05/01/2022
Sakarwa Sisters Ɗawauniyar Ƴaƴa da Brothers Su ke, Shi ne Jigon Samuwar Matsalar.
Ku Karanta Ku ji.
Idan mu ka yi duba da matsalolin da su ke yawan faruwa na Mutuwar aure ko kuma auren ya samu matsala tun kafin ayi a tsakanin brothers da sisters, tabbas zamu iya cewa iyaye maza suna da laifi domin suna bada gudummawa wajen afkuwar hakan, sakamakon sakacin da su ka yi da ƴaƴansu wajen basu kulawa a matsayinsu na Iyayensu.
Brother ne ya na da mata har da Ƴaƴa a tsakaninsu amma ba ruwanshi da batun kulawarsu safgar rayuwarshi kawai ya ke, ya ɗauka cewa haƙƙin ƴaƴan kawai agareshi shi ne ya ciyar dasu da tufatarwa. Yes za ka sha mamaki kaga brother ba ruwanshi da kuɗin makarantar ƴaƴanshi Uwa keye fafutukar hakan, batun Kayan Sawa na gida dana fita (Hijab) Uwa ke fafutukar yi, ko yarinya idan saurayi ya bata wasu kuɗin ko kuma wani ɗan uwa nata ya ba ta. Wallahi da yawan Ƴan matan sister da haka su ke haɗuwa suda iyayensu mata su ke yiwa kansu hidimar rayuwa.
Batun zuwa program ba ruwanka da kuɗin motar zuwansu bare na dawowarsu, to taya kake tunanin uwa ba za tayi ikon da Ɗiyarta ba, a loƙacin da ta ke da ikon yin hakan. Idan sister da brother suna soyayya Sai wani mai Hannu da Shuni ya zo, iya daɗewar da kukai za a kawar dakai gefe ne domin tana tunanin cewa itama ƴarta zata faɗa halin ɗawainiya da ƴaƴanta ne idan ta haihu.
wannan dalilin kesa maganar auren Brothers ke yawon domin koda an samu Uban yarinya akan lamarin za kaga baida power domin bai ɗauki ɗawainiyar yar ba, da kunya yace zai nuna iko da ita, domin ita kanta yarinya za tafi jin maganar Mamarta ne. Kada a cemin talauci ke kawo hakan wallahi idan da talauci ma akwai hali to.
-ak
-5-Jan-2022