05/01/2026
A wannan rana, ina taya Gwamnan Jihar Kano mai girma Alhaji Abba Kabir Yusuf murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
Ina tunawa da shekaru da dama na tafiyar siyasar mu tare, inda ya rike mukamai da dama masu muhimmanci — tun daga zama Mataimaki na na Musamman a wa'adina na farko da lokacin da nake Minista, sannan ya zama Babban Mataimaki na na Musamman, daga baya ya rike mukamin Kwamishina a wa'adina na biyu, kuma yanzu yana matsayin Gwamna — duk wadannan matsayi ya taka rawar gani wajen aiwatar da hangen nesanmu da shirye-shiryen ci gaban Jihar Kano.
Ina addu'ar Allah ya ba shi hikima, lafiya, da fahimtar tafiya bisa gaskiya a wannan sabon shekara." — RMK
Rabiu Musa Kwankwaso
Abba Kabir Yusuf
On this day, I appreciate the birthday of the Executive Governor of Kano state, Alhaji Abba Kabir Yusuf.
I reflect on the many years of our shared political journey, during which he served in various important capacities— first as my Personal Assistant in my first term and as Minister, and then as Principal Private Assistant, and later as Commissioner during my second tenure, and now as Governor— through which he contributed to the vision and programmes we pursued for the development of Kano State.
I pray that this new year grants him wisdom, good health, and clarity of purpose. - RMK