyar Dake Gabana???
Koko Akwai Wanda Yake Kuka Saboda
Rashin
Isashshen Guzuri Na???
Ko Akwai Wanda Yayi Kuka Don Za'a
Turbudani a Turbaya???
Ko Abin Da Zan Tarar Na Mummunan
Hisabi???
Ko Ko Akwai Wanda Yake Kuka Saboda
Tsayuwata a Gaban Rabbil Izzati Bansan Me
Zan Tarar Ba???
Daga Nan Sai Ya Yanke Jiki Ya Fadi, Sai
S**ai Kansa S**a Juya Shi Sai S**aga Ashe
Har Rai Yayi Halinsa Ya Rasu!.
HAQIQA DUNIYA BATA DA TABBAS!
YA ALLAH! KASA MUYI KYAKYKYAWAN
QARSHE, YA ALLAH KAYI MANA KARIYA DA
RADADIN FITAR RAI, YA ALLAH KAYI MANA
GAMDA-KATAR A LOKACIN KARBAN
RAYUKANMU
ALLAH YASA MUGAMA DA DUNIYA LAFIYA AMEEN