P D P ko APC

P D P ko APC lokaci bakone kar idanu yatufe muna tare

04/04/2022

Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun, Ciki Da Gaskiya, Wuka Ba Ta Iya Huda Shi.

04/04/2022

A CIKIN WATAN AFRILU NA SHEKARAR 1983 AN TAFKA TAKAITACCEN YAKI TSAKANIN KASAR NIGERIA 🇳🇬 DA KASAR CHAD 🇹🇩

Rikici Yayi Sanadiyar Rasa Rayukan Mutane Kusan 100.

Yaki Ne Wanda Ba A San Labarlin Shi Sosai Ba.Wanda Aka Yi Shi Akan Ikon Mallakar Wasu Tsibirai A Tafkin Chadi. Yakin Ya Fara Ne A Lokacin Da Wata Runduna Karkashin Jagorancin Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Kasar Chadi' Idriss Déby Ta Mamaye, Wasu Sassan Jihar Borno Ta Najeriya, A Lokacin Mulkin Hissène Habré Na Kasar Chad 🇹🇩 Wanda Yazo Dai-Dai Da Zamanin, Mulkin Farar Hula Na' Marigayi Alhaji Shehu Aliyu Shagari.

Yakin Ya Faru Ne A Lokacin Yakin Tsakanin Kasar Chad Da Libya. Kuma Jim Kadan Kasar Chadi Ta Fuskanci Yakin Basasa, In Da Sojojin Kiyaye Zaman Lafiya Na Najeriya S**a Tsinci Kansu Cikin Fada. Wani Abin da Ya Kara Dagula Dangantakar Chadi Da Najeriya Shi Ne Rikicin Yankuna A Kusa Da Tafkin Chadi , Wanda Ya Dade Yana Haifar Da Rikici.

A Ranar 18 Ga Afrilu, 1983, Sojojin Chadi S**a Mamaye, Tsibirai 19 Na Najeriya A Yankin Tafkin Chadi. Bada Wani Bata Lokaci Ba Jiragen Yakin Najeriya Kirar Mig 21 S**a Soma Luguden Wuta Akan Sojojin Kasar Chadi.

A Gefe Guda Muhammadu Buhari. Shugaban Kasar Nijeriya Na Yanzu. Yana Babban Jami'in Kwamandan ( GOC ) Na Runduna Ta Uku Ta Jos. Ba Tare Da Ya Jira Umarni Daga Gwamnatin Tarayya Ba. Ya Debi Sojoji S**a Rararaka Sojojin Chadi Har Cikin Kasar Su. Saida Sojoji Najeriya S**a Shiga Kilomita 50 A Cikin Kasar Chadi. Har Saida Kasar Chadi Ta Kai Karar Najeriya Majalisar Dinkin Duniya. A Kan Abinda Sojojin Najeriya A Karkashin Muhammad Buhari Su Kayi Mata.

Bada Wani Bata Lokaci Ba Shugaban Kasar Najeriya Shehu Shagari Ya Baiwa Buhari Umarni Ya Fita Daga Cikin Yankin Kasar Chad, Aikin Da Dama Ba'a Sashiba Amma Buhari Yaki Bin Umarni.

A Lokacin Majalisar Dattijan Najeriya Ta Kafa Kwamitin Binkice A Karkashin Sanata Sabo Aliyu Bakin Zuwo, A Kan Lamarin. Inda Majalisa Ta Kirawo Muhammadu Buhari Domin Jin Ba'asi. Muhammadu Buhari Ya Baiyana A Gaban Majalisar, Dauke Da Hular Soja A Kansa, Nan Da Nan Sanata Sabo Bakin Zuwo,Ya Harare Shi Tare Da Daka Masa Tsawa" Yace Kai Mara Kunya Cire Hular Nan, Nan A Gaban Manyan Najeriya Kake Ba Barikin Soja Ba.

Wannan Yana Daya Daga Cikin Rashin Jituwar Data Faru Tsakanin Sojojin Najeriya Da Gwamnatin Farar Hula A Zamanin Har Ya Kai Da Sojoji S**a Kifar Da Gwamnatin Farar Hula A Ranar 31 Ga Watan Disamba 1983.

~ B Salia Sicey

02/04/2022

Interest

01/04/2022

ORUBEBE DAY.....

A rana irin ta yau 31 March 2015 shekaru bakwai da s**a wuce Peter Godsday Orubebe ya dakatar ds bayyana sakamakon zaben shugaban kasa, inda ya zargi Attarihu Jega da aikata kura kurai har ma da kabilanci....

A wancan lokacin miliyoyin mutane sun shiga dsmuwa mai karfi sakamakon dakatar da kidaya da orubebe yayi, domin dai an hango nasara kusa ga Muhammadu Buhari amma Orubebe yana neman haifar da damuwa, a dai wancan lokacin tabbas da ace Orubebe ya samu damar hana cigaba da kirga kuri'a a lokacin, hakan na iya kaiwa ga mummanan yaki...

Kusan dukkan yan Arewa gani muke idan Buhari ya zama shugaban Nigeria shi kenan matsaloli da wahalolin dake addabarmu sunzo karshe, sai gashi maimakon a samu sauki sai ma lamarin ya kazance sosai....

We will Not take it, Jega you have been compromised, we are no longer confident in you...

DAGA Rabi'u Biyora

Address

Bakin/kasuwa
Itass
001

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when P D P ko APC posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to P D P ko APC:

Share